22

111 16 0
                                    

AISHA

Walidation S Mapi

22

Dariya Aisha tayi saboda ta lura Lateefa na son wasa da tsokana da haka suka saba a yau kadai Kai kace sun taba haduwa,can da dare bayan sun idar da sallah sun ci Abinci Fu'ad ya dawo gidan dauke da leda a hannunsa,Lateefa ce ta mike da sauri ta karbi ledar ta aje kan taburma Aisha kuwa bude baki tayi a hankali tace "sannu da dawowa Yaya Fu'ad".

"Yawwa sannu bakuwa" ya amsa dashi.

Lateefa ce tayi saurin cewa "Yaya Fu'ad sunanta Aisha ka daina ce mata bakuwa ai yanzu gani nayi ta zama ya'r gida ko".

"Hakane,Humaira ce kenan".

"Eh wallahi Yaya saika ganta kyakkyawa kamar ka sace ni cewa ma nayi ko ita tuarek ce ashe bafulatana ce".

"Ayya masha Allah dauko ledar nan ki bude".

Ammi ce ta dubi dan nata cikin mamaki tace "Babana yau kaine ka dawo da wuri haka?".

"Ehh Ammi na ai nasan inada bakuwa dukda inada tabbacin zaku kulamin da ita yadda nakeso".

"Hakane Babana bakuwar taka batada mako,hira muke kamar munsan juna".

"Ai Ammi haka akeson mutum ya kasance ba wani dum-dum-dum haka ba".

Sai a nan Aisha tayi dariyar maganar tasa yadda yadda maida murya kamar wani gardi,suma dariya sukayi gabadaya don yadda Fu'ad din yayi maganar abin dariya ne,Lateefa ce ta bude ledar cikin zumudi ba komai bane a ciki,toci ne da kwallon kankana guda daya sai kuma balangu a dayar ledar murmushi tayi don tana matukar son cin dadi,saurin  mikewa tayi ta dauko wuka ta yanka kankanar ta sawa kowa nashi a kan faranti ta kuma bude balangu ta baiwa kowa nashi,Aisha ce ta dauki kankanar ta fara sha a hankali tana kunyarsu saboda yanzu an kunna tocin ana iya ganin komai Fu'ad ne ya lura da yadda take kunyarsu hakan yasa ya mike yayi nashi dakin ya barsu su kadai,a sannan ne ta cire kunya tasha kankanarta yadda take so ta kuma ci tsiren ta bar saura,Ammi ce ta dubi yadda take nishi kadan-kadan Alamar koshi,dariya tayi tace "Humaira masu kananan ciki,wai yanzu har kin koshi da wannan abin?".

"Eh Ammi na bakiga yadda ya cika min ciki ba".

Lateefa tace "kinga Ammi su masu kudi dama haka suke da wannan halin sai kiga sunci Abu kadan wai ya ishe su".

"Tooo,haka akace Miki" inji Aisha dake kokarin mikewa don motsa jikinta.

Ammi tace "Ai gashi mun gani",dariya sukayi a tare Aisha ta fice tayi ta tsalle-tsallenta harta  ware,sai a sannan taji dadi,Lateefa kuwa debe sauran Abinda Aishar tayi ta cinye tas,wanke hannu sukayi Fu'ad ya shigo suka dan taba hira kowa ya kwanta abinshi.

**********
Karfe bakwai na safe Inna ce a daki tana ta safa da marwa tareda sake-sake a ranta,tabbas tana cikin damuwar rashin ganin mesunanta gashi kowa yaki jin maganarta, Hamma ba samunshi ake a waya ba,Alhaji Kabeeru ne ya shigo dakin shima tunanin yake ya rasa me zaiyi kwata-kwata duniya ta daina mishi dadi, samun waje yayi ya zauna ya dubi mahaifiyar tashi cikin damuwa yace "Inna ya kamata ki dauki dangana ki fawwalawa Allah komai insha Allah takwararki na cikin koshin lafiya,muma nan da kika gani ba karamin tashin hankali muke ciki ba".

"Kabeeru na rasa yadda zan bullowa Al'amarin nan,anya ba saida yarinyar nan akayi ba?".

"Haba Inna ki daina munana zatonki a kan yaran nan insha Allah za'a samu saukin Al'amarin".

"To shikenan Allah yasa shirun Alkhairi ne a garemu baki daya".

"Ameen Inna Allah ya jikan magabata".

"Ameen".

Bangaren Haidar kuwa samu cigaba a kamfaninsu sanadiyyar wani kwangila da aka basu kuma sun cimma burikansu a kan kwangilar Amma har yanzu bai fasa neman aikin soja ba saboda soja shine ambition dinshi tun yana yaro.

AISHAWhere stories live. Discover now