AISHA
Labari/rubutawa:
Waleedatu S Mapi.8
_______Can taji karar tsayuwar mota,da sauri ta fito ganin waye.
Tsayawa tayi tana jiran taga me fitowa,Hamma ta gani da wani Abokinshi sun fito daga motar,da sauri ta bar wajen tayi ciki ta samu waje ta zauna a falo.
Suna shigowa sukayi ido hudu da ita,rusunawa tayi ta gaishe su a dakile Hamma ya Amsa dayan kuwa cikin fara'a ya Amsa ya dubi Hamma yace "Abokina kace da cheese kazo?"
Hamma ne ya dube shi a kaskance yace "guy ka gane wannan ba kayana bane,baka ganinta wata so dirty ne?"
"Ni banga dirty a nan ba yarinya ga kyau ga diri everything normal,ai nasan kana ganin yawa ne don batada hannu daya,guy wallahi ka zage kayi Aiki yarinya tayi a ina ka samo ta?"
"Kai Abdul bafa kayana bane nace maka house girl (ya'r Aiki) na dauko ta tun daga yola"
"Woooow Amma yarinyar tayi wallahi,ko zaka bani ita ne Nima tayi min Aiki na kwana biyu......"
Bai karasa zancen ba Aisha ta ruga daki da gudu tana kuka.
Abdul ne ya dubi Hamma yace "lafiya kuwa Aboki na?"
"Ehhh tanada matsalar Aljanu ne bata son yawan ganin mutane haka take".
"A lalle dole mu saba da ita don ba karamin kaya ne a nan ba"
Dayake Hamma bai san darajar Aure ba kuma bai san darajar Aisha ba sai yace "ba damuwa jibi sai nabaka Aronta taje tayi maka Aiki".
Cikin farinciki Abdul yayi tsalle yace "thank you Abokina,shiyasa fa kake burgeni kaf Abokananmu kaine kanka yake kawo wuta".
"Never mind guy,ai kai nawa ne normal ne ai".
Aisha na cikin kuka a daki ta tuno cewa bata ci Abinci ba,saurin mikewa tayi ta nufi falo,karasawa wajensu tayi ta tsuguna tace "yallabai dama so nake na fada maka babu kayan Abinci kuma nima banci Abinci ba"
"Ohhhh God Hamma ya zaka barta da yunwa?gaskiya baka kyauta ba, yanzu haka kake so ta yankwane ai ba za ta iya min Aikin da zata zo yi din ba".
Hamma ne ya dube shi irin kallo ka Dame ni yace "in kaga zaka iya saya mata Bismillah".
"Au kenan ma bazaka siya mata din ba?to wallahi idan ta zo min Aikin bazata dawo ba don zan rike ta tsaf".
"Sai kayi ai"
Abdul ne ya juyo cikin murmushi yace "Beb tashi kije zan kawo miki kayan Abinci yanzu da kuma wanda zaki ci nasan kinajin yunwa.
Aisha ta rasa wanne Aiki ne wannan bawan Allahn yake ta nufi sai ta mike ta tafi kamar yadda yace.
Tana shiga daki ta karasa wajen akwatinta ta dauki wani towel ta shimfida ta kwanta tare da zubarda hawaye me tsuma zuciya.
Abdul ne ya mike cikin sauri ya tafi siyowa Aisha Abinci da kuma kayan Abinci.
Can zuwa Anjima ya shigo gidan ya kira Hamma ya taimaka mishi su shiga da kayan,haka Hamma yaki yace idan dai wa wannan kuturuwar zan shigarwa kaya gwara nima na zama kuturu wallahi.
Da kyar Abdul ya gama shiga da kayan,bai ko dubi inda Hamma yake ba ya nufi dakin Aisha da take-away dauke a hannunshi,sallama yayi ya murda handle ya shige dakin,mamaki ne ya cika shi ganin bakomai cikin dakin tausayin Aisha ne ya cika shi yadda yadda ganta a kwance ta wani kanannade Alamar sanyi take ji,bude baki yayi a hankali yace "baiwar Allah tashi kici Abinci"
A firgice ta juyo ta dube shi sai kuma ta sauke kai kasa tana kallon kayan jikinta.
Karasawa yayi wajenta ya zauna gefenta yace "gashi wannan naki ne ke kadai".
Da sauri ta karba don tasan Abincin ne ya siyo a gabanshi ta bude take-away din,shinkafa ce da jar miya sai kuma kaza guda daya da kuma juice kala biyu,ko kunyarshi bataji ba ta fara ci don yunwa ya matuk'ar galabaitar da ita.
Ci take sosai da yaga Alamar ba tsayawa zatayi ba yace "baiwar Allah ni zan tafi Amma gobe zan dawo,idan kuma zanzo zan taho miki da katifa...."
"Bakada hurumin wannan!!!" Hamma ne ya fada a tsawace, saboda duk Abinda yake fada yana jinshi a bakin kofa.
"Saboda me Abokina?" Abdul ne ya tambaya.
"Nace bakada hurumin wannan ko sai kaji dalili?"
"A'a ba sai naji dalili ba,Amma ya kamata kasan darajar dan Adam wallahi, bakada tausayi ko kadan,yanzu a nan kake so ta kwana?kawai don tana ya'r Aikinka".
"Ehh ko zaka taya ta kwanan ne?"
"A'a ai ya'r Aikinka ce kai keda hakki a kanta Amma ya kamata kasani wallahi dan Adam ba Abun a wulak'anta bane wawa kawai mara tunani".
"Abdul yau ni kake zagi saboda wannan banzar kuturwar?".
"An zage ka din wawa,mara tunani".
"Okay yayi kyau gata sai ka cinye ta danye,sai kuma kabar min gida yanzu".
"Ok gida dai kasan inada irinta sak bazaka min gori ba,Amma ya kamata kasani cewa watarana zaka neme ni". Abdul na gama fadar haka ya fice ya tafi.
_Kuyi hakuri da rashin post da wuri hakan ya faru ne sakamakon kasala da nake dashi,ku Kara hakuri da wannan kadan in,yau ina birthday ne shiyasa nayi kadan._
Walidation S Mapi
أنت تقرأ
AISHA
أدب تاريخيlabarine a kan wata yarinya mara hannu daya wacce take kaunar dan uwanta Amma shi baya sonta ko kadan.