9

70 19 0
                                    

AISHA

Labari/rubutawa:
Waleedatu S Mapi

9

~Abdul na gama fadar ya fice ya tafi.

Yana fita Hamma ya shiga dakin Aisha yayi mata dukan tsiya ya kuma kwace sauran Abincin ya tafi.

Kuka tayi me isanta ta mike ta fita cikin gida ta nemi buta tayi Alwala tayi salla ta kwanta bacci.

Can cikin dare sanyi ya isheta ta mike ta kuma neman wani hijabinta ta lullubu dashi ta kwanta.

Washegari da safe ta tashi ta nemi hanyar kicin tayi girki ta aje mishi nashi a dining table ta wuce daki da nata ta cinye.

Yana fita ya lura da flask nashi a dinning kuma yasan a kicin suke,karasawa yayi ya bude saida ya lumshe idanu saboda kamshin da ya ratsa shi tun a gida yasan Aisha kaf cikin kannensu babu wanda ya kaita iya girki,sake bude dayan flask din yayi yaga wani jajjage murmushi yayi yace "Allah ya bani ya'r Aiki a banza da wofi tunda ta dauki kanta jaka zan siyo kayan Abincin in aje in yaso tayi ta dafamin" yana gama surutun ya samu waje ya zauna ya ci Abinci mai isar sa ya fice office dama daddyn shi ya nema mishi Aikin a nan katsina ko sallama bai yiwa Aisha ba balle ta samu fuskar gaida shi.

Tana jin karan mota ta fito ta kwashi sauran Abincin ta kai kicin ta kuma zauna a falo ta kunna tv tafara kallo,tun tana kallon har ya koma tunani sam ta rasa meyake mata dadi ga kewar umma da Anti Amarya da take barinma Inna da ke matukar kaunar ta batasan lokacinda hawaye ya fara sirnana daga idanunta ba gashi ba waya a hannunta Hamma ya kwace,a wannan tunani da hawaye bacci ya kwashe ta.

Can wajen sha daya taji kamar an bude gate da sauri ta fito taga ko waye,motar Hamma ta gani yayi fakin a fakin sifes (parking space) ranta ne yayi saurin tsinkewa saboda tunawa da tayi batayi Abincin Rana ba gashi yazo karba,sai kuma ta tsaya taki shiga ciki.

Yana fitowa daga motar ya bude boot ya fara fitar da kayan Abinci yana Ajewa a kasa.

Idanu ta kura mishi kana tace "Ayya bawan Allah Ashe yana tausayi na" sai kuma ta shige ciki ta kwanta a dakinta.

Yana gama shigowa da kayan ya shige dakinta yaga ta kwanta Alamar tana bacci,dundu ya sauke mata a bayanta ji kake duum, kana yace "lalle Aisha wato har kin samu fagen bacci da rana ko?to wallahi ki tashi kafin naci ubanki".

"Haba yaya Hamma me zanyi idan na tashi?".

"Me? ubanki zakiyi,nace ubanki zakiyi kinji banza kawai ki tashi kan naci uwarki" Yana fadan haka yana kokarin zaro belt.

Da sauri Aisha ta mike ta rakube a gefe cikin tsoro.

Hamma ne ya bude baki yace "wato har kutare sun samu fagen da zasu rika mayarwa da masu hannu maganganun da suka ga dama ko? to Aisha ina gargadinki da cewa idan baki daina maida min magana ba wallahi sai na cire miki hannu dayan nan naga yadda zakiyi da rayuwarki".

Cikin bacin rai Aisha tace "saika cire Ai tunda tsohon shi....."

Kamin ta karasa Hamma ya rungume ta ya fara romancing dinta kamin ta mike har yaci karfinta,sai da ya gama mata iya muguntar da yaga dama kafin ya mike ya barta a dakin,kuka me tsuma rai Aisha ta shiga yi saboda tasan ba'a fagen soyayya yayi mata ba dan kawai ya sata bakinciki ne,can ta itama gyara kwanciyarta tayi bacci tana kuka.

