7

98 17 0
                                    

AISHA

Walidation S Mapi

Shafi na bakwai

________Asibiti akayi da ita don likitoci sunce idan tayi tari da jinin a kawo ta Asibiti in babu batayi tari ba kada a kawo ta.

Suna zuwa aka nufi Emergency room (dakin taimakon gaggawa) da ita aka fara bata kulawa.

Umman Aisha da Anti Amarya sai hawaye suke suma a matukar tashin hankali suke,gashi likitoci sun hana su shiga duba Aishar,lekawa Anti Amarya tayi taga har oxygen (abin shakar numfashi) ak sanya mata,ihu Anti Amarya ta saki tana fadin "Aisha kada ki mutu,ki tashi Aisha me suka daura miki please ki tashi Aisha na".

Umman Aisha ce ta karasa kusa da window da Anti Amarya ke leken Aishar itama zuciya a raunane ta fasa ihu.

Akyar Haidar ya samu ya kwantar musu da hankali saboda shine ya kawo su Asibitin.

Bayan Awa uku aka fito musu da labarin cewa Aishar ta samu bacci kada su samu damuwa,sai a sannan hankalin su Umma ya kwanta,ta umurci Haidar da ya koma gida  kememe yaki komawa haka ta kyale shi sai dare yabar Asibitin.

Kwanan Aisha hudu a Asibiti Ummanta da Anti Amarya ne suke kula da ita,a Rana ta hudun suka samu sallama.

Koda suka dawo gida aka Kara sanar musu da cewa tafiya gobe ne ba fashi.

Da tausasan kalalamai Anti Amarya ta samu ta ja ran Aishar bata tada ciwon nata ba.

Da dare Aisha taje dakin Inna ta kwanta kan cinyarta tana kuka me tsuma rai tace "takwara kince zaki bani labarin Asalinmu, Amma har yau kin kasa bani,kuma gobe zanbar gidannan ba tare da sanin Asalinmu ba"

"Kiyi hakuri takwara yau zan baki labarin Asalinmu kinji" Inna ce ta fada tare da shafa gashin Aishar.

Asalinsu

k'auyen Rumdakila shine asalin k'auyen su kakanku,Malam Auwalu ne wanda ya fara kafa wannan Ahalin,wato kakanku mijina kenan,fulani ne shi usul,iyeyensa sun rasu babu wanda suka barshi dashi sai kaninshi guda daya shine Lamido sai kuma Arzikin shanaye da kuma yawan tumakai,y'an uwan iyayensa basa sonsu ko kadan wulakanci kala-kala babu irin Wanda ba'a yi musuwannan shine dalilin da yasa ya dauki kaninshi guda daya ya kuma kora shanayen su day dabbobinsu sukayi gaba saboda koda yaushe ana kan yimusu satar shanaye da kananan dabbobi,babu inda suka nufa sai Ganye garinmu kenan babu wanda suka sani a garin sunyi kwana uku a wani kafaffen tanti babu wanda ya gansu shanayensu kuwa sun garkame su waje daya babu wanda ya gani,kwatsam rana daya Allah ya hadasu da wani Baffa Hamma yarda (kanin mahaifina) ya dawo dasu gidanmu da zama,a lokacin wulakanci iri-iri nake fuskanta daga wajen matar kanin mahaifin nawa saboda kwata-kwata bata k'aunata batason farinciki na tunda iyayena suka rasu sanadiyyar hatsari da sukayi a birni,komai na samo daga wajen samarai saboda farinjini ne dani kamar fure,Amshe shi take ta baiwa Mairoji y'ar ta samarai na kuwa da sunzo gidanmu sai tasan kitimurmurar da zatayi ta rabani dasu ta kuma hadasu da mairoji,ana nan kuwa Baffa yake tambayarsu Asalinsu nan suka bashi labarin yadda akayi suka bar garinsu da yadda dangin iyayensu suka tsane su,jikin kanin mahaifina ne ya mutu saboda labarinsu kamar shigen tawa ne,a lokacin Gwaggo Larai matar Baffa na ta yanke shawarar hadani da Malam Auwalu Aure kawai don ta bakanta min rai a lokacin batasan cewa yana da shanaye da tumakai ba,haka Baffa na ya Amince saboda ta riga ta mallake shi sai Abinda ta fada a gidan,Anyi Aure na da Malam Auwalu tun Ina y'ar shekara goma sha hudu shi kuwa yana da shekaru Ashirin a duniya,ba'ayi ko kwana uku ba yace zai kara gaba,kinsan fulani basa zama waje daya kullum cikin yawo suke musamman fulanan jeji,cikin farinciki Gwaggo Larai ta Amince saboda bata son ganin inuwa ta a gidan ko kadan,haka kuwa akayi washe gari na shirya tsaf da y'an kayayyaki na a kulle cikin dankwali na fito kenan sai ga Malam Auwalu da Lamido sun koro shanayensu da dabbobi sun shigo dasu cikin gari kowa sai mamakin yawan dabbobin yake,Gwaggo Larai kuwa duk bakin ciki da kyashi ne ya cika ta Nan Malam Auwalu ya dibi shanaye guda biyar da Akuyoyi uku ya kyautarwa Baffa na muka kara gaba.

AISHAМесто, где живут истории. Откройте их для себя