AISHA
Walidation S Mapi
11
~Suna cikin magana sukaji ana kwankwasa kofa,da sauri Hamma yaje ya bude saboda yanada tabbacin babu me zuwa musu gida,Abdul da suke shiri dinma sunyi fada.
Yana budewa wa zai gani?Abdul ne tsaye da katifa number one a kanshi sai kuma wani leda baki da ya rike a hannunshi da bai yadda suka hada ido da Hamma ba yafara kokarin shiga da katifar.
Tunkude shi akayi saida ya fadi a k'asa ledar hannunshi ta zube abin cikin suka bayyana,soso ne da sabulu da kuma man shafawa sai ice-cream da biscuit dogaye guda biyu,da kuma pad guda daya.
Da mamaki Abdul ya mike ya dubi Hamma yace "wai Hamma rashin hankalin naka ya kai haka ne?meyasa bakada tausayi ne?kai baka ganin mace ce ita?meyasa kake son kuntata maka?Anya ma ya'r Aikin ka ce kuwa?lalle akwai Ayar tambaya a kanka, Hamma indai ka tsani yarinyar nan bazaka dauketa a matsayin ya'r Aikinka ba dole akwai wani abu".
"Ehh akwai wani abu sai ka fice da tsamin kayanka ka barmin gida stupid".
"Zan fice Amma bazan fice da kaya ba yadda nazo dasu haka zan barsu, sannan kasan cewa niba stupid bane sai dai in kaine stupid, nonsense and idiot namijinda baya tausayin mata".
"Abdul tun kamin ranka ya baci ka fice da kayan nan domin banason fitina da kai,wannan gidana ne don haka ka barni nayi rayuwata".
"Hakane gidanka ne Amma kaima kasan cewa idan Abu ya kulle maka ni kake nema in warware maka don haka ina me tabbatar maka da cewa watarana zaka neme ni,kaya kuma bazan tafi dashi ba,in bazaka bata ba ka kaiwa Almajirai".
Abdul na gama fadan haka ya juya ya fice yabar gidan.
Hamma ne yayi saurin daukar katifar ya karasa wajen dakin me gadi dashi yafara kokarin budewa,Aisha ce tayi sauri ta karasa inda kayan ciye-ciyen suke ta diba iya wanda take so ta kai dakinta dagudu ta ta boye ta kuma koma dakin Hamma ta zauna kamar ba inda taje.
Yaje tattare chops din yaga sun ragu, dube-dube ya fara baiga kowa ba dai ya hada su waje daya ya shiga ciki dasu,dakinshi ya nufa ya samu Aisha a inda ya barta.
Dago kai tayi ta kalle shi tace "Yaya Hamma lafiya kuwa wanene yazo?".
"Ya akayi kikasan namiji ne yazo?".
"Mmmm,mmm dama naji kana hayaniya a waje shiyasa na tambaya Amma kayi hakuri".
"Wuce kitafi dakinki banson gulma".
"Sumi-sumi ta mike kamar wacce kwai ya fashe a cikinta ta murda handle kenan yace "zoki karba".
Komawa tayi cikin sauri kada yace tayi laifi,tana tsayen taga ya mika mata wani minti karami irin na goma-goma guda daya yace gashi kije kisha tunda dazu kukan yara kikemin".
Ba karamin kuluwa Aisha tayi ba saboda ji tayi kamar ta maida mishi,ga karami ga bakar magana lalle Hamma baya sonta ko kadan" karba tayi ta fice saboda kada yayi mata tsawa.
Tana fita tayi daki tare da farinciki don tasan zai hanata yasa ta diba me isanta,sakata ta saka ta fara ciye-ciye kamar me yunwa.
Tana fita yaji wayarsa na ruri da sauri ya mike don bata agajin gaggawa daddy ne ke kiranshi,dagawa yayi ya Kara a kunnensa tare da cewa "hello Dad".
"My son yakake fatan komai lafiya?".
