AISHA
Walidation S Mapi
10
~Da sauri ta dago kanta ta fara bashi hakuri,ko ta kanta bai bi ba ya wanke ta mari ya kama hannunta me ciwo yafara bugawa da dayan hannunshi,ihu ta fara tana bashi hakuri Amma ina yaki ji saima kara abin yake babu tausayawa.
Koda taga bazai daina ba saita zube kasa ta yanke numfashinta na sakanni kamar ta suma, sai a sannan ya kyale ta yashige dakinsa, da gudu Aisha ta mike ta shiga dakinta tana haki sanya sakata tayi da wuri don kada ya shigo duba hannun tayi taga yana jini sosai ihu ta saka tayi wajen Akwatinta Allah yayi ma ta dauki wata karamar hankacif da Anti Amarya ta bata tun tana sakandari,dukda tana son hankin haka ta dauka tasa a hannunta da yake jinin.
Koda ya shige ciki yayi wanka ya kwanta kan gado ya dauko wayarshi ya fara chat da ya'mmatan shi yana ta nishadi.
Koda ta goge taga yaki goguwa ta bude kofa ta fita dagudu ta karasa bakin kofarshi ta kwankwasa,daga ciki akace "me kuma ko dukan ne bai ishe ki ba?".
"Yaya Hamma wallahi hannuna ke ta zubar jini please ka taimaka ka kaini chemist, in kuma kanada first Aid box (akwatin bada Agaji na gaggawa) ka bani mana na iya treating din".
Ya dan tausaya mata kadan yace "shigo ki dauka".
Da sauri ta bude kofar ta shige dakin batasan inda ake ajewa ba cikin tsoro tace "Yaya Hamma a ina yake?".
"A inda Kabeeru ya aje".
Ran Aisha ya sosu sosai saboda ita duk Abinda zakayi da ita batason ka zagi iyayenta sai kuma tace "please ka fadamin ban ganshi bane".
"Dama kina tsaye baki nema ba shi zai zo ya sameki ne?".
"A'a" ta fada a takaice sai kuma ta wuce ta fara zagayawa cikin dakin tana neman box din,kyalla ido tayi ta hango shi a gefen wadrobe sauri tayi ta karasa wajen ta dauka ta fice.
Tana shiga dakinta ta zauna a kan towel da ta shimfida ta fara bawa kanta Agaji.
Kusan minti biyar ta dauka tana gyara hannu saboda ba karamin zubar jini yake ba,bayan ta gama ne ta dauki box din ta kai dakin ta aje ta juya sumi-sumi zata tafi,tana karasawa bakin kofa taji Hamma ya kira sunanta da sauri ta juyo gudun kada yace tayi laifi.
Tsayawa tayi taji bai sake mata magana ba ta kuma murda handle din sai kuma yace "Au bazaki zo ba kenan kina tsaye?".
"A'a zanzo mana yayana naji baka sake magana bane ai".
"To sai a karaso ko a rika biyayya ga miji a samu Aljanna tunda ba'aji dadin duniyar ba".
Ran Aisha in yayi dubu to yau ya baci har taso taki zuwa sai kuma ya juya don maganarshi akwai kamshin gaskiya a ciki.
Koda ta karasa yace "yawwa miskiniya ta tausa nake so kimin koda hannu dayan ne zan hakura kimin".
Aisha ce ta fara yi mishi tausa tana hawaye masu zafi ta rasa me yake mata dadi sam rayuwar duniyar ta isheta wato wannan dalilin ne yasa Hamma yaki zama a yola kawai don yayi ta muzanta mata,goge hawayenta tayi taci gaba da tausan a haka har bacci ya dauke shi itama batasan lokacin da bacci ya dauke ta a dakin nashi.
*************
Khadeeja ce a daki tana salla Haidar ya shigo sumi-sumi jiki a sanyaye ya rasa meyake masa dadi,jikinshi yana bashi cewa Aisha Bata zaman dadi da Hamma domin shi a fili ya nuna baya son kuturuwa ya fadi cikinshi,zama yayi a bakin gado yana jiran ta idar.Khadeeja na idarwa ta juya ta dubeshi taga kamar baya lafiya, nade sallayar tayi ta aje ta karasa bakin gadon itama ta zauna ta sakale hannunta da nashi tace "yayana lafiya kuwa?".
BINABASA MO ANG
AISHA
Historical Fictionlabarine a kan wata yarinya mara hannu daya wacce take kaunar dan uwanta Amma shi baya sonta ko kadan.