2

125 24 0
                                    

AISHA

Walidation S Mapi

2

~Duba kwanon naman Aisha tayi taga saura tsoka biyu ce kanana ta saura dago ido tayi ta fara warowa tana kallonsu daddaya a wajen.

Anti Amarya ce ta dago kai cikin sauri tace "Aisha yi sauri mana ya kika wani tsaya kina kallonmu"

Cikin sanyin jiki tace "ya kare"

Anti Amarya ce ta dubeta dakyau tare da fahimtar me ta Aikata sai wayance saboda kada kowa ya gane tace "kash ai kamar nasan naman nan bazai isa ba tunda aka kawo shi,kinga kwashe na yaran nan ki kawo min da wuri"

Baffa Auwalu ne yace "kinga kyale shi kawai mu manyan zamu hakura yaran suci in yaso gobe sai a yanka babban daba a daina yanka kanana"

Ajiyar zuciya Anti Amarya tayi kana tace to ba matsala taci gaba da serving nasu ba nama.

Inna ce ta mika wuya kan sauran da suka samu namar kafin tace "haba mesuna duba yadda kika zugawa Gadanga wannan nama haka nawa zai baki in kukayi gefe kenan? kodai shine gogan nawa?" da Aisha tayi maganar.

Aisha ce ta sauke kai tana kallon kafarta amma batayi murmushi ba gudun kada Inna ta gane don Inna ta gane.

Iyayensu maza ne suka fara murmushin dattako saboda inda hali Inna ta saba jonawa mutum Abinda bai so.

Kadan ya rage momyn Haidar taja tsaki saboda yadda ta tsani Aishar bata sonta ko kadan.

Khadijah,Amina da Fatima ne suka wurgawa Aisha harara saboda dukanninsu masoyan Haidar ne,kuma gashi an fara maganar hada shi da me hannu daya gashi Inna batason bacin ran Aishan saboda me sunanta ce indai tace tanason abu dole a mallaka mata shi.

Maleeka kuwa kallonsu tayi gaba daya tare da fahimtar me ke faruwa cikin family din nasu kada kai tayi tare da cigaba da cin Abincinta.

Inna ce ta miko hannu ta dauki tsokar kaza gaban Haidar ta make tayi shirt,duk kunya ta ishe shi saboda ya rasa ta cewa,maman Haidar kuwa sai bin ya'mmatan take da harara saboda ta gane nufinsu a kan danta.

Sun gama cin Abinci lafiya kowa ya watse yayi nashi part din inda Baffa Aminu mijin Anti Amarya yace mata ta ara mishi lokaci zai dawo bada jimawa.

Daga mishi kai tayi Alamar ba matsala kamin ta ja hannun Aisha sukayi part nata tare.

Suna shiga ta zauna bakin gado ta zaunar da Aisha tace "Zauna nan yar' kaniya kefa wawuya ce Aisha baki iya fighting a kan Abinda kike so ba yanzu don Allah kiga Shirmen da kika tafka ai lokacin da Inna tace kodai shine murmushi zakiyi saboda a gane me kike ciki,ki duba kiga yadda ya'mmatan nan kowacce ke kallonki kinsan fa zasu iya yimiki zarra a wajen Haidar wallahi ki kiyaye".

Daga kai tayi cikin nutsuwa da kulawa tace "Anti Amarya yaya zanyi ne to?"

"Yawwa Abinda nake so da ke shine idan kika kuma samun wannan damar kada ki bari ta subuce miki,in Inna ta Kuma yimiki wannan tambayar murmushi zakiyi ki nuna kina son Haidar din in yaso ayi ta ta kare"

Daga kai tayi Alamar fahimta kafin tace "insha Allah Anti Amarya zanyi hakan yanzu dai bari naje naga yaya Aliyun".

"Ke Aisha zubarda Ajin yayi yawa ya kamata ki kama kanki ba lokaci daya ne so yake shiga ba a hankali yake yiwa zuciya dirar mikiya,ba dazu kinje ba ne?"

"Har sau biyu ma" inji Aishar.

"Yawwa to kibari sai gobe kije kinji kanwata?"

Gyada kai tayi tare da godewa Anti Amarya saboda wannan k'auna da take nuna mata saboda bayan Inna da ummanta da iyayensu maza babu me k'aunarta bayan Anti Amarya.

