✨✨✨✨
NI DA YAYA SADEEQ
✨✨✨✨˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙
Chapter 17
_____Ringing din wayar Khadija ne ya katse shirun nasu bayan ta fiddo wayar Sunan Momy ya bayyana akan screen d'in wayar da han zari Khadija ta d'auka ta kara a kunne tace "Aslm Momy". Daga can 'ban garen Momy ta amsawa Khadeeja da "W/slm Khadija naji ku shiru ne shine nace bari na kira naji ya ake ciki". "wallahi Momy lafiya lau anyi mata dressing din bakin ta ne sai karin ruwa da aka sa mata".
"sai yaushe kenan zaku dawo?".
"dazaran ruwan da ake 'kara mata ya 'kare saboda nurse d'in tace zamu iya tafiya ba wani ciwo bane kawai buguwan da tayi ne, saboda ce mata nayi fad'uwa tayi abayi ta bige".
"yayi kyau". Momy ta bawa Khadija amsa daga haka suka yi sallama♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Da bibbiyu Sadeeq yake tsallake steps soboda yana son yaje wurin cin abinci kafin a kira sallar azahar kici'bus yayi da Momy a dai dai lokacin da ya gama sauko wa daga steps din cikin sakin fuska Momy tace "ah Sadeeq ga fa abin karya wan ka can fuskar ka tayi zuru zuru nasan kuma yunwa ce kake ji"."eh wallahi Momy yanzu haka saurin da ki ka ga inayi restaurant zani".
Kafin Momy ta ba Sadeeq amsa Siddeeqah ta sauko daga sama d'an kwalin ta rike a hannun ta tana susur kanta d'ayan hannun ta kuma rike take da bakin zanin ta daya kwance tayi wani iri da ita yayanayin ta ya nuna alamar tana cikin damuwa
Kallon ta Momy tayi na wasu 'yan da'kiku bayan ta gama nazarin ta tace "Mai gaskiya lafiyan ki ki kayi zuru zuru dake ko kema yunwar ce".
"wallahi Momy nima haka kawai naji ni wani iri ina Ummi take?".
"Ummi tana sama tun da kuka haura tabi bayan ku kin san ta da bacci idan babu makaran ta tana can tana sana'ar".
D'an ta'ba baki nayi nace to ina Khadeeja?".
"ta raka Jiddah asbiti ayi mata dressing d'in gurin da taji ciwo".
"To Momy nima bari naje na huta".
"ba dai ki huta ba kije ki shirya Sadeeq ya kaiki gurin gyaran kai saboda jibi ne tafiya makarantar ki in Allah ya kaimu".
Jiki na ne yayi sanyi ni wallahi da zasuji ta tawa su 'kyale ni na cigaba da rayuwa ta a haka saboda banga aibin ta ba
"Maza mana kije ki shirya Siddeeqah tunanin me kike yi haka". Momy ta tambaye ni "babu komai". na fad'a ina haurawa sama
Maida duban ta tayi ga Sadeeq da yayi kicin kicin da rai kamar wanda akece ga ranar mutuwar sa "ba sai kaje restaurant ba ga kayan da mukayi breakfast can na hana suwaiba ta kwashe kaje ka karya saboda ka kai Siddeeqah wajen gyaran gashi kanta yayi wani iri"."Haba Momy asa idi driver ya kai ta mana ni inada uzurin da zanyi". ya 'karasa fad'a kamar zai rushe da kuka
Saida Momy ta 'kare mai kallo sannan tace "lallai Sadeeq kana da aiki tana matsayin matar ka ace sai wani driver ya kai ta gurin gyaran gyashi to kai maye amfanin ka da bazaka kula da iyalin ka ba?".
Yana sosa 'keye ya ce "uhm Momy baza ki gane bane amma wallahi ba wani son yarinyar nike ba kawai dai zan hakura ne saboda nayi muku biyayya".