Yana fita ya shige mota ya fice ya bar gidan farinciki ne ya cika zuciyarshi saboda ko ba komai ya kunsa mata bakinciki a zuciyarta.

Bayan Azahar ta tashi tayi wanka ta shiga kicin ta dafa macaroni taci ta zauna ta bude tv ta fara kallon Bollywood wani film akeyi chak'de'india dadi film din yake yi mata yadda ya'mmatan suke wasan kwallon kafa,kullum idan ta zauna babu Abinda yake sa ta mamaki kamar ace tana mace Amma da burin wasar kwallon kafa gashi hannu daya ne da ita babu damar tayi wasar,tana cikin farinciki tana kallon taga an hasko wata daga nesa a cikin wasan,hannu daya ne da yarinyar itama black Indian ce saboda batada wani kyau,ganin yadda yarinyar take wasa da kwallo ne ya kara burge Aisha sai wani tsalle take tana ihu Ashe itama zata iya wasa koda batada hannu.

Tana cikin kallon ne taga ana using remote ta samanta,saurin dago kai tayi don ganin wanene,Hamma ne taga ya canza channel daga Bollywood zuwa Sunnah tv yace "Ashe kutare ma sun waye harda kallon Indian".

Bata ko kalle shi ba ta mike tayi dakinta tasa sakata ta kwanta.

Batayi ko minti daya ba ta ji yana ta kwankwasa kofa, da farko tayi niyyar bazata bude ba sai kuma ta daure ta mike ta bude gudun fitina hankade ta yayi ta fada kasa yace "ina Abinci na?tambayarki nake don uwarki ina Abinci na?"

Ido Aisha ta zuba mishi tana kallonshi.

"Au bazaki bani Amsa ba kenan? so kike na mai-maita Abinda nayi miki dazu?".

Da sauri Aisha ta dago kai tace "sorry please ban samu nayi ba ai lokacin yin Abincin dare baiyi ba in banyi karya ba karfe hudu ne fa".

"Haba miskiniya ta yanzu ko ke ma ace miki karfe hudu zaki yadda?to maza ki tashi ki girkamin Abinci nan minti goma na baki ki dafamin shinkafa da wake".

"Haba yaya minti goma ai ko waken bazata dafa ba balle shinkafa minti talatin ma bazata karbe ni ba".

"Kinaji na bazan rage lokaci ba cikin minti goma nake so ki dafamin ko kuma in rabaki da hannu daya da ya sauran kinji na fada miki".

Sauke kai tayi ta mike ta nufi kicin ta barshi a dakin nata,tana fita shima ya fita ya zauna a falo ya maida channel din zuwa mbc Bollywood yaci gaba da kallon film din.

Da sauri take hada-hadan yin girkin saboda so take taga ta gama da wuri komai da wuri take yinshi Agogo ta duba taga saura mata minti biyu ranta ne ya tsinke saboda tasan yau Hamma zai kashe ta Idan bata gama girkin ba,cikin minti goma ta gama dafa Abincin ta kai mishi.

Ga mamakinshi ya karba a zuciyarshi kuma yana Raya cewa wannan Abincin danye ne saboda babu yadda za'ayi mutum ya dafa shinkafa cikin minti goma balle ma da wake.

Bude plate din yayi cikin Azama,me zai gani indomie ne akan plate din taji mai da yaji gashi idon indomin yalo ne,sai kuma kwai da aka dafa dashi a hade tabbas indomin ya shiga ranshi sosai Amma ai ba wannan yace ta dafa ba "lalle yau Aisha zaki Raina kanki" shine Abinda Hamma ya fada a fili.

Da sauri ta dago kanta ta fara bashi hakuri.

Ayi min uzuri inason masu min sako da kuma masu kirana harma da masu min d.m ta whatsApp Ina matukar kaunarku my Wattpad peoples.

AISHAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant