AISHA
LABARI/RUBUTAWA:
WALIDATION S MAPI.19
Dama akwai ya'n canji a wajenta ta tari Napep sai gidan sarki.
Tana isa taga kofar gidan a cike tam da mutane,mamaki ne ya kamata saboda ganin yawan mutanen ya sata mamaki,cikin mutanen ta fara kutsawa tana neman hanyar da zatabi taje ta nemo Princess,tana isowa wajen wasu samarai suna tsaye wani ya rike mata hannu yana murmushi,ihu taso tayi dayan kuma ya toshe mata baki ga mutane Amma ba damar taimakawa saboda kowa hankalinshi baya jikinshi,tana ta kokarin zillewa don kwatar kanta Amma inaa sunci karfinta don maza ne guda uku karfafa,suna cikin hakan sukaji saukar bulala a jikinsu Wanda ya dawo da hankalin kowa izuwa garesu,saurin sakin Aisha sukayi ta fadi a kasa suka fara kokarin guduwa Amma inaa,dogarai sunfi karfin don ko gudun second uku basuyi ba aka kamosu,Aisha ce ta mike tana dingishi dakyar-dakyar kowa na kallonta duk kunya ya ishe ta hakan yasa taja mayafinta ta rufe fuskarta dashi,kafin ta karasa wajen Princess ta sauko daga kan kujerarta ta karasa inda Aishar take,ta rungume ta,yin hakan da tayi ne yasa su fiddausi saukowa suma suka rungume juna suna kukan farinciki,kowa yaji dadin yadda suka rungumu abin ban sha'awa Aisha ce a tsakiya saura na rungume da ita.
"Ya kamata ki samu waje ku zazzauna tunda yau ranar farinciki ne a gareku ba ranar kuka ba" sarkin magana ne ya fada musu.
Sakin juna sukayi kowa ya nemi wajen zamanshi ya zauna, Aisha da batasan inda nata wajen zaman bane yasa ta fara waro ido kamar wacce tayi sata,Nan ta ankare da wata kujera da aka rubuta Aisha yanayin rubutun ya matukar dauke hankalinta don ba karamin kyau yayi ba fonts din da calligrapher yayi Amfani dashi me matukar kyau ne,cikin guduwa me dauke hankali da Sanya nishadi taje ta zauna kan kujerarta Amma har yanzu fuskarta a rufe don tana matukar jin kunya.
Fiddausi ce ta mike tayi takaitaccen bayani a kanta ta kuma fadi yadda akayi ta fada hannun su Mudi, tana gamawa wata ta amshi mic din saida kowacce daga cikinsu tayi sannan mic ya shigo hannun Aisha mikewa tayi a hankali ta sake daure fuskarta sosai ta amshi mic din.
"Assalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuh, blessing be to God the almighty...." Kamin ta kara kalma daya sarkin magana ya tsayar da ita yace,"malama rabin ya'n garinmu basuyi makaranta ba ko zaki yi mana yaren Hausa".
Daga cikin mayafinta tayi murmushi tace "zan iya sai dai hausar ce ba kyau,niba bakatsiniya bace bafulatana ce".
"Tabbas bakida hausa! Amma kiyi mana dashi insha Allah zamu fahimci abinda kike nufi" ya mayar mata.
"Yadda kace haka za'ayi ranka ya dade"Aisha ta fada cikin raha.
Murmushin dattako yayi ya zauna ya maida dubanshi izuwa ga yarinyar,inda sauran mutane kuma ke mamaki wai nakasasshiya ce da jin yaren turanci.
"Bayan sallama da gaisuwa a gareku,ina yimuku fatan Alkhairi a koda yaushe,da farko dai sunana Aisha Kabeer ni haifaffiyar garin yola ce a can na girma nayi primary and secondary school dina bayan nan ban cigaba da makaranta ba,yanzu a haka inada Aure a nan garin....." Ta kasa cigaba da magana don hawaye ne yake sirnana cikin idanuwanta nan ta Mika mic din batare da ta sake magana ba ta zauna tana kuka.
Princess ta lura da halinda Aishar ta shiga yasa ta amshi mic din ta fadawa kowa abin Alkhairin da Aisha tayi musu da kuma kwananda tayi a gidansu Mudi akayi tafi ta zauna.
Aisha na dago kai taga Mudi da dan uwanshi suna tafawa,mamaki ne ya cikata saboda ganinsu da tayi a jerin manyan Alhazai na garin katsina,saurin mikewa tayi taje ta nunawa Princess su,mamaki Princess tayi sosai saboda su basa ganin fuskar su Mudi ko abinci zasu kawo musu sai sun tabbatar fuskarsu a rufe Amma gata ta ganesu kodai ta taba ganin fuskokinsu ne? "Ni ai kullum ina ganin fuskokinsu" kamar tasan me Princess take tunani, nan take princess ta mike ta karasa wajen babban yayanta ta sanar mishi a sirrance ta Kuma bada shawarar yadda za'a Kama su.
YOU ARE READING
AISHA
Historical Fictionlabarine a kan wata yarinya mara hannu daya wacce take kaunar dan uwanta Amma shi baya sonta ko kadan.