4

87 21 0
                                    

AISHA

Walidation S Mapi

4

________Kowa ya kasa magana a wajen kuma sun san Inna da magana daya ko daga baya kuka kebe kukace ku masoya ne bazata Amince ba sam.

"Daya!biyu!uku,nagama zance,ke Maleeka da Hadiza (Khadeeja) kenan na bada ku wa Gadanga,ke kuma Yusra kanwar Haidar kenan uwa daya uba daya,wacce bayan Aisha da Fatima a cikinsu babu wacce kaita hakuri na bada ke wa Ummaru (Faruk),ke kuwa Fatima na bada ke wa Nasuru,mesuna kuwa na hada ta da mesunan Lamido (Hamma wuro) ita kuwa mesunan Maman Baba (Amina) na hadata da Salihu dan wajen Safiyanu yaron Lamido,wani sati za'ayi bikin,fakat inji balarabe magana ta kare a tashi a watse a bani wuri"

Kafin Inna ta kara wani zance kowa ya fashe da kukan da yake boyewa a dakin Aisha kuwa somewa tayi jin wanda aka hada ta dashi.

Rikicewa iyayen nasu sukayi kowa ya bi kan danshi inda Inna ta tsaya kan Aisha ta wani rike kwankwaso tana jimami.

Kowa ya nufi dakinshi da danshi a hannu inda Gadanga ya wuce dakinshi jiki a sanyaye babu kwari saboda yasan dalilin faduwar Aishan.

Daki akayi da Aisha aka bata maganinta ta shaka saboda yanzu sun daina kaita Asibiti domin ko Asibitin sukaje babu Abinda suke bata sai maganin tana shaka kuwa za'a sallame su kuma su caje su kudi,kwantawa tayi luff ta fara bacci Anti Amarya na gefe tana ta kuka kamar yarinya saboda batayi zaton Inna zata zabawa Aisha mutumin da tafi tsana ba.

Maleeka faduwa tayi kan gado tana ihu Gwaggo Rabi bata tambaye ba saboda ita tasan suna soyayya da dan yayanta Nasir amma zabin Inna duk ya baiyi ba ta cuci yaran.

Khadeeja,mamanta daddy, da Kuma Hamma wuro da Amina ne suka wuce part nasu suka zauna a falo Amina da Hamma wuro sai kuka suke ransu duk ya baci Khadeeja kuwa ko a jikinta tunda masoyinta aka zaba mata muradin ranta.

Daddynsu Khadeeja ne yayi gyaran murya yace "Nasan cewa zabin da aka yimaka batayi ba Hamma amma kada ka damu ni nasan mission da na dauka a kan Aisha nasan mezanyi mata dama tun Asali banason Yaya Kabeeru(mahaifin Aisha) da Yaya Ado saboda sun fini kudi a cikin 'yan uwana babu wanda ya kai yaya Ado (mahaifin Haidar) kudi shiyasa nakeson sai naga bayanshi gashi kuma wannan mukami da danshi Haidar ya samu a kamfani kai nake so ka samu saboda a cikin samaran gidan shine kawai ya girme ka,kaga idan mun kau da su sai ka samu matsayi a wannan kamfani ita kuwa Aisha sai mun wulak'anta ta mun gana mata Azaba domin banso ita zaka Aura ba naso ya kasance Yusra zaka Aura kanwar Haidar din kaga sai mu samu Ahalin baki daya ko ya kace?" Ya fada yana fuskantar Hamman.

"Daddy hakan ma yayi" Hamma ya fada yana me share hawaye saboda shima yana matukar son ace shine da mukamin Haidar din.

Khadeeja ce tace "kutumar ubancan,wato mijin nawa zaku kawar a doron k'asa?wallahi hakan bazai taba faruwa ba in dai ina raye, haba ya za'ayi a ce ina k'aunarshi kuma kuce zaku kawar min dashi?wallahi bazan yarda ba ai wannan zancen ma bata taso ba" ta fada babu Alamar tsoro saboda dama duk family nasu babu wanda take tsoro don an koya mata fitsara.

Daddy ne ya dubeta da kyau ya gane cewa lalle wannan yarinyar dagaske take babu wasa a lamarin ta sai ya kashewa Hamma ido yace "okay babu matsala shi baza'a kawar dashi ba amma insha Allah sai mun kawar da Alhaji Ado da kuma Yaya Kabeeru saboda sam bana son in gansu a doron k'asa duk sun girme ni kunga idan na dauke su a doron k'asa ni zan mallake wannan kamfani tamu na kuma zama ne fada a ji a wannan Ahalin.

"Yawwa dai sai a wani ce za'a kashe min masoyi" Khadeeja ta fada a tsiwace tare da barin dakin Amina ce ta bita don ita taga bata kanta ake ba ko rarrashinta an ki yi.

Daddy ne ya dubi Hamma da mommy yace "kada kuji maganar wancan banzan dole ne muga bayan Haidar idan muna so mu cimma manufarmu duba fa kiga Hajiya duk sunje makka matansu sunje harda wannan banzar Aisha wai a fadansu za'a nema mata lafiya amma daga ke sai ni kadai mukaje kasa me tsarki a cikin family na"

AISHAWhere stories live. Discover now