NI DA YAYA SADEEQ•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙
No editing
Chapter 30
_____fita sukai suna huci, ni kam raina gabad'aya ya gama baci, Fadeelah nadafa ido na cike da kwalla nace "wai dan Allah a haka kuke rayuwa na fahimci da kiyi laifi da karkiyi duk daya, idan jinin ki bai hadu da su ba sai suyi ta jibgar mutum, ni gaskiya bazan iya dauka ba, haka kawai a gidan mu ba'a dake ni ba sai anan wasu katunan banza su rinka bugu na".
Fadeelah tace "uhm Siddeeqah kenan wannan ma kadan kika gani amma ahankali zaki cigaba da fahimta, kuma kamar yadda kika ce idan fa jinin ki bai hadu da su ba kin shiga uku, musamman ma suga kina da kyau to sai kin fi banuwa, tashi muje kar wasu su zo, su ganmu mu kara laifi".
Mikewa nai zuciya ta babu dadi yau daya ko yinin arziki banyi a makarantar ba duk ta gundure ni.
Muna cikin tafiya muka ji ana kiran Fadeelah da sauri Fadeelah ta waiga dan ganin wacce take kiran ta, aikuwa tai sa'a dan batai mugun gani ba school Momy dinta ta gani, da sauri taja hannu na muka isa gurin ta rungume ta Fadeelah tai tace "Momy Halima wallahi tun jiya nike zuwa room din ku amma sai su senior Dijah su hana ni shiga". Ta karasa maganar cikin yanayi na damuwa
"ke kada ki damu dama naji ajikina kin zo kin barin ki sukai saboda na tambaye su suka dunga yimin hanya-hanya" a cewar Momy Halima
Kallo na tai muka hada ido tace "Fadeelah kenan, ai dama na fada miki dole wataran zaki nemi kawa, gashi ba'a dau wani lokaci ba har kin gaji da yawo ke kadai, amma dai diyar firinciful ce ko dan ga kama nan?" Momy Halima ta kare maganar cikin sigar tambaya
Fadeelah na Murmushi tace "wannan fa sabuwar zuwa ce yau aka kawo ta kuma ba diyar Firinsifal bace amma dai hostel din mu daya kuma sai naji ta kwanta min a rai, yanzu haka kitchen zamu amsar abinci dan su senior Habiba sun rutsa mu a hostel" nai dai ta labarta mata abinda ya faru, cizan dan yatsa Momy Halima tai ta ce " Allah ya saka mata amma ba wani wanki daza kuyi musu ku zo muje room din mu"
Binta mukai muna tafiya tana mana hira sai dariya muke
* * * * * * * * * *
Zaune suke cikin gurin shakatawar, Lubancy ce ta dubi Zuby ta ce "ni kam kawata kin yi waya da Sadeeq kuwa?"
Sai alokacin Zuby ta dago kanta daga danna wayar da take ta ce "a a wallahi nayi ta kiran sa bai dauka ba, banyi tunanin yana da bakar zuciya ba sai da wannan dan abin ya faru".
"kada ki damu nasan bai huce bane amma tunda yana son ki dole idan ya huce zai daga miki kawai dai ki cigaba da kiran sa"
A cewar LubancyKai Zuby ta daga alamun gamsuwa
Suna nan zaune wata matashiyar budurwa tazo wucewa, sanye take da dogon hijab amma bai kai kasa ba kuma fuskar ta sanye take da nikab, ga kuma bakin glass ta sanya, yanayin ta ya nuna kamar tana sauri, saida tazo gab da su Zuby wata leda dake hannun ta ta fad'i, ai kuwa takardun dake cikin ta suka watse, tsugunnawa tai ta fara kwashewa amma sai dai bata gama ba wayar ta ta fara ringing, daga wayar tai ta bar kwashe takar dun ta kuma yi tafiyar ta abun ta.
Gefan kafar Zuby Lubancy ta kalla tace "ke ga wata nan kusan kafar ki".
Zuby ta ce "me?"
Lubancy ta ce "kardun waccan da suka watse dauko mu gani"
Hannu Zuby tasa ta dauko, har zata mikawa Lubancy sai taga kamar rubutu ne aciki sha'awar karantawa taji, saboda haka ta shiga karanta abinda ke ciki kamar haka
"tabbas ranar nadamar ki ta kusan zuwa bama ke ba da duk wasu masu aikata mummunan dabi'a irin taki na rubata wannan sakon ne saboda nasan zai iso gareki".
YOU ARE READING
NI DA YAYA SADEEQ
Short StoryEvery love story is beautiful but ours is my favourite. Na tsane ki wawuya duk ranar da kika ji ni SADEEQ nace ina son ki kada ki taba yarda dani sbd ba gaskiya bane yaudarar ki zanyi... Kaka kara kaka kada ku bari a baku labari saboda salon na daba...