Chapter 1

472 27 7
                                    

AISHA

Na
Walidation S Mapi

1

This book was written under Zamani writers association.

GABATARWA
Dukkan yabo su tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda ya halicci sammai da kassai ya kuma yi rana da wata,wanda saida izininsa muke aikata komai,dalilin haka yasa ya bani damar rubutu muku wanna littafi nawa,Allah ya bamu ikon gamawa lafiya,wannan labari kirkirarre ne,kuma banyi shi don cin zarafin wata ko wani ba,idan kaga yayi kama da labarinka ko naki,sai ayimin uzuri tunda dan Adam ajizi ne.

~Zaune yake kan kujera me wajen zaman mutum uku laptop ce a gabanshi yana latsawa fuskarshi sanye take da farar gilashi kayan jikinshi kuwa farar jallabiya ce ta zaman gida dago cup dake gefenshi yayi yasha coffee dake ciki kana yaci gaba da duba laptop din.

Da sallama ta shigo dakin nashi kana ta samu waje a gefen kujera me zaman mutum ukun ta zauna ba tareda tayi magana ba.

Da yake yasan muryarta ne yasa yaki juyowa don ba wani abin kirki bane yake kawota wajenshi illah iyaka maganar soyayya.

Wajen minti biyar kenan tana zaune a wajen amma ko kallonta baiyi ba hakan yasa tace "haba yaya Aliyu kada tsanar ta kai haka mana, wallahi ni ba makiyiyarka ba ce ya kamata kayi min uzuri domin kaf cikin zuri'ar mu babu me k'aunarka kamar ni wallahi yaya Ina sonka har cikin zuciyata tun ina boyewa har na yanke shawarar sanar da kai amma tun daga lokacin ka tsane ni,ka tsani mu'amala dani ko me dalilin hakan? Kodan ya kasance banida da hannu ne?" Ta karasa maganar tana me zubarda hawaye

"Wannan shine Abinda ya kawo ki dakina?"

Daga mishi kai tayi alamar eh kana ta sauke kanta k'asa saboda bata iya hada idanu dashi.

"Okay tashi ki fita! Ki tashi ki fita nace" cikin tsawa yake maganar wanda hakan yayi silar tashiwarta cikin sauri tana hawaye ta bar part nashi.

Tana fita ya rufe laptop din ya kwanta a kushin din ya fara kawo tunani kala-kala kwakwalwarshi.

Bayan tabar part nashi babu inda ta nufa sai part na Anti Amarya inda ta tarar da ita tana ta girki a kitchen nata sai kamshi yake tashi kowa na son ranar girkin unty Amarya saboda akwai son kamshi,shiga cikin kitchen din tayi ta karasa wajen unty ta rungume ta da hannu daya tana hawaye.

Ko bata tambaya ba tasan meyi mata haka,juyowa tayi tace "haba Aisha ya kamata ki rika tausayawa zuciyarki,nasan cewa kina son Haidar amma kisani baya sonki ya kamata ki cire shi daga zuciyarki gabadaya tunda zuri'armu ba'a Auren bare saiki daure ki jira kiga zabin da Lamido zaiyi miki in yaso sai ki so shi ko kuma ki kulla Alaka da wani daga cikin 'yan uwanmu kuyi Aurenku inba haka ba Haidar yaki sonki kuma bai nuna zai so ki ba kiyi hakuri kinji Aisha na"

Daga kai tayi tace "Anti kodan banida hannu daya yasa haka"

Saurin sauke kai Anti Amarya tayi kafin tace "Ke Aisha ban hanaki irin wannan maganar ba?bakijin magana ta ko?"

Sauke kai kasa tayi don bata fiye kallon idanun mutum ba tace "sorry anty bazan sake ba"

"Idan Kika sake sai nayi fushi dake zo muje daki kafin wannan shinkafar ta dahu"

Suna shiga daki ta zaunar da ita a bakin gado ta fara bata labarin wani littafi a take ta mance da me Ke damunta saboda tana matukar nishadantuwa da labarin sai dariya take kamar cikinta zai fashe.

