AISHA
Walidation S Mapi
6
~Ihu mutane suka saka kana sukayi kan Aishar da gudu.
Anti Amarya dake gefe tana hawaye ne ta kasa tabuka komai ta rasa me yake mata dadi,ko wajen Aishar ta kasa daga kafa taje.
Umma da sauran 'yan 'yan uwa ne suka ciccibi Aishar sukayi daki da ita aka shaka mata maganinta.
"Tambayarka nake yayan gida gaskiya wannan yarinya take fada ko kuwa?".
Sauke kai kasa Hamma wuro yayi Alamar Akwai gaskiya cikin maganar Nabeela Amma harga Allah ba shine ya lalata ba don a lalace ya same ta.
"Mommy sorry please bazan sake ba dama wannan din....."
Kamin ya sake wata magana mutane suka ga mommyn su Khadeeja a kasa sumammiya.
Ihu kowa ya saki akayi kanta itama Hamma ne ya shiga gagarumar tashin hankali yayi kan momyn nashi da taimakon wasu mata biyu ya daga ta suka kaita mota sai Asibiti.
Nabeela kuwa cewa tayi momyn taje Asibiti tayi sauki zata dawo nan da kwana biyu.
Can da azahar su Khadeeja suna wani kebebben daki da kawayensu inda suka cakude harda kawayen Amina saboda duk sun san juna gaba daya,kuma yaran manya ne kawayen nasu,nan sukaji labarin Abinda ya faru,da gudu sukayi part na momyn nasu kana suka nemi daya daga cikin kawayensu me mota sukace ta kaisu Asibitin da aka kwantar da momynsu,ba bata lokaci kuwa ta kwashe su harda 'yan kinibibi wanda ma ko Auren ba'a gayyato su ba.
★★★
Da kakkarwa Aisha ta fara farfadowa Abinda ya bawa kowa mamaki kenan domin bata taba farkawa da kakkarwa ba,Anti Amarya ce tayi kanta da gudu ta zauna bakin gadon ta rike hannunta daya tace "sannu Aisha,yaya jikin?"Bude idanu tayi a hankali ta dubi Anti Amarya ta daga mata kai Alamar babu komai tana hawaye.
Hankalin kowa na dakin ne ya kwanta inda saura daga cikinsu sukayi Ajiyar zuciya,suka bar dakin don dama akwai masu shirin tafiya gida yau din.
Shiru dakin umman Aisha ya zauna saboda karancin mutane,kowa na sake-saken Abinda ya faru a zuciyarshi tare da tausayawa Aisha halinda zata tsinci kanta a ciki inta je gidan Hamma.
Can saura suka samu suka bar dakin ya saura daga Anti Amarya,sai Umman Aisha,da kuma wata 'yar uwarsu uwa daya uba daya ita ba'a family din tayi Aure ba a gidan Lamido take,bude baki Aisha tayi a hankali tace "Umma ni kenan mazinaci zan Aura?"
Da tausayawa Umman Aisha tace "ke waya fada miki shi mazinaci ne?bakida hankali ne?baki tantance me ke faruwa ba kin tsaya yiwa mutum mummunar fahimta!gaskiya banson haka Aisha na".
"Haba Anti ya zaki boye bayan kinsan mazinacin take Aura" Baaba Shafa ce ta fada rai a bace.
"Hakane Amma ai bai kamata a fada mata mazinaci take Aura ba Shafa,ai sai ranta ya Kara tsinkewa" Umman Aisha ce ta fada tana maida kallonta zuwa kan Aishar.
Aisha kuwa juya kanta tayi ta na me kallon gefe tana fitarda zazzafar hawaye.
Anti Amarya ce tace "Aisha hakika Hamma ya Aikata Abinda kike tunani Amma kika sani ko ya gyara halayensa?Hamma fa Dan uwanki ne kuma bazai cutar da ke ba ya kamata kisan da wannan".
Da tausasan kalamai Anti Amarya da umman Aisha suka samu suka dan kwantar mata da hankali har ta samu ta kwanta bacci,Baaba Shafa kuwa duk bakincikin wannan Auren ne ya isheta,da ba dan Hamma wuro dan uwanta ne na jini ba da wallahi yau sai ta raba Auren.
★★★
Can wajen karfe biyar na yamma Aisha ta farka daga baccin da take har yau tana fashin sallah kawai sai ta mike ta nufi toilet tayi wanka Abinta duk Ummanta na kallonta,ko magana batayi mata ba tana ta tausayawa 'yar tata.
YOU ARE READING
AISHA
Historical Fictionlabarine a kan wata yarinya mara hannu daya wacce take kaunar dan uwanta Amma shi baya sonta ko kadan.