NI DA YAYA SADEEQ
•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•
No editing
Chapter 34
_______bayan wasu shekaru. Zaman aure na nike mai kyau da tsafta da kuma tsantsar so da kulawa da junan mu, alhamdu lillah na kammala secondary school di na , amma ban samu na cigaba ba, saboda yah Sadeeq irin mazajannan ne masu bukatar iyalan su a kusa dasu, kuma yace "mai zanyi da karatu mai zurfi indai zan karanta na rubuta kuma na fadi a fahimta nima idan an fada min na fahimta ai shikenan" .
Mun samu fahimtar juna sosai tsakani na da yah Sadeeq zan iya cewa tundaga ranar da aka kaini har kawo yanzu da nike magana baiyi abunda zai cusguna min da gangan ba, saida bisa rashin sani da kuskure wanda dama dan Adam tara yake bai cika goma ba, yah Sadeeq mutum ne mai saukin kai da tausayin na kasa dashi yanzu haka mun bude gidauniyar da ake temakawa marayu da gajiyayyu. Ya rike mukamai da dama a bangaran aikin sa yanzu haka shine kwamishinan yan sanda na nan jahar kaduna, mun haifi yara yan biyu duka maza shekarun su uku yanzu, Sunan Abba da Daddy aka sa musu, saboda haka muke kiran Abba da Sudais Daddy kuma muke ce mai Taufeeq
Anyi auran Khadija da Yah Mubarak inda suke da yara biyu duka mata, kuma sun koma zama a Dubai, karkashin wani kamfani da suka dauke shi
Sai Ummi da ta auri wani ma'aikacin Jarida, itama ta haifi dan ta namiji
Fadeela kuwa yah Farooq take aure sun haifi yara uku maza biyu mace daya
Sai Jiddah da take auran Maheer wanda sun hadu ne a wajen bikin wata kawar Jiddan yayin da Maheer din shine babban abokin ango sun haifi diya mace
Tsaye muke a filin buga ball din. NI DA YAYA SADEEQ ne sai yaran mu da muke ta guje guje cikin so da kaunar junan mu yah Sadeeq na wurga ma kallon ya cafe da hannu yana dariya ya iso gareni ya shiga raira min wakar "zan rayu da ke zan mutu dake a abadan dani da ke zamu zauna" . ✍️
Comment
Vote
Follow
Share* * * * * * * * * *
Tammat bi hamdulla Alhamdu lillah duka duka anan na kawo karshen littafi na mai suna NI DA YAYA SADEEQ ina rokon Allah ya yafe min abunda na rubuta bisa kuskure wanda kuma nayi dai-dai Allah ya bani lada
Domin yin korafi ko kuma sharhi ko yabawa marubuciyar ko kuma bata shawara za'a iya yin magana da ita ta whatsapp only whatsapp ku TunTuben a wadannan numbobin.
Siddiqahtulkhaireey Yahya
+966591512794
YOU ARE READING
NI DA YAYA SADEEQ
Short StoryEvery love story is beautiful but ours is my favourite. Na tsane ki wawuya duk ranar da kika ji ni SADEEQ nace ina son ki kada ki taba yarda dani sbd ba gaskiya bane yaudarar ki zanyi... Kaka kara kaka kada ku bari a baku labari saboda salon na daba...