NI DA YAYA SADEEQ
بسم الله الرحمن الرحيم
Chapter 10
GARIN ABUJA
Bamu wani tsaya akan hanya ba, Dan Momy tace duk mai uzuri yayi haƙuri, ya riƙe har mu isa gida, saboda ance mata hanya babu kyau, Da misalin 'karfe 3:25pm muka isa garin birnin tarayya Abuja, tun daga unguwar zaki san ba irin unguwar nan ce ta kowa da kowa ba sai ɗan wane da wane tunda ga wajen gidan Daddy zaki san gidan manya ne saboda ko fulawowin kansu da aka zagaye gidan dasu abin kallo ne, ba sai ka shiga daga ciki ba, yawancin gidajen un'guwar ginin gidan sama ne, idan ki kaga wannan sai kiga duk yafi kyau, amma kina ganin wani sai kice wancen bai kai wannan ba, to haka dai gidajen unguwar suke, na wane yana wane na wane,
Ba yau na saba zuwa ba amma har yanzu na kasa riƙe sunan un'guwar Saboda ita kan ta sunan un'guwar na 'yan gayu ce, kuma da turan ci ne 🤔
Gidan su Khadijan ma yana ɗaya daka cikin ƙerarrun gidajen saman dake un'guwar, shiyasa nike son zuwa saboda ina son bene a rayuwa ta.Driver yayi horn adaidai bakin ƙaton get din gidan
Me gadi ne ya leƙo ta ƙaramar ƙofa, ganin motar Momy ne yasa shi saurin wangale get motar mu ta sulala ciki, mai gadi ya maida get ya rufe.
Daka bisani yazo da gudu ya buɗewa Momy ƙofa, cikin ladabi yake yi mata sannu , fuskar Momy a sake cike da annuri ta amsa masa "mun same ka lafiya?". "Lafiya lau hajiya". Mai gadi ya faɗa yana sadda kansa ƙasa, alamun girmamawa "masha Allah babu dai wata matsala ko?". Momy ta kuma tambayar Habu mai gadi, yace "eh Hajiya babu wata matsala komi yana tafiya daidai".
"A kwai kayan mu a bayan mota kashigo mana dasu ciki kaida Idi". Da "to" suka amsa su duka
A kasalan ce muka fito daka cikin motar muka shiga cikin falo, ko waccen mu tasan ɗakin ta dan haka muna shiga ko wacce tayi inda tasan nan ne dakin ta yake.
A sama ɗakin danike sauka yake don haka na haura abina amma dana murɗa hannun ƙofar sai naji a kulle yake gam.
ɗakin Khadija dake kallon nawa naje shima a kulle yake sai dai naji motsi da alamar ita tuni tana ciki ƙwan-ƙwasa ƙofar na shiga yi, daga can ciki tace "wace".
"Siddy ce". nabata amsa
Jim kaɗan sai gashi ta buɗe, jikin ta ɗaure da tawul da alamar har ta cire kaya wanka zata shiga
"Khadija mukullin ɗaki na nazo ki bani".
"To" tace ciki ta komo sai gashi ta fito hannun ta rike da mukullin na amsa nayi gaba a bina.
"Cikin ɗaga murya ta ce" to matar yaya a huce gajiya lafiya". Ai kwa da gudu na juyo dan na doke ta, amma sai tai sauri ta maida ƙofar ta rufe tana dariya
♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
A bangaren sadeeq kuwa yana barin ɗakin Inna bai zarce ko ina ba sai gidan abokin sa Farooq, bai kirasa a waya ba amma yayi sa'a saboda ya same sa ne yana ƙoƙari fita, nan dai ya bashi hannu suka gaisa Farooq yace "yanayin ka ya nuna kamar kana cikin damuwa, kuma ba ka saba zuwa gida na a irin wannan lokacin ba, kodai kai da mutuniyar taka ce? Saboda nasan labarin gizo baya wuce na ƙo ƙi, da fita zanyi na gaji da zaman gidan, amma tunda kazo mu shiga ciki ka faɗa min abinda ke tafe da kai".
To bayan sadeeq ya shiga ciki, bedroom suka wuce, saboda yanayin tsarin gidan irin me ciki da falo ne sai bayi da kitchen kuma duka haka gidajen kusa dashi suke saboda duka manyan 'yan sanda ne wasu suna da 1 star wasu biyu wasu uku wasu kuma igiya ce gare su, da dai sauran su kusan unguwa ce ta ma'aikatan 'yan sanda, shi yasa da wuya kaji ance wani abu ya faru a cikin ta ko kamar ace anyi fashi ko an sace wane, saboda a zagaye take da masu tsaro kamar barikin sojo ji shima Sadeeq saboda ansan shine, dan ko bai nuna id card ba ana barin sa shiga.
YOU ARE READING
NI DA YAYA SADEEQ
Short StoryEvery love story is beautiful but ours is my favourite. Na tsane ki wawuya duk ranar da kika ji ni SADEEQ nace ina son ki kada ki taba yarda dani sbd ba gaskiya bane yaudarar ki zanyi... Kaka kara kaka kada ku bari a baku labari saboda salon na daba...