NI DA YAYA SADEEQ
˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙
Chapter 24
Sai faman yauki take kamar kal kashi bata da tsayi kuma tana da dan jiki taci uban bilicin kan wani dakali ta hau tace "madugo". suka ce "mu ne". "madudo".
"Mu ne!".Ta cigaba da cewa "ba tare da bata lokaci ba kamar yadda muka saba ako wani mako yau ma hakan take a matsayi na na shugabar wannan kungiya ina mai kara farin cikin sanar daku yau ma akwai shagali dan mun yi sabon kamu".
Raf Raf Raf suka dunga tafa mata ana ihu
Haka dai masu mukami a cikin kungiyar su kai ta futowa cikin shigar da bata da maraba da tsirara suna bayani kana su koma su zau na
A karshe dai ko wa ya tashi suka yi layi kana wata Hajiya turai tace "bari naje na kira manyan matan su zo su zabe ku dare na yi
ta wata hanya ta bi bata jima ba sai gata da wasu mata datti jawa da ganin su matan manya ne dan fatar su luwai luwai sai sheki take yi suma ba wata suturar arziki suka sa ba, bayan sun iso, Hajiya turai ta ce "to kun dai gansu nan gogag-gu ne a harkar ba abin da basu iya ba ku koma gefe zan dunga kiran su daya bayan daya duk wacce taga wacce tayi mata sai tayi magana amma baza ku zaba su wuce biyar ba".
Take gurin ya kaure da ihu aka hau tafi Raf Raf Raf
* * * * * * * * * *
Daddy yai gyaran murya yace "Alhamdu lillah ina mai kara jad-dada godiya ta ga Allah ma daukakin sarki daya a ramin lokaci domin na kara tuna tar daku dan gane da wasu abububuwa da na lura suna faruwa a gidan nan,
Ya kalli Momy yace "ko kina da abin fada?".
Tace "bani da shi".
Yace "to madallah
yace to kai Sadeeq "Momyn ku tazo min da batun wai ka sama ma Matar ka makarantar kwana haka a kayi?".
Ya karasa maganar yana kallon Sadeeq
Kamar da gaske Sadeeq yace "wallahi Daddy saboda na temaka mata ne, nayi tunani naga idan anan ne ba lallai ta maida hankali tayi karatun kirki ba amma acan idan bata ganin idan wanda ta sani sai ta fi maida hankali".
Cikin gamsuwa da maganar Sadeeq Daddy yace "idan hakane kayi abu mai kyau, yaushe ne, zaka kai ta?".
Yace "gobe ne daddy dan na gama shirya mata komai".
"Ka kyauta Allah yayi albarka haka ake so".
"Ameen ameen Daddy".
Sadeeq ya ceIn banda faduwa ba abin da gabana yake yi sai na rasa me ke min dadi yanzu gobe wannan mugun zai raba ni da farin ciki na sosai nike jin kuna a raina nayi narai narai da ido ban san sanda kalla ta fara zubo min ba
Momy ta kalle ni tace "kiyakuri ki daina kuka ki kaddara tun kafin Allah ya halicce ki ya tsara miki yadda rayuwar ki zata kasan ce, ba kuka zaki ba gode ma Allah zaki da ki ka samu masu tsaya miki akan karatun ki dan wallahi wasu irin wannan damar suke so amma basu samu ba insha Allah zaki ga amfani karatun nan gaba".
Naji dadin nasihar da Momy tai min saboda a rayuwa ta ina son nasiha kuma ina dauka sosai hawaye na na share nace "to Momy insha Allah zan jure".
Daddy ya cigaba da cewa "na dawo kan ku, ke Jiddah".
Ta dago kai ta kalle sa yace "da ke kuma Siddeeqah".bana son tone tone ba tun yau ba ina lura daku a cikin gidan nan bakwa ga maci ji idan nayi magana wa Momyn ku magana sai tace min ba haka ba, amma yan abu buwan da suka dunga faruwa a yan kwana kin nan yasa naji ba bu Daddy kuna yan kana nun ku daku kun iya fada har haka, a gaban mu kenan fa muna da rai, to idan kasa ta lullube fuskar mu ya kenan? Ku saura ra da kyau ku jini bana son na kara ganin irin haka a gidan nan ko naji labari zanyi mummunan saba muku kun ji ni?".
Yai maganar yana kallon mu
Amma sai mukai shiru bamuyi magana ba
yace "ku tashi ku yafi junan ku kuyi ma junan ku sallama saboda Allah ya la'anci mai tada fitina".
Yi mukai kamar ba muji abin da yace mana ba
yaya sadeeq da mun gama kai shi ban go ya taso da zafin sa zai dake mu Daddy yai saurin hana shi
Yace "ka bisu a hankali yara ne nasiha zaka musu yanzu sai suga muna takura musu ne".
Ba dan ran Sadeeq yaso ba ya koma ya zauna
Nasiha daddy ya fara yi mana mai ratsa zuciya yana kara tunatar damu duniyar nan ba komai bace kuma duk mai yanke zumunta ba zai shiga Aljanna ba haka dai yai ta tuna tar damu! jiki na yayi sanyi matuka na gamsu da duk abunda ya fad'a saboda haka na mika ma Jiddah hannu babu yabo ba fallasa ta miko min mukayi musabaha
So sai Daddy yaji dadi dan ya nuna farin cikin sa yai ta samana Albarka
Khadija na zun buro baki tace "wai ni da Umar me mukayi? Daddy baka sa mana Albarka ba".
Murmushi Daddy yai irin nasu na manya kana yace "ai ban ware ba Khadeeja Allah yai muku albarka gabaki dayan ku".
Khadija na Dariya tace "amin Daddy".
Fira muka shiga ta ba wa ina basu labarin kauye ana kwasar dariya can dana tuna banyi waya da inna ba nace "yaya".
Bai dago ya kalle ni ba dan hankalin sa akan waya yake
Momy tace "baka ji ana magana ba?".
Sai alokacin ya dago kai yace "lah wallahi Momy banji ba me tace".
Tace "yo kace bakaji ba taya kasan ita tayi magana? Allah ya shirya ka Sadeeq".
Siddeeqah tace "dama Momy so nike ya kira min Inna".
Yace "Inna tayi bacci yanzu ki bari sai gobe idan Allah ya kaimu kan ki tafi zan kira miki ita ki mata sallama".
Murya ta a dakile nace "to".
Yace "Momy na manta ban fada muku ba nima gobe zan koma kaduna ana nema na a office din mu".
* * * * * * * * *
Dan Allah kuya kuri da jina da kukai shiru kwana biyuKu cigaba da yimin comment da vote please
Kuyi following dina 💞
YOU ARE READING
NI DA YAYA SADEEQ
Short StoryEvery love story is beautiful but ours is my favourite. Na tsane ki wawuya duk ranar da kika ji ni SADEEQ nace ina son ki kada ki taba yarda dani sbd ba gaskiya bane yaudarar ki zanyi... Kaka kara kaka kada ku bari a baku labari saboda salon na daba...