NI DA YAYA SADEEQ
•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•
No editing
Chapter 33
_______zaune nike a dakin Ladiyo muna firar mu gunin ban sha'awa sai wasa da dan ta Mamman nike yi, tace "wai ke Siddeeqah yaushe zaki tare a dakin mijin ki ne?"
Nace "waya gaya miki zan tare? Nida nike jira ya bani takarda ta naje na auri wanda yake kauna ta".
Bakin Ladiyo bude tace "amma dai baki da hankali, a wannan zamanin ka samu miji irin yah Sadeeq ai ka more, ke sune fa irin mazan da ake bada labarin su a novel, amma kike nema kiyi fatali da damar ki".
Nace "bazaki gane bane, mubar maganar kawai" bayan na bata kyautar kudi nai mata sallama nace "taya kuri nazo mata da kaya sai na bude a kwati na zan kawo mata"
Gadiya tai min har bakin zaure ta rako ni
A hanya na hadu da wani mai naci tun na fara tafiya yake bina yana min magana amma ban kula shi ba.
Har bakin kofar gida ya rako ni inda yah Sadeeq da Yah Mubarak ke zaune suna fira, da gani na Sadeeq ya hade rai kamar ya hangi mutuwa, tasowa yai ya nufo mu kan ya karaso na shige gida ban san ya ya kare da mai bin nawa ba.
Koda shiga na gida Ammi ta hau yin sababi Momy na kare min nan na barsu nai cikin daki na inda na samu Fadeela na ta sharbar baccin ta. Jiddah na zaune na chat Khadija kuma na ninke kaya.
Bayan na cire mayafina na zauna kusa da Khadija ina taya ta ninkin kayan
Jiddah ce ke cewa "yau fa aunty Bilkeesu zata zo".
Khadija tace "au haba na dauka sai ranar Sallah"
"A a yau ne" ta bata amsa
* * * * * * * * *
Yau take sallah bikin daya rana gidan mu cike yake da yan uwa da abokan arziki da makota, anci ansha yara nata har kokin su. Wa'inda suka san inna da dadewa suna ta taya ta murnar bayyanar diyar ta.AUNTY balki sai tsokana ta take wai yayan su zai kamani.
Little Easha ce ta shigo tace "aunty Siddeeqah yah Sadeeq na kiran ki"
"To" nace amma ban tashi a lokacin ba sai da na gama shan kanshi na
Ina ta raba mutane har na wuto falon. Shima tsakar gidan cike yake da mutane suna cin abinci gunin burgewa.
Dakin yah Sadeeq na nufa bayan nayi sallama ai min izinin shiga na shiga.
Tasowa yai ya maida kofar ya rufe kana ya kama hannu na ya zaunar dani bakin katifar sa yace " na gaji ne shine na kira ki ki mun tausa".
Dago kai nai muka hada ido ya daga min gira gajeran wando ne a jikin sa sai rigar shan iska wato bes fuskar sa kuwa dauke take da saje ga dan gemu ya aje gunin burgewa.
Kwanciya yai yace " fara nana " ido na zaro waje nace "yaya me zan fara kuma? Wallahi ban iya ba"
Tashi yai ya zauna yace "to shikenan bari na gwada miki inyaso sai ki min yadda nai miki ".
Da sauri nace na iya ba sai ya min ba amma yace "Allahn kashe sa sai ya gwada min"
Ya na iya haka ya Sadeeq yai ta jagwalgwala ni, tun yana yi cikin hankalin sa har ya fara fita hayyacin sa dan kokari yake ya rabani da kayan jiki na.
Kuka na sa masa ina magiya akan ya rabu dani " ganin haka yasa ya sauka daga kai na yai gefe idon sa a rufe yana jin marar sa na murda masa, take ya fara juyi yana kiran sunan Allah, yanzu na fahimci dalilin wannan ciwan na yah Sadeeq da tun ina karama naga yana yi, amma gaskiya bazan iya basa kaina a wannan halin ba, ganin ciwan nasa na kara tsanan ta yasa na mike da hanzari na fita daga dakin, a tsakar gida na hadu da Ammi, ta ganni kamar bana cikin hayyaci na tace "lafiyan ki kuwa duk kin sukurkuce?"
YOU ARE READING
NI DA YAYA SADEEQ
Short StoryEvery love story is beautiful but ours is my favourite. Na tsane ki wawuya duk ranar da kika ji ni SADEEQ nace ina son ki kada ki taba yarda dani sbd ba gaskiya bane yaudarar ki zanyi... Kaka kara kaka kada ku bari a baku labari saboda salon na daba...