20

95 14 3
                                    

AISHA

20

Na
Walidation S Mapi.

Aisha ko na jin ya fita ta ciro cimar data dawo dashi ta cinye tayi sallah ta kwanta bacci.

Washegari tunda safe ta mike don jiya tayi baccin farinciki,dakin Hamma taje ga mamakinta taga baya ciki,hakan ne ya bata damar shiga toilet tayi wanka ta fito daure da towel a kirjinta tana sharce ruwan kanta,jin an bude kofa yasa zuciyarta bugawa dimm,gani take kamar tata ta kare a yau,saurin mikewa tayi ta farabi ta jikin bangon tana neman hanyar da zata zille a dakin don a matukar kunyace take ga kayanta a dakin Babu damar sasu,duk ya wani bita da idanu kamar yayi ajiya a jikinta.

"Ni kada kar ka cinyemin kyauna" shine Abinda Aishar ta fada tana tuttura baki.

Dariya Hamma yayi harda rike ciki kafin yace "yo har wani kyan ne dake da zakice kada na cinye!,kema kinsan cewa ko zaben kyawawa kikaje bazaki zo koda ta karshe ba saboda kin Riga kin nakasa kanki".

"Kaga Yaya Hamma ka daina cemin na nakasa kaina Ai Allah ne yayi sanadin hakan Kuma kaddara tana iya fadawa kan kowa tayu ka rasa ranka ma gabadaya ba hannu ba".

"Da anyi magana zata fara yiwa mutane ririri kamar gidan rediyo,wallahi ki sake mayarmin magana kiga saina wanke ki da Mari".

Shiru Aisha tayi ta farabi wawwaro idanu don tasan ba Mari kadai ba har duka Hamma zai iya yimata.

Tana cikin tunanin taji Hamma yace"Ke zonan ban yadda dake ba ma"

Amsawa tayi da "kamar ya?baka yarda dani ba" a zuciyarta kuwa cewa tayi anya bai gane ta taba sabulun daya hanata Aiki dashi ba,hawaye ta fara zubarwa tace "Yaya Hamma don Allah kayi hakuri wallahi bazan sake tana sabulun ba,ni bama zansake wanka a dakinka ba please kada ka dakeni".

Yadda take maganar a tsorace Saida ya sashi dariya Amma ya make yace "ba kiranki nake ba Aisha?wato ke bakisan darajar Aure ba ko".

Wajenshi ta karasa a hankali kanta a sunkuye tana harde kafa,durkusawa tayi ta daga kai ta kalleshi wanda tunda ta fara tafiyar ya fara bintada kallo don ba karamin dauke hankalinshi tayi ba yarinya ga kyau ga gashi duk na bugawa a jarida Amma yawanta daya batada hannu daya, tsaki yayi a fili ya fincikota izuwa jikinshi Yana wani tabe baki shi a dole yaga abin kyama,hade bakinsu yayi waje daya da niyyar ramoncing dinta yaga tana mishi kuka tana magoya yareda raba jikinta da nashi,hakanda tayi ba karamin Bata ran Hamma yayi ba dalilin hakanne yasa ya mike ya rabata da towel dinda take ta wani kare jikinta dashi ya fara kusantarta Babu shiri a zafafe yake shigarta don haushinta yake ji sosai,saida ya tabbatar ya gama bukatarshi kafin ya barta yashige bangida yayi wanka ya fito,tararda ita a sume da yayi bai bashi mamaki ko tsoro ba don yasan shine aikinta dama yawan some-some.

Sallah ya tayar ya idar don jiya rufe gidan yayi ya nufi gidan joy suka kwana bai samu yayi sallah ba dukda cewa joy ta sashi yi yaki,tsabar tsananin sonda take yiwa Hamma ne yasa ta siya sallaya da buta na musamman ta ajiye duk lokacinda aka kira sallah takan bashi yayi.

