AISHA
Walidation S Mapi
12
________Bai bi ta kanta ba ya tsallake ta ya fice a dakin yana dariya.
*********
Inna ce tsaye a falo ta tusa Akwatinta a gabanta tana ta ruwan masifa wai yau ita saita tafi katsina koda kafa ne,yaran gidan ne suke tayi mata dariya sauran harda faduwa kasa suna rike ciki,musamman ma Khaleel da ya saba dariyar mugunta,harara Inna ta sauke mishi kana tace "wallahi kalilu Anyi jikan banza yanzu ace ni ina uwar ubanka kake tayi min dariya harda rike ciki,naci kutumar ubanka in baka bar falon nan ba" Inna ce take ta yiwa Khaleel masifa saboda yau acike take fashewa ne kawai ya saura."Ke tsohuwa ki shiga tai-tayinki don kin ganni gaye dani santali shikenan saiki wani juye min fushi a kaina" Khaleel ne yake fadan haka cikin sigar wasa saboda sun saba ya'r haka da inna.
Daga sanda Inna tayi tace "na mauje ka shegun yara fitsararru,babu Abinda kuka sani sai raina na gaba daku".
Ma'ida ce tace "haba innarmu meyasa laifin wani zai shafi na wani?yanzu fa Khaleel ne yayi miki laifi Amma kin hadamu kina zaginmu".
Inna ta dauki sanda ta buga a bayan Ma'ida tace "kinci ubanki da manyancen nan,ni zaki yiwa wa'azi".
Da kuka Ma'ida tabar falon tare da cewa "nidai gaskiya ce saina fade ta koda kuwa kashe ni za'a yi".
Inna ce ta yar da sandarta ta kurma ihu tace "nashiga uku na lalace shikenan ni Indo naga ta kaina,manyan ba jin magana ta suke ba haka yaran ma,yanzu don ubanki Ma'ida nice zan kashe ki? wayyo na mutu na lalace".
Sauran yaran ne suka tsaya ganin abin mamaki tun suna dariya har suka daina ga babba da kukan yara.
Mikewa tayi kamar bazatayi wani Abu ba ta dauki sandarta tabi jikokin nata dagudu tana ta kurma zagi.
Karo sukayi da Gwaggo Rabi (maman Maleeka) tsayawa Inna tayi tace "An dake ta me kuma kika zo yi? ko rama mata zakiyi?".
"Haba Inna ya kamata ki daina Abinda kike yiwa yaran nan ya isa haka".
"Au wa'azi kika zo yimin? aji nawa kika tsaya a islamiyya? Badawiyya (sunanda take kiran maman Maleeka dashi kenan) yaushe kika girma ne wai? yaushe har Lami ta haife ki?".
"Inna don Allah kada ki dauke ni a bai-bai wallahi bahaka nake nufi ba don Allah kiyi hakuri" tana gama fada ta juya ta nufi part nata.
Koda tabar wajen,Inna ta koma ta dauki Akwatinta dakyar saboda ita ba irin ragwagen tsofin nan bane,hanyar waje ta nema ta faki idon kowa dama akwai dari biyu da Ashirin a wajenta shi zatayi Amfani dashi ta tafi katsina.
Tana fita me gadi ya tare ta tareda fadin "Inna ina zaki?".
"Laminu ina son nayi maka tambaya daya".
"To Inna In jinki".
"Laminu menene Aikinka a gidan nan?".
"Inna gadi ne Aiki na".
"Gadi da kuma bincike ko?" Inna ta fada a takaice.
"A'a Inna gadi kawai".
"To kayi gaggawar bani waje in wuce kan ranka ya baci".
Matsa mata yayi ya bata wuri saboda ya lura yau ran Inna a bace yake don bata taba mishi magana haka ba.
Fita tayi ta fara tafiya batasan ina ne tasha ba kawai dai tafiya take dama Akwatin bai wuci kaya kala uku bane ba wani nauyi ne dashi ba kawai dai dole zai yiwa tsofi nauyi.
Umman Aisha ce keta tunani a daki can sai zuciyarta ta bata shawarar taje ta nemi Inna tasa dole a kira Hamma aji labarin yaya Aisha take saboda shirun yayi yawa,mikewa tayi cikin Azama ta nufi part na inna.
Abin mamaki yau Inna bata saki wakar fulani ba part din shiru kamar bata ciki,haka dai umman Aisha ta karasa ciki tayi ta rafka sallama ba'a Amsa ba hakan ne yasa ta kutsa kai cikin wadataccen falon Inna me kyau da tsari kamar dakin Amarya,nan ma tayi ta sallama babu amshi,hakan yasa ta shiga inner room na Inna shima ba kowa aciki, sai ma ankarewa da tayi babu Akwati.
Hankalinta ne ya tashi ta fita neman Inna cikin gidan,Amma inaa sama da kasa babu Inna ba labari wata zuciyarce ta bata shawarar fadawa sauran matan gidan,haka kuwa akayi ta sanarwa kowa da kowa,har kuka wasu daga cikinsu sun fara musamma Anti Amarya da tunda Aisha ta tafi hankalinta ya gushe sam batason zaman cikin mutane, Idan ana yi mata magana sai tace na'am Aisha sai an ankarar da ita take shiga hankalinta,momyn Khadeeja kuwa hamdala tayi tace koma huta da jaraba na kwana biyu.
Sun gaji da nemanta ne yasa aka sanarwa iyayensu maza saboda wannan ba karamin lamari bane.
Hankalinsu ne ya matuk'ar tashi harda daddy saboda yana matukar son mahaifiyarshi kawai dai ya'n uwan ne baya so.
Dawowa sukayi suma akabar karamin kaninsu kan kamfani don yau Haidar baya gari yaje kai Appointment nashi yana neman Aikin soja, saboda wannan shine burinshi tun yana karami.
Iyayensu maza na dawowa suka baza neman Inna cikin gari don hankalinsu ya matuk'ar tashi bana wasa ba, basu taba kawowa kansu cewa Inna zata yanke wannan mummunar hukuncin ba.
أنت تقرأ
AISHA
أدب تاريخيlabarine a kan wata yarinya mara hannu daya wacce take kaunar dan uwanta Amma shi baya sonta ko kadan.