NI DA YAYA SADEEQ
Love story
Na
Siddiqatulkhaireey Yahya
(S beauty ✍️)
*EWF*📚✍️
_________________________________
Page 02بسم الله الرحمن الرحيم
_________Inna tace, "daure ki tashi ki kaiwa yayan ki abincin sa, kinga daga aiki ya dawo ya gaji ga yunwa".Ɗaure fuska ta nayi ina turo baki nace, "ni dai Inna bazan kai mishi ba, duka na zaiyi, baki ga yadda yake bina da kallo kamar wani tsohon maye ba, kwana biyu bai samu ya dakeni ba, kinsan halin muguntar sa ba sai nayi masa laifi ba, yana iya ina shiga ya rufo ƙofa, ya jibge ni, kin san
shi kullum cikin jin haushi na yake"."A haba, yau dai Garba ko kunnan ƙashi ne dashi bazai dake ki ba, kina kallon yadda na tsawatar mishi a gaban ki, idan ko har ya kuskura ya taɓa ki saina haɗashi da Alhaji Ƙarami, tashi maza kije ki kai mai yar albarka".
"Yo ina abincin nasa yake?".
"Yana kitchen mana, inda kika ɗauko naki".
koda na ɗauko abincin a saman kaina na ɗorashi ina ɗigir-gire.
"A a fa kada tsautsayi yasa ki zubar mai, kinga yana cikin fushi, babu abinda bazai iya miki ba". A cewar Inna
"Haba Inna bazai zube ba sai dai idan kece kike so ki zubar dashi, amma ai ba yau nikeyi ba, kuma bai taɓa zubewa ba".
"To Allah ya bada sa'a" ta faɗa tana mai shigewa ɗaki abinta.
Ni ko na cafke da "Amin hajiya Inna".
Ina tafe ina 'yan waƙe na, ina tafa hannu, hanyar ɗakin yaya Sadeeq na nufa saboda yana daga hanyar waje ne. Koda nazo bakin ɗakin ban tsaya yin sallama ba, kuma ban buga kofar ba, duk da yasha yimin gargaɗi a kan indaina shiga masa ɗaki, ba tare da nayi sallama ya bani izinin shiga ba, ko kuma na buga masa kofar. Amma tsabar taurin kai irin nawa sai naki yin ko ɗaya acikin umarnin shi, kawai bankaɗa ƙofar nai, Ina tura ƙofar na bankaɗa labule nakutsa kaina ciki. Yanayin da naga yaya Sadeeƙ ne yasa nasaki wata uwar ƙara, har saida kular abincin kaina ya faɗi, murfin kular ya buɗe dambun ciki ya watse.
A fusace yah Sadeeƙ ya nufo ni, kamar mayunwacin zaki, kamin in ankara ya wanka min kyawawan maruka, haske nagani wal-wal a idanu na, har saida ji na ya d'auke na wasu 'yan daƙiku, ba wani abu ne ya firgita ni ba, illah ganin sa da nai babu riga, kirjin sa ɗauke da yalwataccen gashi baki siɗik dashi, kwance luf-luf bantaɓa ganin ɗa namiji haka ba tunda nike a rayuwa ta, ja da baya na fara yi, ina rawar baki, yayin da shi kuma yake nufo ni, haƙiƙa na furgita dashi matuƙa. Saboda haka na fara ihu iya ƙarfina, yadda Inna zata iya jiyo ni, tazo ta cece ni.
Takaici na ne ya kuma kama shi, cikin zafin nama ya cafko ni, belt ɗin jikin wandan sa ya zaro, sai alokacin nai yunƙurin guduwa daga ɗakin. Amma ina aikin gama ya riga ya gama, saboda riƙe yake gam da hannu na, maida ƙofar yai ya rufe harda samata kye da sakata, kana ya soma duka na, kamar Allah ya aiko shi, kota ina zabga min belt ɗin yake yi. Ihu nikeyi da duka murya ta, saboda naga so yake ya kashe ni, tun kamin lokaci na yayi.
Inna dake cikin ɗaki tajiyo ihuna da gudu ta fito tazo bakin ƙofar ɗakin sa, buga ƙofar tafara, tana kiran suna na da ƙarfin ta, ganin ba kiran sunan nawa ne mafita ba yasa tafara kiran sunan yah Sadeeƙ, Garba Garba kada ka kashe 'yar mutane na shiga uku, dan Allah ka yaƙuri ka ƙyaleta haka nan, komai tai maka ai tadaku, bazata ƙara ba daga yau insha Allah".
YOU ARE READING
NI DA YAYA SADEEQ
Short StoryEvery love story is beautiful but ours is my favourite. Na tsane ki wawuya duk ranar da kika ji ni SADEEQ nace ina son ki kada ki taba yarda dani sbd ba gaskiya bane yaudarar ki zanyi... Kaka kara kaka kada ku bari a baku labari saboda salon na daba...