21

98 16 1
                                    

AISHA

Walidation S Mapi

21

~Ya shiga mota yaja yabar Aisha a wajen ko numfashi batayi, yana shiga gidan ya rufe ya shiga ciki ya rufe dakin Aishar ya  kwanta abinshi.

Can wajen sha biyu da rabi na dare ta mike dalilin ta mike dalilin ruwanda akeyi me karfi yanayin yadda iska take kadawa da karfi ne yasa ruwan yake yi da zafi kamar ana zaneta da bulala,gashi bazata iya daga akwatinta ba balle ta matsar dashi gefe gashi ruwan sai karuwa yakeyi, kwanciya tayi ta takure ta wani tattare jikinta kamar wacce take daki duk sanyi yabi ya isheta, sai a lokacin ta lura da babu gashi kaya a jikinta daga ita sai towel dake daure a kirjinta,saurin mikewa tayi don ta canza kayan sai ganin kudi tayi da paper a sama saurin dauka tayi donta karanta Abinda ke kan paper Amma babu wani haske isasshe,walkiya ce kawai take dan haska ta,karasawa wajen akwatin tayi ta tsuguna a kai ta dauki kaya da sauri don kada na cikin akwatin su jike,sanya kayan tayi a cikin ruwan ta ajiye towel din a gefe ta kwanta a kan akwatin saboda sam batada kuzari a jikinta, kukan ma ta kasa yi don bakinciki ne a tattare da zuciyarta, can taji sawun tafiyar mutum hakan ne ya bata damar mikewa don neman taimako saboda ba'a karamin tsorace take ba kawai ba yadda ta iya ne,a hankali taji me tafiyar ya karaso kusa da ita zai bi wata hanya yaje gida.

"Dan uwa ko ya'r uwa don Allah ku taimake no,wallahi banida kowa a garin nan kuma banida wajen zuwa,kaddarace ta kawo ni nan,don Allah ka taimake ni" ta karasa maganar da lamairin namiji don ta fahimci namiji ne shi.

Kokarin guduwa yayi saboda baison daukar jigillar da yafi karfinshi sai kuma ya tuna da cewa idan yabar wannan baiwar Allah a nan wani abu ya sameta tabbas shima yanada alhaki tunda gashi yanada damar taimaka mata Amma yaki,komawa yayi a hankali ya dubi inda take "mutum ko aljan?" ya tambaya a tsorace.

"Wallahi mutum ce ni,don Allah ka taimaka min wallahi ina cikin matsananciyar rayuwa".

"To ta ya zan tabbatar da hakan?kimin sauri fa kinga ruwa na jikani,kuma lemata ballewa take kokarin you" har yanzu a tsorace mutumin yake.

"Haska kafafuwata ka gani wallahi ni mutum ce".

Kamar tasa me yake kokarin yi kuwa,hakan ne yasa ya zaro wayarshi daga aljihu ya kunna toci ya haska kafarta yaga normal ne sai dai tayi yellow dayawa, "zaki iya zuwa muje Amma ke zaki kasance a gaba don bazan iya barinki a bayana ba".

"To shikenan nagode,amma inada kaya kuma ni nakasasshiya ce banida hannu daya.

Firgita yayi a tsorace yace "me? bakida hannu? Baiwar Allah ki taimaka kada ki cutar dani wallahi bamuda komai a gidanmu,Abinci ma dakyar muke na sawa a bakin salati,duk kudinda nake nemowa wallahi a karkashin makarantar kanwata nake gamawa,bazan iya samun kudin magani ba inkin cutar dani".

Tun Aisha na kuka harta fara murmushi don ba karamin dariya ya sata ba,yadda yake kora bayani kamar an tambaye shi.

"Wallahi ni da kake gani mutum ce me zuciya daya,sam banida niyar cutar kowa a rayuwa balle ma wanda zai taimaka min don Allah ka taimaka ka dauka min sanyi nake ji gashi jikina na rawar dari".

Da sauri ya karasa wajen ya suri  akwatin ya daura a kai ya mika Mata lemar yace ta rike tana binshi dashi a baya.

Wajen wani gida suka nufa me dauke da dakuna biyu,dakin na kasa Amma anyi musu filasta,gidan an zagaye shi da kara da zana gidan dai ba wani kyan gani a talakawan ma sune lambar karshe,suna shiga cikin gidan ta sake sandarewa don ba karamin mamaki ta shiga ba,nan ta shiga tambayar kanta shin mutane ne suke rayuwa a wannan gidan?meyasa a koda yaushe masu kudi suke killace kansu a gida suna hutawa inda wasunsu suke fita kasashen waje suna sharholiyarsu,bayan ga talakawa birjik a gari,mabukata masu neman rufin asirin kansu,tana cikin wannan tunanin taji an katseta da fadin "sannu da zuwa ya'r uwa" ta kusa tayi dariya jin wata mummunar Hausa da yarinyar tayi,makewa tayi tareda fadin "yawwa" wata tsohuwa ce ta fito daga dayan dakin dauke da lema a hannunta ta karasa wajensu tayiwa Aisha sannu da zuwa suka dan kimtsa ciki suka ce ta shigo,ai kuwa da sauri tayi ciki don ji take kamar anyi mata bishara da gidan Aljanna,a bakin kofar ta tsaya ta cire kayanta tasa aka ciro mata wasu ta sanya saboda duhu nee dakin hasken kadan ne yasa ta samu damar canza kayan.

AISHAWhere stories live. Discover now