AISHA
Walidation S Mapi
17
~Ya bude mata kofar tana shiga tare da rufe kofar tana dariyar mugunta.
Ya'mmatan ne suka yo kan Aisha da gudu sunayi mata sannu a zatonsu ko har sun riga sunyi lalata da ita,fashewa da dariya Aisha tayi tace "sisters babu Abinda suka yimin sai ma ni da nayi maganin shegu".
Girgiza kai daya daya cikinsu tayi tace "ba dai wadannan mugayen kikayi maganinsu na,mufa mun sansu infact ni shekara ta uku dasu amma babu wanda ya taba koda zaginsu sai kece zaki wani ce mana kinyi maganinsu".
Daya daya cikinsu wacce suke kira princess ya'r sarkin katsina ce da aka sace shekara biyu da suka wuce tace "kuci gaba da jinta banida time din shegiya".
Fiddausi ce tace "haba princess ya zaki kirata shegiya bayan gashi tana da shirin taimakon mu ke meyasa kike da mugun hali ne".
"Ni kike kira da mai mugun hali ko?".
"Eh nafada mugun hali ne dake, nifa Abinda kike mana ya isa haka ya kamata kisan cewa nan ba masarautar ku bane may be ma ba a katsina muke ba ya kamata kisan wannan".
Princess Sadiya ce tace "idan kuma naki fa".
"Wai hausawa suka ce gyara halinka ko kuma kaci kaniyarka".
Hannu princess ta daga da niyyar marin Fiddausi,Aisha ce tayi saurin mika hannu ta tare ta tace "ya isheki haka malama,ya kamata kisan cewa sarkin yawa yafi sarkin karfi don haka ki kiyaye".
Sauke hannu princess Sadiya tayi tace "duk kunyi kadan wallahi kuma zamu fita a nan watarana sai na nemo Adireshin kowace shegiya na gallazawa iyayenta Azaba".
"Kima samu ki fita a nan din mana banza kawai" Aisha ce ta fada a fusace.
Suna gama haka Aisha ta rika yi musu tambayoyi a kan musulunci ta lura da cewa mafi yawancinsu basu iya komai ba sai hudu daga cikinsu daga gani sun karantu.
Zama Aisha tayi ta rika fayyace musu abubuwa dangane da addinin musulunci ta kuma kara musu karatun al'qur'ani mai girma a hankali suka fara dauka harda princess da ta sauke kanta saboda ta lura cewa babu wanda zai sake daka ta izzar ta.
Sai da Aisha ta tabbatar sun fahimci abu dayawa ta kuma sanar musu da cewa insha Allah baza ta sake bari a sa musu maganin feelings ba,ta mike ta baza gashinta ta fice daga dakin tayi waje.
Tana fita taga mutanen nan biyu zaune suna ta shawara a tsakaninsu.
Aisha ce taje tsakiyarsu ta tsaya tace "meyasa zaku kama bil'adama ya'n uwanku ku rika adana su a nan babu dalili?".
"Wallahi ranki shi dade kawai Amfani muke dasu kuma muna tsoron idan muka sake su suka tafi zasu iya kawo mana matsala Amma wallahi bama wani cutar dasu".
"Wani irin cuta ne bakwa yi musu bayan gashi kuna sasu Aikata mafi girman laifin da Allah yafi tsana".
"Wallahi mu bamu san me suka yi ba".
Aisha ce tayi musu tsawa tare da cewa "karya kuke banzaye munafukai zaku rika zubawa mata maganin feelings sannan kuce baku San me suke yi ba wallahi na fatattake ku mutanen banza kawai".
Dayan ne ya mike da wuri ya shiga bawa Aisha hakuri yana rokonta don Allah ta barsu kada ta cutar dasu.
Aisha ce ta girgiza kai tace su fice subar mata dakin cikin gaggawa,da sauri suka mike sukayi falo tare da sake-sake a ransu,Aisha ce ta ja bargo ta kwanta tare da kwatanta dariyan Aljanu tayi bacci Abinta.
************
Hamma ne da joy suke ta yawo cikin garin sun rasa inda zasu je su nemi Aisha yau wajen kwana biyu kenan da batar ta duk ya rasa me yake masa dadi a ranshi kuwa cewa yayi duk daddy ne ya jawo mishi wannan in ba haka ba da yanzu suna zaune da matarshi a family hankalinsu kwance.
YOU ARE READING
AISHA
Historical Fictionlabarine a kan wata yarinya mara hannu daya wacce take kaunar dan uwanta Amma shi baya sonta ko kadan.