3

97 21 0
                                    

AISHA

Na
Walidation S Mapi

3

~Umman Aishar suka kira tazo dakin saurin ciccibar ta sukayi suka bar part nasu Maleeka suka nufi part nasu Aishar kwantar da ita akayi aka dauko maganinta aka shaka mata a hanci nan ta ja wani numfashi me tsayi ta juya dayan gefen tayi bacci.

Ajiyar zuciya Maleeka ta sauke kana tace "Alhamdulillah"

Umman Aisha dake hawaye ne ta juyo ta fuskanci Maleeka tace "meya faru?" saboda tasan cutar Aishan baya tashiwa sai in tana cikin damuwa.

Maleeka ce tayi musu bayanin komai da komai har yadda sukayi da Nasir din.

Umma ce ta girgiza Kai tace "ba matsala yanzu zata tashi kinji ko kada ki damu kanki"

Maleeka ce tace "to umma Amma gaskiya wallahi raina ya tsinke"

"Kada ki damu kanki"

Gwaggo Rabi dai bata tanka musu ba jimamin wannan cutar kawai take saboda yaki ci yaki cinyewa Allah ya taimaka ma yau bai zo mata da tarin ba.

*******
Haidar na zaune a office yana Aiki tunanin gida ne ya fado masa babu wacce ya fara tunawa sai Aisha,yadda take bashi daraja da kima harga Allah yana son Aishar amma bata kyauta mishi ba Sam ya za'ayi ta bada hannunta daya don taimakon na wani? meyasa zata cucesu dashi da ita?gaskiya bazai iya Auren miskiniya me hannu daya ba ai wannan yawa ne yadda yake da aji cikin Abokansa amma a ce me hannu daya zai Aura kai Ina bazai iya ba,buga desk din gabanshi yayi tare da cewa "Aisha kin cuce mu" wanda yayi dai-dai da shigowan Hamma wuro cikin office din.

Karasawa yayi wajen shi da gudu tare da cewa "lafiya kuwa Gadanga?"

"Lafiya kalau" ya fada a takaice yaci gaba da latsa laptop din.

"Amma ya naji kana Ambaton Aisha?kodai laifi tayi maka?"

"A'a bakomai"

"Look Haidar kada ka boyemin komai nifa dan uwanka ne kuma bana shiga harkar kowa a family dinmu sai ya shiga tawa,kai lura kana cikin damuwa fadamin me ke faruwa?"

Tabbas yasani indai Hamma wuro ne baya shiga harkar kowa sai an shiga tasa yasa yace "ga waje zauna na fada maka damuwata"

"Yawwa don ni gaskiya banson in rika ganin mutum cikin damuwa" samun waje yayi ya zauna yana fuskantar Haidar din.

"Hamma!wallahi matsala gagaruma ce narasa yadda zanyi in samu mafita,kuma kasani cewa a wannan Ahali namu Auren hadi kawai ake babu Auren bare"

Hamma ne ya dube shi da kyau yace "wato bare kake so ko?"

"A'a ba haka zancen take ba Hamma,Aisha nake so"

Hamma ne ya waro ido yace "what! wancan fitsararriyar kake so?yarinya sai rashin kunya,da nuna isa"

"Wannan duk ba halin Aisha bane,kawai kaine kake yi mata kallon haka saboda kana daukar kanka babba a family dinnan ita Kuma batason girman kai shiyasa baka shiri da ita Amma indai Aisha ce to na tabbatar babu me zagin tarbiyyarta a cikin wannan Ahali namu sai kai"

"Okay cin fuska ne abin?"

"A'a Hamma kayi hakuri babu batun cin fuska ko kadan gaskiya nake fada maka"

"Amma kai Haidar kana ganin zaka iya Auren wacce bata da hannu daya?dubeka fa da kyau gaka fari ga hanci ga manyan idanuwa ga kuma karamin baki infacts kana da cikar halitta Amma kake ja wa kanka Auren nakasasshiya?"

"Hamma kaima fa kasan cewa Aisha ta fini kyawun da kake lissafawa nesa ba kusa ba,kuma wannan rashin hannu sadaukarwa tayi"

"To wa waye ta sadaukar din?" Hamma ne ya tambaya.

AISHAWhere stories live. Discover now