24

106 12 11
                                    

AISHA

Walidation S Mapi

page 24

Mubin da Lateefa kuwa suna tafiya suna takunsu na masoya, Aisha ji tayi kamar ta janyo su, sun karaso wajen suna dariyar Aisha dake zaune rai a hade itama juyowa tayi ta kalle su taga sun matukar burgeta tace "don Allah wannan wani irin tafiya kukeyi ne? sai kace kuna tausayawa tiles din,ni wallahi bazan sha ice cream din a nan ba takeaway zamuyi".

Ba tareda sun kawo komai a ransu ba Mubin yace "to malama Aisha muje tunda an siyo kuma ai ke kika zabi wajen saida ice cream" murmushi tayi ta mike ta same su a tsaye taje gefen Mubin suka sashi a tsakiya itada Lateefa suka fice a wajen tana kallon Hamma da joy ana ta tafka fitsara,daga waje ta tsaya ta haska su a hoto dakyau kafin ta karasa dagudu ta samu su Lateefa da har sun shiga mota suna hira,itama shiga tayi da tunane-tunane iri-iri a ranta.

Suna zuwa kofar gida ta fice a motar ta yiwa Mubin sallama ta shiga gida,samun Ammi tayi a cikin gidan tana hada-hadan daura girkin yamma ta zauna a kan taburma ta yiwa Ammin sannu,ta bude roban ice cream dinta ta fara sha ta ajiyewa Lateefa nata,saida ta kusa rabi ta tuna cewa bata bawa Ammi ba sai ta bude ledan taga guda uku ne Kenan da Mubin a ciki, da sauri ta mike dagudu ta fito a gidan ta karasa wajen motarshi ta kwankwasa suka bude ta mika mishi ledarshi dama an hada a leda daya Amma kowanne da ledarshi,kin karba yayi da haka ta koma dashi ta mikawa Ammi itama dakyar ta karba dama can Bata saba da kwalam ba.

Suna gama hira Lateefa ta shigo gidan da tsallenta saboda yau Mubin ya bata kudi don akwai wani tafiya da zaiyi zai kwana uku,karasawa inda Aisha ke zaune tayi ta zauna a kusa da ita tace "baby girl yau fa aljihu ya cika".

Aisha ce ta dago kanta ta dubeta a hankali tace "ke haba?".

"Wallahi kuwa ke bakisan meya faru ba" Lateefa ta fada tana kirga kudinda aka bata.

Aisha tace "Meya faru Kuma Lateefa?".

Lateefa tace "ke kamar dubu hamsin na irga".

"Don Allah,to meya farun".

"Aisha akwai ki da son jin gulma,Mubin ne yace mu kawo takaddun makarantar mu zai sama mana aiki a Hamlam".

Aisha ta waro ido tace "ina ne kuma Hamlam?".

"Wata sabuwar babbar kamfani ce na wani abokinshi,yanzu zamu tura application letter ya bani email address din kamfanin".

Daga hannu samma Aisha tayi tace "Allah mun gode maka kuma kasa wannan Aikin shine Alkhairi a garemu,shi kuma ya saka mishi da Alkhairi ya kuma nuna min ranar aurenku irin wannan dawainiya haka da yake yi damu Allah ya biyashi".

Ameen kowa ya amsa dashi harda Ammi take ta tunanin irin wannan dawainiyar da Mubin yake dasu ya kamata kawai ya fito ya Auri Lateefar inda gaske yake,kusan shekara biyu suna tare Amma bai kawo maganar Aure ba.

Shanye ice cream din sukayi sukayi wanka suka kwanta dama Ammi ce meyi musu girki sam bata barinsu suyi,can da dare Fu'ad ya dawo Aisha da Lateefa sukayi dakinshi wai a fadarsu zasu tayashi hira amma ba shine yake kaisu ba Lateefa ce ke raka Aisha hira a wajen Fu'ad ita tayi chatting dinta,su kuwa susha soyayyar su har sai lokacinda suka gama suke dawowa su samu Ammi nan Aisha ta tuna da application letter dinda aka ce su tura tayi saurin fadawa Lateefa suka tuttura suka kwanta bacci abinsu.

Washegari tunda safe suka tashi sukayi wanka dama karyawa siya sukeyi,suna gamawa suka kwanta suna chatting dinsu kowacce tana murmushi lokaci zuwa lokaci domin Aisha da Yaya Fu'ad take hira shikuma yana office ya dan samu karin girma a wajen aiki,dinki kuwa ya bari tun da dadewa saboda me gidan nasu yana yi musu Abinda yaga dama, Aisha ce ta juyo ta dubi Lateefa dake cikin farinciki don Mubin na ratsa ta da kalaman soyayya "tattabara iyayen kauna" shine Abinda Aisha ta fada itama ta juyo taga sako ta email dinta ta karanta kamfanin Hamlam ne ya bukaci ganinsu,da tsallenta ta fadawa Lateefa itama a lokacin sakonta ya shigo,mikewa sukayi suka shirya don zuwa kamfanin Aisha himar tasa da nikab Lateefa kuwa cewa tayi ayi Mata kwalliya bazata iya zuwa tamfatsetsen kamfani kamar wannan ba Ado ba,dariya Aisha tayi mata tace "dama dai karfe goma ake bukatar ganinmu wallahi da yanzu ne sai dai ki hakura da kwalliyar".

