NI DA YAYA SADEEQ 22

1.2K 124 21
                                    

NI DA YAYA SADEEQ

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Chapter 22

To bayan fitar su Zuby gidan su Lubancy suka zarce dake wata unguwa amma unguwar ba ta masu kudi can bace, kuma ita Lubancy iyayan ta sun rasu tun tana yar karama, a gurin kawun ta take, kasance war sa namiji ba ko da yaushe yake gida ba shiya yasa Lubancy ta zama abar da ta zama yanzu duk da matar kawun na kokari amma sam Lubancy ta raina ta bata jin maganar ta, ganin Allah bai bata haihuwa ba kar ta cika matsawa ace dan bata son zafin yara bane shiyasa ma yanzu ta zuba mata idanu, in dai duniya ce wanda bai zo ba ma jiran shi take.

Duk da sun sami matar kawun a tsakar gida, haka su ka wuce ta ba tare da sunyi mata sallama ba, da shigar su dakin Lubancyn suka wuce suna wani  shan kamshi.

A cikin zuciyar ta take musu adduar shiriya dan baza tayi musu mugun fata ba kuma Allah na gani tayi iya bakin kokarin ta dan ta san abin da suke aikata wa ba abin arziki bane, ta bar ma Allah saboda duk zagin da mutanen unguwa suke mata yana dawo wa kunne ta a cewar su "dan ba yarinyar ta bace shiyasa ta barta tana yin abin da ta ga dama". Amma ita ta san d'a a wannan zamanin ko kai ka haife shi sai kayi hakuri da shi.

* * * * * * * * *
To bayan sallar isha'i ne Daddy ya ce wa Momy "ta je ta kira masa yaran gidan zai yi magana dasu". Ba tare da tayi musu ba ta ce mai "to".

Falo ta fito in da ta kwalama Suwaiba mai aiki kira, nan take suwaiba ta zo tace "na'am". Momy tace "haura sama ki kira min yaran nan, ki tabbatar kin fada ma ko wacce su".

"To Hajiya".
Suwaiba ta fada kana ta haura sama

Dakin Khadija ta fara zuwa in da ta shiga buka kofa  ba ta wani bata lokaci ba Khadijan ta zo ta bude kofar ganin Suwaiba tsaye tace "Suwaiba lafiya?".

Suwaiba tace "lafiya lau Hajiya ce tace "tana son ganin ku".

To kice "gamu nan".

Da "to". Suwaiba ta amsa

sai da tabi duka d'akunan yan matan ta sanar musu, sannan ta sauko kasa inda ta tarar da Momyn inda ta bar ta take ta shaida mata gasu nan zuwa kana ta koma bakin aikin ta.

Ku san a tare Siddeeqah da Khadeeja suka sauko dan sun ruga kowa fito wa a lokacin falon babu kowa sai TV da yake a kunne yana karatun Al'qur'ani mai girma

Kusan tare suka zauna kan kujera kowa da abinda yake sakawa cikin ran sa, can dai Khadija tace "sister yau ba magana ne?".

Ita Siddeeqah ba rufi ne da ita ba saboda haka ta mayar wa da Khadija amsar ta da cewa "yo gani nayi kina wani share ni nayi tunanin kina shigar ma Jiddah ne shiyasa ki ka ga ban kula ki ba, saboda na yarda na bata da kowa a gidan nan in dai akan kwatar yanci na ne".

Bata karasa maganar ba Jidda ta sauko ganin Siddeeqah a zaune yasa ta ja dogon tsaki ta ce "sis Khadee me yisa ki ka zauna tare da wannan abar".

Khadija tace "wa fa?".

Nuna ni tayi da yatsa ba tare da ta jiwo ta kalle ni ba,

ganin haka yasa na mike cikin masifa na kama hannun nasa abaki na ganna mata cizo kana na koma gurin zama na kamar ba ni nayi ba.

ai kuwa ta shiga yin kuru-ruwa wanda yai sanadin fitowar su Daddy, Ummi ma da take sama ta ji ihun cikin sauri ta sauko har ta kusan tayi tun tube saboda ko gaban ta bata kalla ba.

Kafin su Daddy su ce wani abu yah Sadeeq ya shigo bakin sa dauke da sallama amma saboda ihun da Jiddah take yi babu wanda yaji sallamar.

Da ma-maki dauke a fuskar Sadeeq ya kara so cikin falon ya ma rasa wa zai tambaya abin da ya faru saboda haka ya jingina da bango ya harde hannayen sa waje guda

* * * * * * * * *
Bayan shigar su Zuby dakin Lubancy ta maida kofar dakin ta rufe da mukulli, kusan zan iya cewa Lubancy bata gajiya da da romance saboda haka ta shiga shafa jikin Zuby take ita ma tsigar jikin ta ya fara tashi nan take suka shiga cire ma juna kaya bayan sun gama suka fada kan katifar Lubancy suna nishi sama sama take suka fara tso-tse tso-tsan juna suna fada ma juna kalamai masu dad'i.

Wa iya zu billah Allah ka shirya mu kashir ya zuri'ar musulmai baki daya

* * * * * * * * * *
Sam sadeeq bai son hayaniya ganin Jiddah bata da niyar yin shiru ya daka mata tsawa, nan take tayi tsit kamar ruwa ya ci ta sai shash-sheka da take yi a kai a kai, sai a lokacin Daddy ya nemu guri ya zauna kana Momy ta zauna ita ma.

Da hannu Daddy ya nuna ma Sadeeq din Kujera alamar ya zauna babu musu ya zauna, an dauki kusan mintuna hudu babu wanda yai magana can dai Daddy yai gyaran murya yace ma Jiddah "ke! Tashi ki zauna".
Saboda a lokacin Jiddah a duke take kan ta a kasa tana sash-shekarar kuka.

Ita ma babu musu ta nemi kan Kujera ta zauna kusa da Ummi sai murza idanuwa take yi.

Bayan ta zauna Daddy yace kafin na fara cewa komai "ku tashi muje muyi dinner".

Gunin sha'awa zaune suke reras a kan dinning din ba ka jin sautin kowa sai karan cokula saboda Momy ce tayi girkin abincin ba karamin Daddy yayi ba jalof din taliya ce da kuma farfesun kaza ga farfesun kifi ga kuskus haka ban garen drink ta hada jus kala-kala dan Momy ba baya ba wajen iya abin ci.

Ina cikin ci Inna ta fado min a rai saboda haka na ijiye cokalin nayi tagumi kwalla na zubo min, Daddy ne ya lura da halin da nike ciki yace "A a mai gaskiya mai kuma aka miki?".

Cikin kuka nace "Daddy Inna na tuna tun nazo banyi magana da ita ba".

Yace "ai ba kuka zaki ba ko Sadeeq ki ka ce ma kina son magana da ita zai kira miki it maza dai na kuka bari mu kammala cin abinci sai a kira miki ita ko".

Ya karasa maganar cikin sigar lallashi nace "to Daddy

 

* * * * *
My Fan's
Please ku cigaba da bani hadin kai saboda shine karfin gwuiwa ta

Dan Allah Wanda beyi following dina ba dan Allah kuyi yanzu sannan ku cigaba da danna min vote kuna aje min comment please show me love 💞❤️

NI DA YAYA SADEEQ Where stories live. Discover now