Yana idarwa ya haye gadon yaja blanket dinda ke gefen Aisha yanata tunanin yadda yadda yadda jita jiya,daban take da matanda yake bi a waje dukda cewa ba wani romantic sex sukayi ba ya matukar gamsu da ita sai dai bai ga jini ko kadan ba,tunawa da yayi da hakan ne yasa shi tashiwa daga kwanciyarda yayi ya zabga tagumi,zuciyarshi kuwa ta fada mishi lalle-lalle Aisha ba budurwa bace tunda baiga jini ba kuma yasan Aisha bata Kai shekarunda za'ace ba'ag jini ba saurin fincikota yayi a sumen yana jijjigata yace "ina kika kai budurcin Aisha?wa wani katon kika baiwa?Aisha kin cuceni a rayuwa,ga rashin hannu ga rashin budurci kinje kin siyarwa wasu a waje,to wallahi ki tashi ki barmin gida bazan iya zama da karuwa ba maciyiya Amana ki tashi ki tafi na sakeki saki uku" Yana fadin haka Aisha ta farka taji kalmarshi ta karshe cewa ya saketa saki uku,hakan ne yasata fashewa da kuka ta mike dakyar tayi toilet ta zuba ruwan zafi ta gasa jikinta kana tayi wankan tsarki tayi wanka ta fito ta sameshi a dakin yanata hawaye kona menene oho,karasawa bakin mirror tayi ta shafaa mai a jikinta ta dan gyara fuskarta ta karasa bakin gadon ta zauna "don me yasa ka sakeni Yaya Hamma?".
"Au tambaya ta kike? Aisha ina kika kai budurcinki?Ashe dama ke munafuka ce?babu wanda bai shaide ki da hankali ba Ashe ke fasika ce me fuska biyu".

Mamaki ne duk ya cika Aisha,wai itace karuwa? "Haba malam kamar ya zaka tisani a gaba kana wani zagina karuwa,menayi na karuwanci? kai din ba mijina bane?".

Cikin tsawa Hamma yace"Ke dalla yiwa mutane shiru fitsararriyar banza saiki nuna min inda kika fitarda jini munafuka kawai".

Aisha da kuka yaci karfinta ne ta budi baki a hankali tace"shine illar Auren jahili ko kuma me ilimin da baya aiki dashi kenan, Inna kin cuceni kin cuceni".

"Aisha me kike nufi?nine jahilin? kinaso kice bani aka cuta ba ke aka cuta? what hell on Earth? Aisha bazan taba yafe miki ba, ki shirya barin gidan nan a yau zaki koma Yola don ubanki shegiya miskiniya".

Dagudu tabar dakin don bazata iya sauraron irin cin mutuncin da Hamma ke mata ba,tana shiga dakinta tasa sakata ta kwanta a kasa ta fara rero kuka da salati,daga hannu sama tayi tace "ya ubangiji kaine mamallakin komai,kaine mahillicin sammai kassai babu me wata iko sai kai,ya ubangiji ka cireni a cikin wannan ukuba dana shiga",tana cikin haka taji Hamma na kwankwasa kofa yanata surutai yana tsine mata tareda la'antarta, kwarin gwuiwar magana ta samu yasa tace "ya isa haka tunda ka sakeni,kuma bazan tafi ba don bansan me zan fadawa su Abbana ba,sai dai muje tare kayi musu bayani".

"Ki fito kafin na balla kofar na Bata miki Rai".

Bude baki tayi a hankali tace "koba rai ba?".

Tsaki yayi don yaga tana Bata mishi lokaci,saurin barin kofar dakin yayi, ya wuce falo ya zauna.

Haka Aisha ta wuni a daki ita kadai tana ta kuka kamar ranta zai fita,can wajen Isha yunwa ya fara koya mata hankali,tunawa tayi da ragowar cimarta data dawo dashi jiya ta mike ta cinye ta kwanta bacci.

Can wajen sha daya na dare Aisha na daki tana kuka saboda ta lura Hamma so yake yaci zarafinta,Bata Ankara ba sai ji tayi an yarda kofarta dama ba wani kyau ne da kofar ba saurin mikewa tayi dama daga ita sai hijabi babu komai a jikinta.

"Please Yaya don't do something crazy, please".

Kafin ta sake magana ya janyota jikinshi ya hade bakinsu waje daya ya fara romancing dinta a hankali,da iya karfinta ta tureshi "bakada hankali ne?to inma bakada shi ni inada shi,ya za'ayi ka sakeni kuma ka sake tabani".

Kan ta sake magana ya kwarfeta ta fadi kasa ya sake kusantarta na karfi da yaji nan ma baiga jini ba,hakan yasa ya fincikata izuwa waje ya kara cillo mata akwatinta waje shima ya biyota yaja hannunta ya kaita motar yasa kayanta a boot ya ja suka bar gidan ko rufe get baiyi ba.

Lungu-lungu ya nema ya wurga Aisha a tareda amwatinta wanda yayi dai-dai da buguwar kanta a jikin wani katon dutse dake gefenta,ko gezau Hamma baiyi ba saima dagata da yayi kadan ya ajiye mata kudi da paper karami ya juya ya tafi don ba karamin hadari aka hada ba gashi Aishar kuma ta suma,mota yashiga yaja yabar wajen Aisha na nan a kwance ko numfashi batayi.

AISHAWhere stories live. Discover now