NI DA YAYA SADEEQ
˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙
Page 15
Washe gari da misalin 'karfe 11:00 gaba d'aya mutanen gidan zaune suke akan dining ana breakfast har da Daddy saboda jiya da daddare ya dawo, kasan cewar yau din asab ranar hutu ce babu school a tsanake muke breakfast d'in mu
tunda ya doso gurin 'kamshin turaren sa ya dake hanci na ya bud'e ilahirin gurin da sanyan yan 'kamshin sa d'aga kaina nayi ai kuwa karaf muka yi ido hud'u dashi tsura masa manyan idanuwa na nayi ko kifta su bana yi gaskiya yaya Sadeeq karshen had'uwa ne kansa na fara kallah gashin nan na kansa ya gyara sa sai kyalli yake yi masha Allah sajan nan nasa bakinkirin dashi a gyare gunin ban sha'awa da dan gemun sa da bai wuce kamu daya ba 😜yana sanye cikin wata riga blue mai layi layi hannun ta anyi masa ninki biyu da wani botiri mai kyau da 'kyalli sanye yake da wandon jus lite blue mai kyau da tsada kasan bai kama sa sosai ba ban san sanda na bude baki da hanci ba na cigaba da kallon sa ashe Momy ta lura da ni kawai magana ce bata yimin ba shikuwa gogan da ya 'kara so kan dinning din sai yazo yayi kamar zai wuce ta kusa dani ya take min yatsun kafa ya murza da karfi yayi gaba kamar bashi ne baWata uwar 'kara na kwalla ina yarfe 'yan yatsun hannu na gaba d'ayan su ido suka zuba min da son jin mai ya same ni wasu hawaye ne masu zafi suka fara kwaran yo min saboda naji zafin murje min yatsun 'kafa da yayi "Sadeeq mai kayi mata". Daddy ya fad'a yana duban sa zaman shi kenan akan kujera ya fito da ido waje alamar firgita yace "ni kuma Daddy yanzu fa na iso ko magana banyi mata ba". Jinjina kai Daddy yayi alamar gamsuwa ya waigo ya kalleni yace "mai sunan manya me ya sameki ne?".
Ina shash-shekar kuka nace "yaya ne ya murje mun yatsun kafa na kuma ban san mai nayi masa ba".Gaba dayan su maida kallon su sakayi ga Sadeeq da ya curo waya yake dannawa a hasale Daddy yace "ai kaji abinda tace". Fuskar tausayi yayi ya dube ni yace "yarinya kiji tsoran Allah zaki mutu ki fad'i gaskiy saboda ni kinga da na shigo ma ko kallan ki banyi ba, ko dai aljani ne yayi miki siffa ta ya taka miki 'kafa saboda ace ni ne?".
Ido Siddeeqah ta 'kura mai sai alokacin ta tuna yace yana da aljani idan ko hakane shine ya aljanin ne ya taka ta Allah sarki bai san yayi ba ashe
Kallan ta ta mayar akan Daddy tace "kamar yadda yaya". Yace "ko aljani ne yayi siffar sa inaga hakane saboda wallahi...".
"Ya isa". Jiddah ta fad'a tana wuci kamar wacce aka mata wani abun ta d'ora da cewa "malama kada ki raina mana hankali na dad'e da sanin ke makar ya ciya ce ba tun yau ba saboda kinga Momy da Daddy suna goyan bayan ki sai ki dunga 'kullawa yaya sharri ke ga annamimiya kina shiga tsakanin d'a da uwa wallahi..."
Tau tau! 'karan marin da Siddeeqah ta wanke Jiddah dashi kowa a wurin mamaki yake! banda Sadeeq saboda yafi kowa sanin halin ta shammatar ta ta kuma yi ta dad'a mata wani tas! 💃Gaba daya ji da ganin Jiddah sun tsaya cak sai wasu tau rari da take gani can kuma duhu ya rufe ta
ran Siddeeqah a 'bace ta cukwuikwuyi wuyan rigar Jiddah "wallahi yau koni ko ke sai naji dalilin da yasa ki ka kirani da annamimiya".
Tuni idanunun Jiddah suka furfito waje saboda sha'kar da Siddeeqah tayi mata daman ita ba wata mai 'karfin azo agani bace sai tsinanniyar tsokana da kin ma'kure ta ta koma fuskar tausayi gashi ita kuma Siddeeqah babu hakuri wani lokacin har jira take ka taba ta tayi rashin mutunci yau jin zuciyar ta take asama saboda haka ta fara kaiwa Jiddah naushi a baki tana fad'in "wallahi saikin fad'a min inda na had'a d'a da uwa idan ba haka ba mai...".
