AISHA
Walidation S Mapi
5
________Aisha na dakin Inna tana cikin tsofin tana zaune labarin daurin Auren na isota ta some a dakin.Tsofin ne sukayi kanta da gudu suna ihu da kururuwa irin wanda tsoffi suka saba,kowa sai rike Aisha yake da gudu Inna tayi part na umman Aishar ta amso maganinta suka shaka mata a hanci.
Bata farfado ba amma ta yi bacci.
Haidar ne ya faki idon mutane yayi kuka yadda yake so,Nasir kuwa idon shi ne yayi rau-rau amma baiyi kukar ba saboda ya daure yayi tawassali,Faruq kuwa sai washe hakora yake yana gaisawa da mutane haka Salihu ma Hamma wuro kuwa tunda aka daura Auren ya bar wajen shi da daddynshi.
Can wajen la'asar Aisha ta farfado a hannun inna, ido ta fara kyallawa ko me take nema itama bata sani ba.
Tsofin ne suka fara godiya ga Allah sauran tsofin kuwa saurin mikewa sukayi zasu tafi wai kada yarinya ta mutu a hannunsu.
Anti Amarya yau ana buduri tayi wanka na gani a fada don itace Antin gida,Aisha ta nema ta rasa cikin gidan yasa ta nufi part na Inna don tasan indai ka rasa Aisha cikin gida to bata wuce part na Inna.
Yanayin da ta tsinci Aishar ne ya tsinka mata rai saboda batayi zaton cutar zai tashi yau ba,karasawa wajenta tayi ta zauna bakin gadon ta rike hannunta daya tace "Aisha yau kuma?"
"Anti Amarya ba laifi na bane raina ne ya tsinke wallahi"
Tsofin ne suka saka dariya sukace "laaa dama tsinkewar rai ce?ai kiyi ki gaji yarinya kowa yayi wannan zamanin" suka fice a dakin suna dariya.
"Anti Amarya yau Ina cikin damuwa na rasa yadda zanyi da rayuwata an Aura min wanda bana muradi bana k'auna ya zanyi"
"Hakuri" shine Abinda Anti Amarya ta fada a takaice.
"Anti Amarya na kasa hakurin wallahi,tun dazu nake ta kuka a dakin nan Allah ma ya taimaka tsofi ne basa gane kuka na"
"Yanzu dai yi hakuri ki tashi kije kiyi wanka tunda duk sauran 'yan uwanki sunyi"
Bata iya musu ba yasa ta mike tabi Anti part nata.
Suna shiga Anti Amarya ta daga waya tace "kin karaso kuwa Rufee?"
"Ehh kawata na karaso Amma wallahi bazan iya shiga ni kadai ba mutane sunyi yawa ga kuma Akwatunan sunyi yawa"
"Okay ki jirani yanzu zan zo in shiga da ke"
Datse wayar Anti Amarya tayi tare da kallon Aishar tace "zauna nan 'yata kanwata yanzu zan dawo kinji"
Gyada kai Aisha tayi ta kwanta kan gadon Anti Amarya.
Shigowa dakin Anti Amarya sukayi suka samu Aisha kwance yadda ta barta.
"Aisha na mike kinji" Anti Amarya ta fada tare da daga Aishar da hannu daya.
Rufee ce tace "Ayya Aishar mu ba lafiya ne"
Anti Amarya ce tace "ehh wallahi Rufee Aisharmu me hankali ce ta sadaukar da hannunta ga wani"
"Ayya" Rufee ta fada tare da cewa "sai mu fara da wuri ko naga hudu ta kusa"
"Ehh hakane ayi sauri nizan fita yanzu zan dawo please Rufee ki hadarmin kanwar tawa wallahi inaso tayi kyau tafi kowa"
"Insha Allah kada ki samu damuwa kawata Aisha zatayi kyau har tafi sauran 'yan uwan nata"
Aisha ido take warowa tana kallonsu kamar karamar yarinya tana kuma mamakin yadda Anti Amarya take k'aunarta kamar ita ta haife ta sai kuma ta bude bakin hankali tace "Anti Amarya kece kika dauko min me kwalliya da kudinki?"
KAMU SEDANG MEMBACA
AISHA
Fiksi Sejarahlabarine a kan wata yarinya mara hannu daya wacce take kaunar dan uwanta Amma shi baya sonta ko kadan.