AISHA
Walidation S Mapi
13
~Basu taba kawowa kansu cewa Inna zata yanke wannan mummunar hukuncin ba.
*********
Zaune take gaban madubi tana make-up yarinya ce da bazata wuce shekara Ashirin da biyu ba daka ganta zaka san unguwa zata Amma saboda irin dressing da tayi me bala'in kyau gata doguwa ga hanci idanunta dara-dara gashin giranta kuma a tausashe take me bala'in yawa daka ganta zaka tabbatar da irinsu ne ake kira black beauty,gashin dokin nan ta cika kanta dashi ta kuma sanya riga da wando bakake, inka ganta zaka zaci cewa musulma ce saboda tana wasu Abubuwan kamar musulmai saboda mafi yawancin kawayenta ma musulmai ne,Joy kenan wacce ta fito daga gida don yawon karuwanci daga waya tayi ta kara a kunnenta."Hello".
Daga daya bangaren kuma aka Amsa mata da "baby gani a kofa tun dazu nake jira ko zaki fito".
"Sorry Reekado gani nan zuwa yanzu".
"Ai ya kamata kiyi sauri mu tafi".
"Ok shikenan kabani second Ashirin zaka ganni".
"Nabaki talatin sai kiyi ki fito don na gaji da jiranki".
"Ok Beb" tana gama wayar ta suri jakarta tayi saurin fita ta rufe gidan ta karasa wajen motarshi.
Bude mata yayi ta shiga gidan gaba tun a lokacin ta wani ririce don yau ba karamin kyau yayi ba saboda fulantakarshi ta fito sosai kana ganinshi zaka gane cewa wannan cikakken bafulatani ne.
Juyowa yayi yaga yadda take kallonshi hade rai yayi yace "ke meyasa kike son zubarda Ajinki ne?".
"Baby menayi kuma? kawai don ina kallon product nawa?".
Dariya ne yaso ya kwace mishi sai kuma ya make saboda bayason ya zubarda class nashi a wajen ya'mmata.
"Dalla ni ki daina kallo na kada ki cinye min kyau na,kuma bance kada ki kuma zuwa wajena da cingam ba?".
Dariya ne tayi wanda ya kara mata kyau sai kuma tace "Wai kai har kana da wani kyaun da za'a cinye shi ne? Allah sawwake nama daina kallonka" ta cire cingam din ta rike a hannu saboda batada niyyar yarwa.
A haka suka iso gidan suna hira sama-sama saboda shidin ba wani me yawan surutu bane,sai fadan tsiya,fita yayi ya bude musu kofa saboda babu me gadi a gidan,dawowa motan yayi ya ja suka shiga ciki a Ajiye motar a harabar Ajiye motoci.
Fitowa sukayi hannu a sarke kana ganinsu kaga masoya saboda ba karamin k'aunarshi Joy take ba.
Aisha na zaune a falo ta tisa tv a gabanta,inka ganta zakace kallo take Amma ina hankalinta sam ba'a kan tv yake ba gida kawai take tunani.
Ji tayi kamar tafiyar mutane biyu yasa ta juyo me zata gani Hamma ne tsaye da wata mace da ka ganta zakasan karuwa ce saboda wani irin kallo da take da kuma yanayin cin cingam nata saboda tunda taga mace a gidan ta maida cingam din baki.
Dafe kirji Aisha tayi tace "yaya Hamma mezan gani?".
"Me kika gani kuwa?".
"Ganinka nayi kamar da mace".
"Wooooow Ashe yarinyar tana gani da kyau, baki bata ba nida baby na ne, lafiya kuwa?".
"Amma Yaya Hamma ka kyauta kenan Ashe kana zuwa katsina da biyu ne?".
"Ke dalla niba sa'anki bane banson doguwar magana".
Joy ce ta juyo a fitsarance tace "Reekado who is this?".
"Sorry beb she is my house girl bakiga yanayinta ba".
"But you look alike".
"Yeah itama ai a Yola take kuma kinga jinin fulani ne".
Bata wani yadda dashi ba tace "ok let's go in nifa yau na kagu".
"Okay Beb".
Suna shiga yaji muryar Aisha na cewa "wallahi bazan juri wannan cin fuskar ba abin ya ishe ni haka kuma niba house girl bace matarshi ce ni".
Saida ya leka yaga Joy tayi cikin daki tana kokarin kwanciya kan gado yasa ya koma ya karasa wajen Aisha ya rike mata kunne sosai.
Ihu ta saki tana rokonshi don Allah ya barta, bai bi ta kanta ba yaci gaba da sha kafin yace "Ni zaki yiwa katsalandan Aisha, ni zaki tonawa asiri?".
Hakuri taci gaba da bashi don kunnen yana matukar yimata zafi kamar zai tsinka.
Saida ya tabbatar ta ji zafi sosai kafin yace "maza ki wue kicin ki dafa mana irin wancan indomie da kikamin kwanaki ki kawo mana cikin gaggawa, in kuma kika ki yi ko kuma kika canza kika yimin wani girkin bashi ba, yarinya sai kin yabawa Aya zakinta saboda irin na kwanaki zanyi miki".
Sake ta yayi ita kuma tayi saurin nufar kicin don girka musu Abincin domin tasan karamin Aikin Yaya Hamma ne ya kuma maimaita Abinda yayi matan.
Komai da komai ta tanada don ganin ta gama girkin da wuri,cikin mintunan da basu wuce Ashirin ba ta kammala komai ta nufi dakin nasu dauke da plate guda biyu a hannunta, kutsa kai tayi ba tare da tayi sallama ba saboda tasan yanayin da zata tsince su a ciki, kamar bakinta saboda ba'a yanayi me kyau ta same su Ajiye musu tayi tareda cewa "ranka ya Dade nagama".
Shiga haiyacenshi yayi kafin yace "okay jeki bamu son sa ido".
Kamar yasan kallonsu take ta fice a dakin cikin sauri kafarta yana sarkewa saboda haka kawai taji tana matuk'ar kishin Yaya Hamma.
Tana fita ta fadi kasa ta suma saboda cutarta ta tashi gashi kuma Bata tuna daukar magani a gida.
YOU ARE READING
AISHA
Historical Fictionlabarine a kan wata yarinya mara hannu daya wacce take kaunar dan uwanta Amma shi baya sonta ko kadan.