NI DA YAYA SADEEQ
بسم الله الرحمن الرحيم
Chapter 07
Ya ansa gorar ruwan ya fara sha, saida ya shanye ruwan tas sannan yace "malam kayi min bayanin matsala ta nasan dai ba waccar matsalar bace".
"Eh ba ita bace" Farooq ya bashi amsa
"Amma a bisa binciken danayi, ya nuna kayi amfani da abu mai saka fatar jikin mutum ƙaiƙayi acikin ruwan da kayi amfani dashi, sannan shima wannan raɗaɗin da kake ji kayi amfani da abu mafi zafi ajikin fata, shiya sa yake maka wannan raɗaɗin". Dr Farooq ne yayi wannan bayanin.
Shuru Sadeeq yay kamar meyin nazarin wani abu, be tuna komai ba, Dan haka ya taɓe baki yace "Nidai nasan ban saka komai cikin buta ta ba amma zanyi bincike, saboda abin da mamaki".
"Dadai yafi". Farooq ya bashi amsa ya kuma cewa "katashi muje akwai magun-gunan da zan rubuta maka zasu temaka sosai, wajen rage maka raɗaɗin da kake ji".
♾️♾️♾️♾️♾️
Ina zauna a kan kujera a tsakar gidan mu, ina dakan kayan miya yamma ne lilis, saiga Ladiyo kawata nan ta shigo jiki duk kwata, tun daka nesa nike ɗaga mata hannu, saboda kada ta ƙaraso inda nake, bazan iya jure shakar warin kwatar da ke jikin ta ba, ida nuwan ta jawur dasu, alamun taci kuka ta ƙoshi.
Saida nayi dariya mai isa ta sannan nace " ke Ladiyo garin ya kikayi wanka da kwata a jikin ki kamar sabon shiga hauka?".
Takaici na ne ya ishi Ladiyo na dariyar da nike mata, ga tambayar rainin hankali dana jefe ta dashi.
Cikin shash-sheƙar kuka take cemin "Ummata ce ta aike ni na kai mata niƙa, bayan nakai annuƙo, akan hanyata ta dawo wa gida na haɗu da su Habibalo, itada Larai sukai ta zagi na, naƙi kula su, nayi ƙoƙarin ganin na cigaba da tafiya ta, amma suka hanani wuce wa, wai sai nayi dambe. can saiga Atinen Malam Bala nan Shine tace "wa na kama wai jiya ni dake munwa ƙanwar ta duka, haƙuri na fara bata, amma suka samin dariya, wai wallahi sai sun rama wa ƙanwarsu dukan da da kika yi mata, shine suka haɗu sukai min dukan tsiya, sannan suka jefani a cikin kwata". Ta ƙarasa maganar hawaye sabbi suna zubo mata ta ciga ba da faɗin "basu tsaya iya nan ba saida Suka zubar da ƙullun wainar da na markaɗo".
Wata muguwar dariya ce ta ƙwace min ban san da zuwan ta ba, saida nayi mai isa ta.
Sannan nace mata "wallahi Ladiyo ke sakarya ce ki ka tsaya kamar kayan wanki suka jibgeki,
🤣Baki iya koda mintsilun su ba, Hhmm ai da ni ce koda ya ƙushi da cizo saina rama, kindai san halina, ni yanzu da ki kazo ki ka faɗa min inyi miki me? ai da zuwa gida ma ki kayi Umman ki ta miki dukan da zata miki da tuni ya wu ce, amma a nan kina ƙarawa kanki laifi ne a gun umman ki, kuma kin santa da jaraba".Wani sabon kuka Ladiyo ta kuma fashe wa dashi,
Ni kuwa sai ƙyalƙyala dariya nikeyi harda rike ciki abin nema ya samu.
Dundun da naji an ɗuma min a bayana ne ya dawo da ni haiyaci na, Inna ce tsaye tana huci.
Tsuke baki na nayi nace "Inna kin wai me nayi miki ne?".
Cikin jaraba irin ta tsofaffi Inna tace "ja ira ba ke kika ja mata du kan ba, amma tana faɗa miki kina yi mata dariya".
Ta juya ta kalli inda Ladiyo take tace "kema ai da naki laifin, Ladiyo kina san kiyi tsokana amma ba kida ƙarfi, kuma tsokana ta mara tsoro ce, tunda ba zaki iya cire tsoro ba, sai kidena biye mata, idan ba haka ba wataran karyaki za ai".
Jin Inna tace za'a ɓalla Ladiyo yasa na ƙara kwashewa da dariya.
Cikin takaici na Ladiyo tace "ke ai sunce idan suka kama ki ɓaɓɓalla ki za suyi".
YOU ARE READING
NI DA YAYA SADEEQ
Short StoryEvery love story is beautiful but ours is my favourite. Na tsane ki wawuya duk ranar da kika ji ni SADEEQ nace ina son ki kada ki taba yarda dani sbd ba gaskiya bane yaudarar ki zanyi... Kaka kara kaka kada ku bari a baku labari saboda salon na daba...