NI DA YAYA SADEEQ14

1.4K 105 12
                                    

✨✨✨✨
NI DA YAYA SADEEQ
✨✨✨✨

بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Chapter 14

_____"To". Nace wa Momy na nufi hanyar kitchen bayan na shiga na d'auko kular abinci da zobon da Momy ta hada mai akan wani madai dai cin tirai na d'oro su sanda na fito babu kowa a falon har Momy ta wuce d'akin ta, saboda haka nima na haura sama sai da na fara zuwa daki na na sauya kaya na saboda izuwa yanzu nima na fara sabawa da kayan baccin idan ba dasu ba bana jin dadin baccin saboda haka na sauya izuwa wata farar doguwar riga, mai kauri ta bacci akwai wata yar baza mai kamar leshi a gaban ta ina sauyawa na nufi bangaren ya Sadeeq da yake dan nesa da mu saboda saikin bi ta wata kofa sannan zai sadaki da bangyaran sa dake dauke da falo da d'akuna 2 sai bayi da kitchen, nayi sa'a saboda kofar shiga a bude take ina murmushi na karasa ciki saida na gama karewa falon kallo sannan naja dogon tsaki ina ta'ba baki na ce "shi ko kunya baya ji daki sai kace na mace". A bude na bar kofar sannan na wuce bedroom din sa da shiga ta naga gado a gyare luf luf dashi ya lailaye zanin gadon sa ji nayi ina sha'awar hawa gadan saboda haka na ajiye kular abincin a kan wani teburi nayi sufa kan gadon😜 ina 'yan tsalle tsalle na ina dariya ni kadai

♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾

Tafe yake a kan hanya tunani ne fal a cikin zuciyar sa ya sa'ka wannan ya warware wancen, duk da tuki yake yi amma yayi zurfi a cikin tunanin sa ta yadda bai san mai yake yi ba Allah ne ya tsare sa da kuma kasan cewar ba akan babban titi yake ba ringing din wayar sa ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula fir gigit Sadeeq yayi saida ya dafa kansa "ya Salam ni Sadeeq mai ke damu na haka wani irin tunani ne kuma akan me nike yin sa mtssss" .yaja dogon tsaki ba shida amsar tambar sa saboda haka ya lalubi wayar sa da yaji tana ringing bai wani tsaya ya kalli sunan wanda ke neman sa ba yana dauka ya kara a kunne.
Daga d'ayan bangar akace "wallahi aboki baka da mutunci daka zuwa Abuja ganin Princess sai ka manta damu, munafuki amma da anyi magana kace baka son yarinya ka tsane ta".

"shege akace maka kowa mayen mata ne irin ka ka rasa dawa zaka hada ni sai da yar karamar yarinya wacce ko...".

"haba malam kada kacika min baki daga karshe kazo ka fada tarkon yar yarinya".

"Wa ni?!". Ya fada yana nuna kan sa da yatsan sa ". Kamar Farooq din yana ganin sa "Allah ya kyauta ai na fada mata duk sanda taji nace ina son ta kada ta taba yadda dani saboda ba da gaske bane".

Farooq baiji dadin yadda abokin sa yayi su'bul da baka ba saboda haka yace "uhm Sadeeq idan Allah ya tashi kama ka bazai maka kadan ba kuma gaskiya bazan ji tausayin ka ba koda zanji sai ka ji jiki, saboda duk abinda ka Shuka shi zaka girba dama na kira ne naji ya kake ya Momy tunda duk kuna lafiya sai da safe".

"Kaga Farooq kada ka kashe a kwai maganar da nike so muyi".

"Ina jin ka to"

"yanzu haka fa a hanya nike naje naga gimbiya ta, gaskiya babyn ta hadu tafi kyau a fili nike fad'a maka komai yaji zam-zam hhhmm nasan ba lallai ka yarda ba tunda kaki ko hotan ta ka gani amma tun na ganta na shiga wani yanayi".

"Haba Sadeeq daman wannan ce maganar da kace za muyi?.

"Eh amma da akwai d'ayar nafi zumud'in wannan shiyasa na fara fada maka ita" kuma kasan nace "Momy ce take nema na ashe akan makarantar yarinyar nan ne to shine nike so ka nema mata admission a makarantar da Sadiya take saboda na cewa Momy na gama komai tafiya ta rage".

Shuru Farooq yayi na wasu yan da'ki'ku alamar nazari can ya numfasa yace "haba Sadeeq wai meke damun ka meyisa kake son ka kuntatawa yarinyar mutane wani irin makarantar kwana ana zaune 'kalau don Allah kajanye wannan maganar kaji tausayinta
Har yanzu fa Siddy yarinya ce karama na tabbatar ma batasan maye aure ba da tasani wallahi da...". Bai karasa maganar ba Sadeeq ya dakatar dashi da cewa "malam don Allah ba shawara na tambaye ka ba
Dan kaga na biyo ta hanyar ka shine zaka tozartani idan baza kaimin ba kawai ka fadamin"

NI DA YAYA SADEEQ Where stories live. Discover now