NI DA YAYA SADEEQ 23

1.2K 90 18
                                    

NI DA YAYA SADEEQ

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Chapter 23

 

   Cigaba da cin abincin nayi ina jin dadi har cikin raina yau zanyi waya da inna, saboda zumudi ban wani koshi ba na mike daga kan dinning din

Momy tace min "ina zuwa?".

Naba ta amsa da "na koshi ne".

Bayan na wanko hannu na falo nazo na zauna ina sake sake a raina

can shima yaya Sadeeq ya zo ya zauna, na kalle shi muka hada ido ya banka min harara nima na rama.

Yace "ke da ni ki ke?".

Nace "nima dani kake?".

Ganin ya taso nasan bugu na zaiyi na mike da gudu na nufi dinning ina kiran sunan Momy, ban kai ga karasa wa ba nayi kicibus da ita, da alamar ta tsorata da yadda nike kwala mata kira tace "ke lafiyan ki?". Murya ta na rawa nike nuna mata Sadeeq da saura kiris ya damko ni Allah ya kawo ta.

Sai a lokacin ta lura a tsaye yake sai mazurai yake na rashin gaskiya.

Momy tace "Sadeeq Sadeeq wai sai yaushe zaka girma? To idan ka dake ta me zaka ji?".

Yace "Allah Momy rashin...".

Cikin sauri Momy ta katse sa da fadin "ban tambayeka ba Sadeeq ba tun yau ba nasan halin ka idan aka bibiya kai ne ka fara".

Daddy ne ya zo gurin da muke yace "kai dai Sadeeq anyi katon banza abin kunya ka tsaya kana biye ma karamar yarinya sai kayi ai tunda kaima irin ta ne baka da hankali, ku wuce mu koma falo".

Ya fad'a yana nuna mana hanya Momy ce ta fara yin gaba Daddy yabi bayan ta, ganin da gani sai yaya na kalle sa karaf muka hada ido ya galla min hara ra madadin na rama sai na kwashe da dariya ina yi mai gwalo nace "anji kunya giwa tana fada da shawo inba ga tsoro ba...".

Ban karasa maganar ba ya damko ni ya toshe min baki ya tsats-tsare ni da idanu yace "ke dan uban ki yaushe zaki hankali dan kinga su Daddy na shigar miki shine zaki min rashin kunya dama na dade ina neman wannan damar gashi yanzu na samu zan ragar gaji bakin yarin ya".

Tuni ido na ya raina fata gashi ya toshe min baki bare na basa hakuri

Ana haka sai ga Daddy ya zo wuce wa ganin Sadeeq matse da baki na yasa shi ma-maki dan takai ci bai ce masa komai ba illa  da yace "bani guri na wuce".

Kunya ce ta kama Sadeeq yana sosa keya ya sake ni kana ya matsa a hanya Daddy ya wuce ni kuwa ina ganin Daddy ya wuce na falla da gudu ina haki kamar wacce tayi gudun fan fa laki

Momy tace "keda wa kuma? A ina ki ka tsaya bayan mun taho?".

Sai da na zauna akan kujerar da ke kallon ta nace "kedai Momy ki bari kawai kuna wuto wa ya damko ni ya shake min yuwa tare da toshe min baki, yanzu haka bacin Allah ya kawo Daddy da kashi na ya bushe".

Momy tace "Sadeeq din?".

Nace "kwarai kuwa".

Zatayi magana kenan ya shigo yana dan so sa keya tace "ka kyauta ka nuna bamu isa da kai ba".

Zai yi magana tace "za kai shuru ko sai na saba maka".

Bai kuma magana ba ya nai mi guri ya zauna,

bai jima da zama ba sai ga Khadija da Ummi nan bayan wasu yan daki ku Daddy ya dawo hannun sa rike da na Umar can sai ga jidda nan ita ma fuskar nan tata a kwabe kollo daya nayi mata na kawar da kaina saboda dariya na so ta kama ni zokai zokai tazo ta zauna a kan kujera.

*  * * * * * * * * *

Aban garen zuby kuwa bayan sun gama sheke ayar su, wanka suka kuma yi a gur guje kana suka fito kasan cewar a kwai taron da suke zuwa duk karshen mako, toro ne da manyan mata yan madugo suke sheke ayar su,

sun shirya tsaf cikin wata doguwar riga yar kanti daga kasan ta a yanke yake haka saman ta shara shara yake kuma hannun bes ne da ita yanayin rigar iri daya ce suka sa, sai dai kowa da kalar tasa,

Wani katon hijabi suka maka akan yar iskar shigan nan tasu dan ko undies basu saka ba kuma dama idan zasu taron ba a saka undies kashe wayoyin su suka yi kana suka daura nikab suka fito lubancy ta rufe kofar ta, alokacin tsakar gidan ba kowa

Sadaf Sadaf suka fice daga gidan dama kafin nan sunyi waya da drivern da yake kaisu duk karshen mako

Sun kuma ci sa'a suna fito wa yana karasowa ba su wani tsaya bata lokaci ba suka hau yaja su,

Bayan doguwar tafiyar da sukayi yayi fakin a dai dai get din wani gida mai girman gaske suka fito yaja motar sa yayi gaba saboda ya saba yana kawo su kuma duk karshen wata suna biyan sa kudin sa dan haka suka tsara dashi,

duk da bai san me suke aikata wa ba amma yana kyauta ta zaton ba alkairi bane,

Saboda tsaro ko mai gadi ma mace ce tsohuwar soja saboda basa son harka da maza sam

Bayan sun kwan kwasa an buda musu suka shiga gida ne mai girman gaske an kawata sa da ado irin na zamani sai da suka wuce gat biyu sannan suka samu inda ake toron mata ne a zaz zaune sun kai su tala tin ko wacce ka gani ba shigar ar zi a tare da ita,

Basu karasa inda matan suke ba sai da suka cire nikab da hijabin, suka tura cikin jaga dama ta kalmi mai tsini zuby ta saka take ta shiga tafiya tana gir giza ba bu abinda bai motsawa a jikin ta, gaba daya hankulan matan ya dawo kan ta a ka shiga tafa mata ana kiran sunan ta ana wasa ta kana ta sami kujera ta zauna lubancy tabiyo bayan ta

Sai da aka fara gabar da abinci suka ci suka sha tare da kayan marmari iri iri da madara bayan sun gama babbar cikin su mai suna Hajiya Turai ta tashi tana kwar kwasa shigar jikin ta bata da maraba da tsira ra

* * * * * * * * *

Please and please
follow
Comment
Vote

NI DA YAYA SADEEQ حيث تعيش القصص. اكتشف الآن