Mikewa anti Amarya tayi ta nufi kicin biyota Aisha tayi tace "Nima bara naje na koyo girkin da zan rika yiwa Haidar nawa" ta karishe maganar tana dariyar kanta

Anti Amarya na jinta taci gaba da tafiya tare da tausayin Aishan a cikin zuciyarta.

Suna zuwa kuwa girkin ya shanye ruwa sauke wa Anti Amarya tayi kana Aisha tayi saurin dauko flask guda daya saboda hannunta bazai iya dauka duka biyu ba don batada hannu daya Anti Amarya ce ta dauko sauran ta kwashe Abincin gabadaya ta sanya su cikin flask din ta rufe suka nufi dinning suka jera shi gaba daya.

A waya aka kira kowa yazo inda Aisha ta hana Anti Amarya kiran Haidar wai sam ita zata kirashi,haka ta kyale ta.

Saurin hayewa part din nashi tayi ta kwankwasa tayi sallama ta shige.

A kwance ta same shi kanshi na kallon silin yana bacci tsayawa tayi ta kare mishi kallo kana tayi murmushi tace "Allah mallaka min kai yaya Aliyu"

Tashin shi tayi a hankali ya Mike Yana fuskantarta kana ya daure yace"lafiya kuwa malama nifa kin ishe ni"

Inda-inda ta fara kana tace "dama dinner is ready shine aka ce na kira ka"

"Dinner is ready?tsabar munafurci dai kawai amma ai kiran mutum ake waya"

"Dama wayar ce taki shiga yaya Aliyu shiyasa"

Kallonta yayi yaga yadda ta tsure yasa yace "jeki gani nan zuwa"

Fita tayi cikin farinciki tare da Aniyar daga yau ita zata rika zuwa kiranshi.

Shikuwa binta yayi da kallo yadda tayi wani kyau kamar ka sace ka gudu sai dai kash nakasun ta daya!batada hannu daya mikewa yayi yayi toilet ya wanke fuskarshi ya goge da tissue ya fice.

Dukkanin yan gidan sun hallara kan dinning table din dake dauke da kujeru wajen zaman mutum talatin Sha biyar a gefe guda haka dayan gefen ma yara da manya yammata da samarai iyaye da kakanninsu kowa na jiran ayi serving nashi Anti Amarya ce ta mike ta fara serving nasu inda Aisha ma ta mike tace sai tayi nan suka cigaba dayi tare.

Da wuri Aisha ta karasa wajen Haidar tafara serving nashi a hankali tare da lafta mishi nama me yawa a gabanshi tana mishi kallon so.

Khadijah ce ta sauke wa Aishar harara kana taci gaba Abinda take yi,dukda Aishar ta gani Amma bai dame ta saboda tasan cewa Khadija na son Haidar amma ba kamar yadda take son shi ba,sai dai kuma batason bata ran yar' uwarta ko kadan,nan jikinta yadanyi sanyi.

Dariya ne yaso kwacewa Khaleel yadda yadda tana ta lafta nama a nashi tunanin Bata iya serving bane, kana ya dake yace "unty Aisha nima kiyi serving nawa"

Harara ta sauke mishi kana ta wuce wajenshi tafara serving nashi tana kuma harararshi shima sanya mishi namar tayi dayawa.

Unty Amarya ce ta juyo tace Aisha zo da Abincin nan nama ya kasa zan sawa bappa dasu Alaji su Kaka sun samu nasu.

Da yake Aisha tasan cewa Ahalin bakwai ne a gidan nasu sai kuma su kakanninsu da yara-yara yasa tace "to Anti Amarya".

Duba kwanon naman Aisha tayi taga saura tsoka biyu kanana dago ido tayi ta fara warowa tana kallonsu daddaya a wajen....

Shin Yaya Haidar zai so Aisha kuwa? yaya kuke ganin Ahalin akwai fa munakisa a kasa wallahi Khadeeja fa son shi take wani irin hukuncin kuke gani zata yiwa Aisha yar fulani?

AISHAWhere stories live. Discover now