26

170 9 6
                                    

AISHA

Walidation S Mapi

26

Cikin mintuna kadan gida ya kaure Aisha ta dawo,kowa sai farinciki yake banda mommy dake daki ko sani ma batayi ba,Anti Amarya ce ta kira Lamido ta sanar dashi cewa Aisha ta dawo ba karamin farinciki yayi ba yasa a shirya mata abinci mai rai da lafiya,ai kuwa warce wayar tayi tace mishi a hada da kindirmo don bazata iya cin abinci kadai ba sai da shi cikin harshen fulani tayi maganar, hakan ba karamin burge Lamido yayi ba saboda iyayen yaran basu tashi da iya yaren fulani ba sai hausa shiyasa basu koyawa ya'yansu ba,murmushin dattako Lamido yayi tareda sake nuna farincikin dawowarta ya kashe wayar annuri cike taf a fuskarsa ya juyo ya dubi Amnah matarsa ya sanar da ita dawowar Aishar itama tayi farin sosai don duk batan Aishar baiyi musu dadi ba ta mike tayi ciki ta sanar aka fara shirye-shiryen abincin ya dauko ta tsattsen kindirmo me kyau daya aje a fridge nashi dama shima kullum sai yasha, tsiyayowa yayi ya rage nashi ya dauki nata a jug ya fita a gidan da niyyar zuwa gidan inna.

Yana zuwa ya same su a babban falon gidan kowa ya hallara sai taba Aisha suke saura nayi mata dariyar kauyancin da ta koya, tana ganin Lamido ta mike dagudu taje rungume shi shima rungume jikar tashi yayi yana hawayen farinciki raba jikinshi yayi da nata ya kalleta shima yayi dariyar dressing nata kana yace "jikata kin dawo lafiya ko?" da yake Aishar ba gane hausa take ba saita sake baki tana kallon shi.

Sai da ya fahimci haka ne yayi mata da fulatanci cikin farinciki ya bata kindirmo ba tare da an dama shi ba ta fara sha,suna cikin haka Khadeejah ta shigo falon ita da maleekah kowa sai kumburi yake daga gani basu yiwa juna magana ko sunyi fada,Aisha na ganinsu ta saki Lamido taje ta rungume su tareda fadin "i missh you bandirawo am".

Dariyarta sukayi saboda yadda ta furta kalmar i miss you din daga ji kasan ta dade bata furta ba,suma rungume ta sukayi suna hararar juna, dukda Khadeejah ba wani shiri take da Aisha ba amma tayi farincikin dawowarta sosai don hakoranta sun kasa komawa ciki.

Fatima da yaya Naseer ne suka shigo Maleeka tayi saurin dauke kai daga gare su saboda a duk lokacinda taga yaya Naseer ji take kamar taje ta rungume saboda a lokacin ne sabuwar soyayyar shi take dawo mata har tayi hawaye,suna shiga suka rungume Aishar harda yaya Naseer din ba tareda kowa ya kawo komai a ranshi ba,yayi matukar farincikin dawowar abokiyar wasar tashi shekara da shekaru ba'aga juna ba,Aisha ce ta ankare taga wata kyakkyawar yarinya a gefe dago yarinyar tayi ta rike a hannunta ai nan da nan ta sake ihu tana dauke kai bata son ganin Aishar, dariya kowa tayi savoda sun san taji tsoron ganin dressing din Aishar ne, Aisha ce ta budi baci cikin harshen fillanci ta tambayi yayya Naseer ko ya'r wacece? murmuashi yayi mata tareda sauke kai saboda duk kunya ce ta kama shi abinka da kunya irin ta fulanai Lamido ne yayiwa Aisha bayanin ya'r su ce duk bayan tafiyarta ya'n uwanta sun haihu Ameenah da Yusrah ma duk sun haihu Khadeejah da Maleekah be suka sa rigima a gabansu kullum fada da juna basa taba sanya Haidar cikin farinciki,Aisha ce ta dago kai da sauri jin an ambaci sunan yaya Haidar,kyalla ido ta farayi tana nemanshi saboda yawan su a cikin falon tana ganin baza'a rasa shi ba,rashin ganin shi yasa ta tambayi Lamido ko ina suke? dama can tun asali sun saba da Lamido tun tana gida itace jikarshi da yake sake mata fuska sai yaya Haidar da takwaranshi sannan Yusrah amma dukka sauran baya sake musu fuska don marasa ji ne,da haka yayi mata bayanin cewa yaya Haidar ya tafi wajen Aiki yanzu shi officer ne yana da mukamin babban soja, taya shi farinciki tayi ta zauna a gefen mamanshi taba yi mata murmushi duk kyanta ya bace.

Inna kuwa tunda Aisha ta dawo ta kasa magana sai sakin baki da tayi tanna waro ido kamar wacce ya'n daba suka shigowa gida, murmushi kuwa abin ba'a magana musamman ganin Aisha da tayi cikin dressing din fillanci sai ta fito kamar ita a da.

Aisha na zauna wa a gefen maman Haidar ta juyo ta kalle ta sai a lokacin maman Haidar din ta ji wani soyayyar Aishar ta kuma fara dana sanin kiyayyar data nunawa yarinyar a lokacinda aka ce ba ita ke auren danta ba, Naseer ne ya kyalla ido ko zaiga kyakkyawar Antin shi wacce a kull take shiga ranshi Anti Amarya kenan data wuce kicin tun dazu tana hadawa Aisha abinci saboda ji take tafi kowa jin dadin dawowarta da bai ganta ba ya kame baki saboda tasan vazata wuce tana kicin tana yiwa Aisha girki ba.

Você leu todos os capítulos publicados.

⏰ Última atualização: Jan 26, 2021 ⏰

Adicione esta história à sua Biblioteca e seja notificado quando novos capítulos chegarem!

AISHAOnde histórias criam vida. Descubra agora