16

186 19 2
                                    

AISHA

Walidation S Mapi

16

__________Ya zare igiyar cajinsa ya shiga zane ta babu kakkautawa.

Ihu ta shiga yi tare mikewa cikin sauri ta fara bashi hakuri.

"Ba hakuri zaki bani ba don ubanki wato ina cikin tashin hankali babu Abinda ya dame ki ko?".

"Reekado why do you change?".

"Na canja uwarki Joy kinji ko na canza uwarki,zaki mike mu tafi nemanta ne ko kuwa!".

Mikewa tayi tare da kunkuni can k'asa-k'asa.

"Sai dai kiyi kunkuni Amma wallahi kina daga min murya a nan sai naci bantan ubanki mara kunya kawai".

Dai-dai zata shiga toilet tace "nidai kada ka juye fushi a kaina sannan kuma maganar ka akwai gyara a ciki marasa kunya zakace ba mara kunya ba".

Nufo hanyar toilet din yayi dagudu da zummar zai dake ta ita kuwa saurin shigewa tayi tare cewa "nifa bazan fasa fada maka gaskiya ba saboda kasan i no dey lie".

"Zaki fito ki same ni shegiya cingam kawai ana korarki kina sake manneewa jikin mutum".

"Nasan kanayin duk wannan ne ka kore ni, to bara kaji in fada maka babu inda zani wallahi iya wuya muna jone".

"Ai in dai nine sai kin raina kanki maza ki fito mu tafi police station ko sun samu wasu bayanan".

"Bazan fita ba idan har wannan socket na hannunka wallahi sai dai kaje kai kadai Amma banda Joy".

Wurgar da igiyar yayi a gefe da karfi yadda zata iya sauraro yace "oya come let's go".

Bude toilet din tayi a hankali taga tabbas ya aje yasa ta fito suka fice ya rufe gidan suka nufi ofishin ya'n sanda.

************
Khadeeja ce zaune a babban falon dake sashensu tana kallo tana shan juice dauke da snack cikin roba daya tana ci,Haidar ne ya shigo dakin Maleeka na biye dashi a baya ko kallonsu Khadeeja batayi ba don bata ganin kowa da gashi a gidan gwara Haidar ma da yake dan taka mata birki.

"Mutum kullum sai ci ba dole ya rika zama lukuti ba yanzu da za'a auna ki wallahi sai kinfi nauyin buhun masara" Maleeka ce ta fadi maganar a sigar wasa.

"To da na rika zama ramammiya kamar muciyar sakace ai gwara na rika cin kinga riba biyu kenan ga jiki ga dadi ballagaza kawai".

"Kul kada ki sake cemin ballagaza ai kowa yasan yaran mummy ne ballagazazzu a family dinmu jaka kawai".

Khadeeja ce ta harzuka tace "Ke dalla yiwa mutane shiru dube ki fa kamar tsintsiyar laushi sam bakida auki a nan da zan gwada lankwasa ki wallahi cikin minti biyu zaki lankwasasu".

Maleeka duk bacin ran duniyar nan sai da ya taru cikin zuciyarta ta mike a hankali ta karasa wajen Khadeeja ta rike kwankwaso tace "ke malama ba jiki bane fa karfi ya kamata kisani".

"Ke is better for you to leave don wallahi idan na rike ki baza kiji dadi don banida kyau".

"Dama ina kike da kyau a fili ma bare a zuciya".

Khadeeja ce ta mike ta juya kamar batada shirin yin komai sai kuma ta juyo cikin sauri ta daga Maleeka sama ta kaita kasa ta hau ruwan cikin ta tace "kinje kilo na?nace kinji kilo na?".

Ihu Maleeka ta shiga yi tana rokon Yaya Haidar yazo ya taimake ta Amma kota kansu baibi ba sai ma sake maida hankalinshi da yayi kan na'ura me kwakwalwa (laptop) yaci gaba da ayyukan dake kanshi.

Suna cikin haka sai ga Sadeeq (abokin Haidar) ya shigo gidan da gudu ya karasa wajen tare da tsayawa a gefe dasu yana basu hakuri, sai a lokacin ya lura da Haidar dake ta latse-latse wannan kyawawan idanun nashi sanye da farin gilashi irin na ma'aikatan lafiya,karasawa wajen yayi ya rufe laptop din ya shiga yi mishi masifa "haba Haidar ya kana zaune matanka na gefe suna fada kuma bazaka rabasu ba?".

"Kaga Sadeeq barsu jini ne yayi musu yawa".

"Kamar ya zaka ce haka fadan ne har wani jini ne yayi musu yawa? dalla ka tashi kaje ka raba matanka".

Haidar ne ya mike tare da rike hannun Sadeeq ya ja shi zuwa dakin karatu suka fara Aikin da ya zo da Sadeeq din shi Sadeeq Aiki yake tare da tunanin hali irin na Haidar sam baya shiga harkar mutum gashi yana daukar rayuwa so simple.

**************
Dayan ne ya shiga salati tare da cewa "ku kuke ganin mu bamu ke ganinku ba,ranki shi Dade don Allah kada ki kashe mu wallahi mu marayun Allah ne bamuda kowa a rayuwarmu".

Aisha ce ta waro hanci tace "kai yiwa mutane shiru,kuma ina jiyo kamshin mutane a gidan nan koda wasu kuke ne?".

"A'a mune kadai muka zo".

Aisha ce ta mike tare da waro ido tace "mu zaka rainawa wayo to yau zamu kasheka idan baka fada mana inda muke jiyo kamshin bil'adama ba".

"A rikice dayan ya nuna mata inda sauran ya'mmatan suke yafe can ne wallahi ranki shi dade".

Aisha ce ta wuce dakin taga a rufe yake yadda ta barshi sai kuma tace dayan ya zo ya bude mata,babu bata lokaci daya daga cikinsu yazo da gudu ya bude mata ta shiga tare da rufe kofar tana dariyar mugunta.

_Har ila yau sadaukarwa ne ga dukkanin nakasassu ina me farincikin sanar daku cewa nakasa bakasawa bace_

AISHADonde viven las historias. Descúbrelo ahora