Tabe baki Momy tayi kana tace "ina tausayin ka Sadeeq amma kaje kayi duniya ce"
Ba tare da yaji komai aran sa ba ya nufi dinning tebur
Momy ma d'akin ta wuce abin ta saboda Daddy yana gidaZuciyar Sadeeq a cun kushe ya bud'e kular farfesun hanta ya zuba a filet kana yaja kujera ya zauna ya d'auki cokali ya fara cin farfesun amma sai yaji kamar yana cin magani saboda magan ganun da Momy tayi masa basu yi masa dadi ba saboda haka ya bar cin abincin ya ciro wayar sa yad'an shafa screen d'in wayar ya danna number Farooq saida Wayan ta fara ringing sanan ya kara a kunne ringing d'in farko Farooq d'in ya daga yace "officer officer". Muyan Sadeeq a murtuke yace "kayi maganar makarantar yarinyar nan kuwa?".
"d'an iska wai saurin me kake yi haka yaushe garin ya waye".
Sadeeq na jin amsar da Farooq ya bashi yayi saurin katse kiran yana Jan wani dogon tsaki "mtssss".
Adai dai lokacin Siddeeqah ta sauko daga sama tayi fes da ita sanye take cikin shigar doguwar riga 'yar dubai mai ruwan hanta ta yafe kanta da mayafin rigar duk da ba kwalliya tayi ba amma tayi kyau abinka da farar mace mai siririyar fuskar da ke d'auke da dogon hanci gaskiya tayi kyau ko ma'kiyi dole yace masha Allah saboda kama take da larabawaGaban sa ta tsaya tace "yaya na shirya". Wani mugun kallo ya watsa mata gami da cewa "dan uban ki ni sa'an ki ne zaki 'bace min dagani ko saina tashi na yi ball da ke". Kafin Siddeeqah tayi wani yun 'kuri Momy ta fito daga part din ta. Tana Murmushi ta 'karso gurin Siddeeqah ta kama hannun ta ta kalli fiskar ta tayi fayau da ita masha Allah "gaskiya irin wannan kyau haka kamar zaki gasar kyau". Rufe fuskar ta tayi da d'anyan hannun ta ce "Allah Momy banyi kyau ba ko hoda da kwalli ban shafa ba".
"ai gwara da kika bar fuskar ki ahaka sai ainihin kyanki ya dad'a fitowa masha Allah".
Tana Murmushi tace "Momy da gaske ina da kyau?".
"wata ta ta'ba kiran ki da mummuna ne?".
Waiga wa tayi inda yaya Sadeeq yake suka had'a ido ya balla mata harara Momy na lura dasu idan ta fahimci Siddeeqah Sadeeq ne ke ce mata mummuna. Kafadar Siddeeqah ta dafa tace "rabu dashi mai sunan manya kinfi shi kyau nesa ba kusa ba kishi yake dake amma ko makaho ya shafa yasan kin fita daban kama da larabawa kike yi wallahi da za a kwana yana fad'a ma wani ke hausa fulani ce bazai yadda ba har sai kinyi magana yaji muryan ki".
Murmushi ne kwance akan fiskar Siddeeqah tace "Allah yabar mana ke Momyn mu ta bata fek kiss a kumatu".
Kallan sa Momy tayi tace "tashi mana Sadeeq ka kai ta ta shirya kai take jira".
Kamar zaiyi kuka ya ce "yanzu sai a ganni da wannan abar rigi rigi zan kaita gurin gyaran gashi ai abin kunya ne".
Momy na dariya tace "Sadeeq kenan wani lokaci idan kayi wani abu kamar sai ka dawo kamar karamin yaro Siddeeqah ce zaka ce wannar abar? Allah ya shirya ka amma aga ni na ganin ka tare da ita zai 'kara maka girma saboda iyalin ka ce".
YOU ARE READING
NI DA YAYA SADEEQ
Short StoryEvery love story is beautiful but ours is my favourite. Na tsane ki wawuya duk ranar da kika ji ni SADEEQ nace ina son ki kada ki taba yarda dani sbd ba gaskiya bane yaudarar ki zanyi... Kaka kara kaka kada ku bari a baku labari saboda salon na daba...