14

78 18 0
                                    

AISHA

Walidation S Mapi

14

_________Ta fasa ihu ta fadi ta suma a motar.

Koda suka ga ta suma suka bude mata baki sukayi hanyar gidansu dake nassarawa phaste one suka jefa ta kan gado suka kuma fita wasu sabgoginsu na dare.

Inna ce zaune ta kara minti goma babu Hamma ba labari,saurin mikewa tayi ta shiga daki ta fito da akwati tace ko Daddy ya kaita katsina taga takwararta ko ta tsine mishi albarka.

Ran daddy ne ya tsinke saboda yasan babu yadda mutum zai cigaba sai da Albarkar iyayensa sai kuma yace "Inna me yayi zafi kuma shi ba wuta ba?don Allah Inna kiyi hakuri mu kara musu lokaci kinsan fa yaran nan sai an rika yi musu uzuri dududu yaushe akayi Auren nan Inna in banyi karya ba yau fa wata biyar ne".

"In tambaye ka mana dannan".

"Inna ina jinki,Amma don Allah ki sassauta kalamanki".

"Yanzu wa muka kira a waya?".

"Inna Hamma mana dana".

"Kace danka ko?".

"Eh Inna dana ne mana".

"Yanzu bakaji dadi ba da kaji muryar danka?".

"Inna ai dole mutum yaji farinciki da annashuwa idan yaji muryar dansa".

"Na nasha uwarka,nace na nashe uwarka munafiki duba kaga bayin Allahn nan" ta nuna su umman Aisha data sauke kai tana kuka a boye.

"Yau wajen wata biyar kenan basu ga Ya'r su ba kuma basu ji muryarta ba ya kake tunanin zasu shiga farinciki da annashuwar da kace ko wani iyaye dole ne yaji farinciki idan yaji muryar dansa?".

"Bakada tausayi ne?".

"Inna don Allah ki sassauta kalamanki a kanshi,insha Allah Aisharki na nan cikin kwanciyan hankali ai kinsan dan uwanta bazai wulak'anta ta ba".

Sauke kai Inna tayi daboda tana matuk'ar jin kunyan mahaifin Haidar danta na fari domin a al'adar fulanai dole ne mutum ya rika jin kunyar danshi na fari.

Hakuri kowa ya shiga baiwa Inna saboda dukkaninsu basa son ganin bacin ran Inna duk yadda take bata musu rai a koda yaushe tana kara shiga ransu.

Daddy ne ya sauke kai ya shiga bawa Inna hakuri yana hawayen karya tace ita bata son munafurci kowa ma ya bata waje, sumi-sumi suka shiga barin falon kamar wadanda kwai ya fashe wa a ciki.

*************
Ihu yake a motar saboda ya rasa yadda zaiyi duk inda zai shiga neman Aisha sai da ya je Amma babu Aisha babu labarinta babu kuma wanda yace ya ganta mutanen da akaje Asibiti dasu ma ba ya'n unguwar bane kawai sun bi su Mubin ne don kada su sace Aisha Amma wannan shine sahunsu na biyu cikin unguwar.

Joy ne ta bude motar ta shigo tare da rike hannunshi tace "Reekado lafiya kuwa?".

Fizge hannunshi yayi daga nata yace "duk ba kece sila ba ke kika sa nayi baccin da banyi niyya jaka kawai mara tunani".

Juyowa tayi ta dube shi tare da rashin fahimtar Abinda yake nufi tace "haba Reekado meke faruwa?".

"Ubanki ne yake faruwa nace ubanki ne yake faruwa banza dakikiya".

"Reekado please tell me what's happen with you may be I can solve your problem".

"Wannan fitsararriyar yarinyar ce ta gudu".

"Which naughty girl?".

"My wife Aisha".

"What! matarka fa kace?dama kanada Aure ne?".

"Look Joy yanzu ba lokacin wannan zancen bane ya kamata ki kawo min solution ba wai ki tsaya wani tambaya ta ba".

"You make me surprise that's why I ask walayi (wallahi) Amma are you sure kanada Aure".

"Of course that girl was not my house girl but my wife".

"Amma Reekado kai mugu ne walayi,dama a gaban matarka ka kawo ni don kawai kaci fuskarta baka kyauta ba walayi bakada tausayi".

Wasu zafafan mari biyu ya sauke mata a kuncinta yace "ke har kin isa kice wai banida tausayi kifa shiga hankalinki ko in bata miki rai wallahi jaka kawai ya'r bariki".

"Ya'n bariki dai zaka ce ba ya'r bariki ba,ko kai din ba barikancin kake ba?".

"Dalla madam in bakida solution ki fice min a mota kiyi hanya".

"Can you emergin mace zata iya fita cikin daren nan".

"To haka matata take yawo cikin daren babu wanda zai dubamin ita don haka bazan duba karuwa ba get out!".

Tana fita tayi ciki don batada niyyar tafiya don bazata iya tafiya cikin daren ba.

Hamma ne ya buga sitiyarin mota ya kurma ihu kamar karamin yaro, sai hawaye da yake ta zubawa kamar karamin yaro.

_Sadaukarwa ga dukkanin nakasassu,ina me farincikin sanar daku cewa nakasa ba kasawa bace_

AISHAWhere stories live. Discover now