"Nidai a daure ayi min saboda nayi kyau tunda ke kince matar malami ce".

"Me nayi na malamta a Nan?" Aisha ta tambaya tare da fara yiwa Lateefa kwalliyar.

"Gashi kuwa kin wani sanya hijabi da nikabi sai kace wata malama ko matar malami".

Aisha tace "in kinji haushi kema kisa".

"Haushi Kuma?haba dai Humaira don me zanji haushi don kawai kinsa hijabi da nikab ai nima inada su,kinga ni kimin kwalliya ta banson neman magana".

Murmushi Aisha tayi tace "sai kiyi ai" ta cigaba da yimata kwalliyar,cikin ya'n mintuna suka gama dama ba wani me yawa bane,nan Lateefa ta sanya kayanta suka yiwa Ammi sallama suka wuce.

Suna zuwa sukaga Ashe basu kadai bane sun kai talatin da haka suka ja gefe suka tsaya sun cire rai a samun Aikin saboda anyi yawa a wajen kowacce da takardu a hannunta kuma dukka mata ne,me kamfanin ne yake neman masu aiki kamar p.a dinshi da masu kawo mishi coffee sai masu kawo mishi Abinci.

Suna cikin tsayuwa sukaga wata farar mota me lafiya tazo ta gifta su ta karasa wajen aje motoci akayi parking dinta, kowacce a wajen saida ta kissima Abu a ranta banda Aisha da take waya da sahibinta tana ta murmushi,Lateefa ce ta juyo ta dubi Aishar tace "Humaira kiga wancan motar,wallahi ta matukar tafi da hankalina".

Aisha ce ta yiwa Fu'ad sallama ta katse wayar ta juyo ta dubi Lateefa da hankalinta ya koma kan motar baki daya cewa tayi "latee kodai motar ta miki ne".

"Ehh mana wallahi ba karamin daukar hankalina tayi ba kamar ace me motar ne Mubin".

Aisha tace "Come on my latee ki daina son abin duniya kinga Yaya Fu'ad baida mota kuma a haka nake son abina bana burin wata ta kwace min shi,shiyasa kikaga a koda yaushe muna like a way,kuma ai Mubin nada mota shima sannan da kin ganta kinsan me tsada ce".

"Hakane Amma wallahi motar tayi" Lateefa ce ta fada taci gaba da kallon motar ko kifta ido batayi.

"Ehh tayi sosai ma" Aishar ta fada tana sake duba sakonda Fu'ad ya turo Mata.

Mai motar ne ya ciro dayan kafarsa a hankali ya kuma fitarda dayan farar Kaya ce a jikinshi irin na zuwa aiki suit da wandonshi sai kuma bakin riga ta cikin suit din,bakin gilashi ne sanye a idanunsa sai kuma kuma farar takalmi day sanya,yayi matukar kyau sosai don daka ganshi zaka zaci dan indiya ne shi Amma ina cikakken bafulatani ne me jini a jika,hankalin ya'mmatan ne ya koma kanshi sunata ganin abin mamaki,wasu na tambaya Anya wannan bawan Allah a Nigeria yake rayuwa sauran kuwa duk sun maida hankalinsu kanshi sunata crushing a kan gayen,Lateefa ce ta taba Aisha ba tareda ta juyo ba tace "Humaira don Allah ki daga kanki kiga gayen nan wallahi ya tafi dani".

Aisha ce ta dago kanta taga ko wani gaye ne ya tafi da Ya'r uwarta haka,me zata gani Yaya Hamma ne sanye da fararen kaya ya rataya jaka a kafadarshi yana tafiya yana basarwa sai a lokacin taji sauran ya'mmatan na cewa "shine Reekado c.e.o din kamfanin" mamaki ne ya cikata fal dama taso tayi ihu Amma ta fasa gudun kada Lateefa ta gane wani abin sai kuma taji wasu na sake fadin "kamfanin shi ne ai shiyake neman masu aiki" so take ta tafi tace ta fasa kawai ta dake itama ta nuna batasan shi ba Amma tana ta tunanin dama Yaya Hamma yanada kamfani, a dai-dai lokacin ne ta dago kai ta karanta sunan da ke rubuce a jikin kamfanin taga Hamlam (Hamma Lamido kenan) mamaki ne ya cikata ta rike haba,da daddaya aka fara kiransu in kowacce ta shiga sai ta fito da kuka duk kwalliyar ta ya baci,saida suka gama fitowa babu wacce tayi nasara Aisha ta juya ta dubi Lateefa tace "kinga Lateefa mu tafi kawai tunda babu wacce tayi nasara,dame muka fisu?".

"Haba Aisha ya zamu sare bamu gwada sa'armu ba?kika san ko munada rabo?".

Aisha tace "To shikenan ke kifara shiga in kinyi nasara in shiga,in kuma bakiyi ba shikenan saimu Kama hanyarmu mu tafi".

Lateefa ce ta cire tsoro ta shiga office din c.e.o

AISHAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن