NI DA YAYA SADEEQ

1.9K 92 7
                                    


NI DA YAYA SADEEQ
                 

              Na
Siddiqahtulkhaireey Yahya
            (S beauty ✍️)

                 EWF📚✍️
_________________________________

Page 05

Bayan gama cin a bincin mu da Umar na miƙe ina hamma alamar bacci nike ji.

Khadija ce ta kalle ni tace "ba dai bacci za kiyi ba". Nabata amasa da "eh kwanciya zanyi".

"Dawuri haka" ta tambaye ni

Da "eh". Na bata amsa

"Yo in banda abinki khadija ai Allah kaɗai yasan inda Siddiƙa taje bayan fitar ta gida, kinga ko dole ta kwanta da wuri". Inna ce dake kwance tace haka, taɓe baki na nayi nace "Momy zan kwanta saida safe".

Wayarta ta kunna ta kalli a gogo ƙarfe goma saura na dare, kallon Khadija Momy tayi tace "kitashi kibita dare yayi goma saura". Umar ma tashi yayi ze bimu amma Momy tace, bata yarda ba tare da ita zai kwana saboda ita batasan kwana ita kaɗai".

Akwai ɗakin da idan sunzo suke sauka acikin sa, duk wani abun buƙata Daddy ya zuba a ciki.

Sai da safe muka ƙara yimusu Khadija ta rigani yin gaba, ina cikin tafiya naji kamar na taka ƙafar mutum dayike lungun ɗakin a kwai duhu, ƙauyen dande kuma ba wuta, jannareto muke kunnawa zuwa ƙarfe goman dare a kashe, to yau yaya sadeeq be kunna ba. Ban gama tabbatar da ƙafar mutum bace a gurin, hakan yasa na ƙara ɗora kafata a kai na murza, 'yar ƙara naji anyi alamun mutum ne, koda na waiga inda nike tsammanin zan sami Khadija wayam babu ita ba alamar ta, zaro ido na nayi da kyau gabana ya soma dakan uku-uku, sakamakon tunawa da nai ba wani bane illah Sadeeq.

A ɗan tsorace nace "la! yaya". Ban ƙarasa maganar ba ta maƙale, sakamakon bige min baki da yayi, gami da shaƙe min wuya,ya haɗani da jikin bango, Yana faɗin me hali be fasa halin sa gwara na kasheki kowa ya huta, sa'anki ne ni zaki murje min yatsa eye?.

Da iya ƙarfin sa ya shaƙemin wuyan, ina son inyi ihun neman ɗauki amma na kasa, cikin ikon Allah saiga Momy da Umar, sunzo wucewa hannun ta ɗauke da hasken fitilar wayar ta, tana haskawa, mai zata gani wani ƙara tasaki saida wayar ta yafaɗi a ƙasa, Inna da khadija rige-rigen fitowa suka yi saboda ihun Momy da suka ji.

Umar tuni ya das-kare a gurin, jikake tas tas ƙaran marin da Momy ta wanke yaya Sadeeq

Amma duk da haka yaƙi sakina, don haka ta ƙara mai wani saida tayi mai mari biyar amma ko gezau, beyi ba dayike yah sadeeq namijin duniya ne, "to idan baza saketa ba sadeeq zan cireka cikin 'ya'ya na".  ta faɗi haka fiskar ta babu alamun wasa.

Jin wannan lafazin na Momy yasa Sadeeq yayi jifa dani, idanuwan sa jajur kamar Wanda yasha wani abun, huci yake yi sosai

Kasa nafadi shirim jikina babu ƙwari, ina fitar da numfashin wahala Inna da Khadija takaici ya hanasu magana, hawaye ne ke gangan garowa a cikin Idanuwan Momy, ta kasa magana hannuna ta kama muka wuce ɗaki na, su Inna na biye da mu abaya, kan gado ta ɗorani, na kwanta yaraf, ruwan fridge me sanyi khadija ta ɗibo min ta ɗaga kaina ta bani nasha ina maida numfashi.

Babu Wanda ya tambayi me ya haɗamu, duk kuwa da cewa zuciyoyin su cike take da tambayoyi, daga haka kowa ya tafi ma kwancin sa.

a raina kuwa saƙa yadda zan wulaƙan ta yaya sadeeq nikeyi, domin wallahi bashi yake ci wani mugun tsanar sa naji ya ƙara da ɗuwa a zuciya ta.

da wannan tunanin bacci ɓarawo ya sace ni.

Kiran sallar asuban fari a kunne na akayi, banida nauyin bacci, tashi nayi na zauna gaba ɗaya jikina ciwo yake min amma wuya na yafi min ciwo.

NI DA YAYA SADEEQ Where stories live. Discover now