"Ehh lafiya kalau daddy everything is moving successful wallahi".
"Wooooow dagaske?ya wancan miskiniyar to?".
"Tana lafiya wallahi daddy jiya ne ma na ji mata ciwo a hannu bakaga yadda jini ba har kuka tayi min".
"To baka tunanin zata fadawa ya'n gida Abinda ke faruwa?".
"Ai muna shiga katsina na kwace wayarta,sam na hana ta saboda ban yadda da ita ba kuma wulakanci sai wanda naga dama nake yi,daddy bakaga yadda ta rame ba wani sa'in har tausayi take bani".
"Kada ka sake ta baka tausayi balle ka bata mana shiri,domin mace ba karamar Aljana bace,zata iya rinjayarka sannan ina yimaka Albishir da cewa game start,yanzu aka fara wasar".
"Daddy kuturuwar?haba me zanyi da ita God forbid wallahi babu Abinda ya kaini taba kuturuwa ita a suwa?".
"Yawwa dana haka nake so yanzu kashe waya zanfita domin yau zan fara buga wasar".
"Ok dad i love you,bye".
Bai jira Amsarshi ba ya kashe wayar ya juya ya dubi mommy yace "nagama da wannan wutar nasan bazai taba kulata ba balle so ya shiga cikin lamarin nan, kinsan so babu Abinda bata sawa".
"Hakane Alhaji shiyasa ai na lura da soyayyata ce ta rufe maka idanu kake Aikata wadannan".
Murmushi yayi ya rungumota yace "kullum dama idan nace mu maida sabuwar soyayyarmu cewa kike in bari yara na ganinmu yanzu kuma naga ba yaran kinga zamu koma honey da darling kamar da ko?".
Dariya tayi mishi tace "to my honey hakan za'ayi".
Janyo ta yayi yace mushiga ciki.
********
"Yau fa sai kun kiramin mesuna naji ya take saboda inji muryarta kozan samu sadida a zuciyata,ace yarinya wajen sati daya babu waya, shi Lamidon bazai bata shawaran ta kira gida taji lafiyarsu ba, shikenan don yarinya tayi Aure ta fara wani girman kan tsiya duk sanda aka kira waya a kashe,shiyasa ai nace muku ku daina soyayyar shan minti a idon yara yanzu gashi yaja hankalinta yasa ta kashe waya". Inna ce take ta zabga ruwan bala'i cikin bacin rai.Tsayawa tayi jin babu wanda ya fara bata hakuri a cikinsu sai kuma tace "Au idanu zaku zubamin kenan?bazaku kirata ba?".
Alhaji Kabeeru (Abban Aisha) ne ya daga waya ya kira tsohuwar layinshi data bata kamar yana kiran Hamma ne sai suka faraji dogon bayanai wayar a kashe,dago kai yayi yaga Inna saboda wayar a handsfree take.
"Mtswwwww ni zaka yiwa katsalandan?ya zaka kira wani layi kuma kacemin Lamido ne?".
Mamaki ne ya kama Abban Aisha sai kuma yace "haba Inna meyasa bakya taba yadda dani ne wai?".
"Bawai yadda dakai ne banayi ya za'ayi ace yarinya tun tafiyarta bamuyi waya ba?ai akwai abin dubawa a nan" ta fada tare da fashewa da kuka.
Sai a sannan jikin Abban Aisha yayi sanyi saboda tabbas Inna nada gaskiya sosai,ai idan Aisha taki yin waya da kowa to dole zatayi da Anti Amarya domin suna matuk'ar shiri sosai,jikin kowa ne yayi sanyi a falon,umman Aisha ce ta wayance tace "kunga kowa yaje ya kwanta dare yayi".
Haka kowa ya mike ya tafi tare da dariyar maganar Inna.
YOU ARE READING
AISHA
Historical Fictionlabarine a kan wata yarinya mara hannu daya wacce take kaunar dan uwanta Amma shi baya sonta ko kadan.