Sallama sukayi ta bar dakin ta nufi part nasu tana shiga ta tarar da ummanta tayi bacci saboda dama ta saba da fitan Aishar zuwa dakin Anti Amarya,itama samun waje tayi ta kwanta saboda sam batason fitinar su Khadeeja ga shegen wayar dare kuma suna yawan habaice-habaice da ita hakan yasa ta daina kwana a dakin nasu ba tare da sanin iyayensu maza ba.

*********
Washe gari da safe bayan sun gama karin kumallo kowa ya mike yabar wajen inda Aisha ta lura da Haidar yaki tafiya yasa ta fake da kwashe kwanuka karasawa wajen nashi tayi ta tsuguna ta gaishe shi.

Amsawa yayi a dakile kafin yace "lafiya kuwa kika kasa mikewa me ke tafe dake?"

"Yaya Aliyu dama kawai gaishe ka nake son yi bakomai ba"

Har a zuciyarshi yana jin dadin yadda Aisha ke kiran sunanshi da kuma tarbiyyarta ba kamar sauran ya'mmatan gidan ba duk iyayensu mata sun sangarta su ga fitsara sai a wajen iyayensu maza ne suke nuna sunada hankali.

"Okay nagode" shine Abinda ya fada a takaice.

Jin dadin godiyar tayi kafin ta mike taci gaba da kwashe kwanon kada Anti Amarya tace ta barta ita kadai.

Mikewa yayi yabar dinning yana murmushin da bai san dalili ba.

Anti Amarya ce ta karaso inda Aishar take ta rike hannunta guda daya tace "Aisha kenan masoyiyar Haidar"

Murmushi Aisha tayi ta sauke kanta k'asa tace "Kai Anti bakida dama wallahi"

"Karya nayi ne?" Inji Anti Amarya bata jira Amsar Aishar ba tayi gaba.

Murmushi Aisha tayi ta wuce part Baffa Musa wajen su Maleeka kenan can kadai take iya zuwa saboda itama Maleekar batada matsala.

Tana shiga ta tarar da Maleeka na waya,da Alama dai da Nasir take wayar saboda kullum suna like a fili in kuwa basa tare to suna waya,tunani ta fada inama ace itace da Yaya Haidar nata sai kuma ta karasa wajen Maleekar.

Warce wayar tayi tare da cewa "to tattabara iyayen soyayya,ba'a ma san na murda handle ba ko?"

Daga wayar taji ana magana karawa tayi a kunne tace "Dalla Nasuru kabar yarinyar mutane tayi Aiki kullum waya ai sai ku gaji da juna"

"Bata wayarta dalla kema kije kiji da masoyinki ai ni tunda wuri na gane kuna soyayya da Hamma wuro kawai mazgewa kukeyi" ya fada tare da make dariyar shi.

Saura kadan Aisha ta fashe da kuka saboda ita in Akwai wanda ta tsana sama da Hamma wuro bata sani ba.

Hakuri ya bata a kyar ya shawo kanta dama inda sabo sun saba 'yar haka da Nasir.

"Wallahi kada ka sake min haka Nasir,banaso"

"Kin gyara sunan Ai dan kaniyarki"

Dariya ta saki saboda tasan ba'a yiwa Nasir ya kyale komai kayi mishi sai ya rama.

"Bazan sake ba kaji na wajena"

"Kima sake wallahi sai naje wajen Inna ince kefa kince Hamma wuro kike so a Aura mishi ke kawai"

"A'a yaya Nasir kada kamin haka,in kamin haka wallahi bazan taba yafewa ba"

"To nima kada ki sake cemin Nasuru"

Amsawa tayi da insha Allah ta datse wayar saboda tasan in dai Nasir ne bazai taba kashewa sai in su suka kashe.

Fuskantar Maleeka Aisha tayi tace "Maleeka akwai wata magana da nake so muyi,so nake ki bani kyakkyawar shawara"

Kafin ta kara wata magana ta fara kakkarwa idonta ya kafe sama ta kuma fada a kan gadon.

Ihu Maleeka ta saki hakan ya Ankarar da Gwaggo Rabi,umman Maleeka kenan yasa ta shigo dakin da gudu ta rike Aishar saboda sun saba da wannan cutar irin ta Aisha.

AISHAWhere stories live. Discover now