"ke sake ta kafin na tashi na 'babballaki". Sadeeq ya fad'a yana nufo inda nike ni kuwa bil ha'k'ki naushin Jiddah nike abaki yanzu haka na fasa mata yana zubar jini
"Kada ka sake ka buge ta zan 'bata maka rai saboda tayi min dai-dai tunda ba da ita ake yi ba ta ara ta yafa yanzu Khadija da Ummi da basu sa baki ba ai ba ayi dasu ba". Momy ce tayi wannan maganar zaiyi magana Daddy yace "nima ai tayi min dai-dai saboda haka ko kallon banza ban yarda kayi mata ba".
Khadija dai bazan ce taji dad'i ba saboda ita bata san fitina kana kallon fuskar ta kasan ba a yanayin jin dad'i take ba Ummi kuwa saboda farin ciki bakin ta ko rufuwa bai yi har kai naushi take kamar ita ke dukan saboda ba wani shiri take yi da Jiddahn ba kasan cewar ta ba 'yar Momy ba yar yayan Momy ce wato kanwar Naseer da ke 'kasar India karatu tun sanda mamar su ta rasu ta dawo gurin Momyn da zama a lokacin tana da 7 year's old kuma ita ma sa'ar su Siddeeqahn ce a ran ta tace "da jiya na biyema Jiddah da da ni za a fara" soboda sanda ta shiga kitchen ta tarar da ita tana hada tea bata tanka mata ba ta hau fad'ar magan ganu kamar yadda ta saba
Umar har yafi Khadija damuwa saboda shi harda guntun hawayen
A lokacin da ya 'kara so inda muke caraf ya d'auke ni daga kan Jiddah zai aje ni Momy tace "a a kasan fad'an Siddeeqah baya 'karewa indai aka taba ta to sai ta rama kaita sama cikin dakin ka idan Jiddahn ta haura sama sai Siddeeqahn ta sauko".
Ina ji ina gani yaya ya haura dani sama ba dan raina yaso ba dan ni da so samu ne a bar ni da ita na koya mata hankali saboda tana da raini da jin kai ni kuma bana jure wa dan ko babba ba 'karamin nauyin sa ni keji ba idan har yaga yayi min ban rama ba
Kamar yadda Momy tace bai dire ni a ko ina ba sa a cikin falon sa ya maida kofar ya rufe da dan mukulli sannan ya zare ya saka a cikin al'jihun sa ya nemi kujera 2 cter ya kwanta ya lumshe ido
Sosoi bakin Jiddah ke zubar jini tuni Daddy ya wuce ban garen sa saboda yadda Jiddahn ke rusa ihu kamar wacce aka aikoma sa'kon mutuwa
Khadija dur 'kushe gaban Jiddah cikin tausaya mata take mata sannu kana daga bisani tace "sannu Little sister zaki iya tashi mu tafi asbiti saboda aduba lafiyar ki?".
Bata gama rufe baki ba Momy ta kara so daga tsaye tace ai daman ance jiki magayi gobe sai ki kara, ke kuma kin zo sai faman sannu kike mata ba ita tajawa kan ta ba? Maza d'auko mayafin ki kije ki" cewa "driver ya tada mota saboda ku kaita ayi mata dressing din bakin ta".
"Wallahi Momy ko da ita ce da laifi bazan iya jure kallon ta cikin wani hali ba na kyale Siddeeka ne kawai saboda itama 'yar uwa ta ce amma baki ji yadda zuciya ta ke mini ba a lokacin da abin ke faruwa".
"Ai fa nan dama ke ki ka fi auki wajen son yan uwan ki nasan ko kanki baki masa san da kike musu abu ne mai kyau amma ina baki shawarar da ki rage saboda kada wata rana ya za me miki matsala".
Idanun Khadija ya kawo 'kwalla ta dubi Momy tace "idan har kuna raye kuna ci gaba da samin albarka bazanyi da na sani akan 'yan uwa ba ba insha Allah ".
"to Allah yasa". Momy ta bata amsa tana barin gurin
Duban Umar Khadija tayi tace "kaje ka cewa Idi driver ya tada mota sannan idan ka dawo ka dakko mini gyale na dana Jiddah".
YOU ARE READING
NI DA YAYA SADEEQ
Short StoryEvery love story is beautiful but ours is my favourite. Na tsane ki wawuya duk ranar da kika ji ni SADEEQ nace ina son ki kada ki taba yarda dani sbd ba gaskiya bane yaudarar ki zanyi... Kaka kara kaka kada ku bari a baku labari saboda salon na daba...