NI DA YAYA SADEEQ
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 11
Bayan mun idar da Sallar isha'i wata firar muka cigaba da yi, idan Khadija tayi nata nima sai nayi nawa hakama Umar, yayin da Jiddah ke faman cika tana batsewa tana jan dogon tsaki, ko ita da wa oho.
yanzu haka Umar ne ke bamu labarin wani Almajiri daya shiga bara gidan wata amarya, sai mijin yace "almajiri kawo kwanon ka". Sai amarya ta leko ta amsa, ta zuba masa abincin, Koda ta miko mai kwano sai ya amsa yatafi zauran gidan yana kuka, sai mijin amaryar yabiyo almajirin, ya tambayesa meye dalilin kukan nasa "ko abincin ne ba zai isheshi ba?". Sai almajiri ya girgiza kai, sai mijin amaryar yace "to meye kake ma kuka?". Budar bakin Almajiri sai cewa yayi "shi ba komai ya sashi wannan kukan ba illah yana tsoran agama aure kyawawan mata kafin lokacin su yai.
" Idan ke/kaine ya zaki/ka yi", haka ya jefe musu tambaya aikuwa nan sukaita tafka muhawara suna shirme
♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Sadeeq kwance a kan gado, wayar shi a hannu yana cikin Instagram, sai kallon hotuna yake, kwatsam idanuwan sa suka sauka akan hotan wata yar budurwa, acikin zuciyar sa yace "daga ganin ta tanada aji kuma ba zaka ce mata 'karamar yarinya ba domin zata iya kaiwa 25 years old da haihuwa". Kara shiga account dinta yayi nan take hotunan ta da take dorawa suka bayyana sosoi Sadeeq ke kallon hotunan, sunan account din ta ya kalla yaga anyi rubuta kamar haka *Zuby officially*"Wow" ya fada afili Suna mai dadi *Zuby* haka yaita maimaitawa bata da wani kyau a fuska, kuma ba wani haske gareta ba, amma dagani ta 'kara da na kanti, 'kirjin ta cike yake da dukiyar Fulani tana da dirin jiki.
♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
*ABUJA*
Ba muyi wata dinner ba, kasancewar bamu dade da cin abincin ba, shayi Momy tasa Suwaiba ta hado mana yaji ni'inal da kayan kamshi, mukai ta kurba kamar wasu larabaw😂
Bayan mun gama kowa ya watse, amma nikam sarkin tsoro d'akin Ummi nayi tana 'ko'karin rufe kofar nai saurin turawa
Da mamaki tace min "sisi yadai". "Anan zan kwana" na fad'a yayin da nike shigowa ciki, ta maida kofar ta rufe♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾♾
Ahaka rayuwa ta cigaba a gidan Momy, tsakanina kuwa da Jiddah babu jituwa, zan iya cewa tun nazo gidan magana bai shiga tsakanin mu ba, kuma babu Wanda ya lura a gidan saboda tun asali kowa yasan bama wani shiri, yau kimanin kwana bakwai kenan da aurena da Sadeeq amma har yau ban sashi a cikin ido naba gashi su Khadija har sun koma makaranta.
Muna falo ni da Momy a zaune, sai Suwaiba dake faman zirga zirga ta kai ta komo tana kokarin hada abincin rana, kafin su Khadija su dawo, "dauko min waya ta a bedroom dina" cikin sauri na mike domin Momy batasan simi simi, bayan na dawo nace "Momy gashi nasamu wayan ma tana ringing". "Kawo mugani waye ya kira" ta amsa tana shafa screen d'in wayar sannan ta kara a kunne
"Wa'alaikumussalam". shi ne abinda naji Momy tace kafin tace "lafiya lau". Ta kara da cewa "wallahi Sadeeq zan cimaka mutunci fiye da yadda kake zato, kasan dai yanzu ba kamar da bane kana da nauyi a kanka, amma kayi burus da mu dama gwada ka nayi naga hankalin ka, to maza maza kazo gobe inason magana da kai na fada maka idan kuwa ba haka ba zanyi mummunan saba maka".Cikin fushi Momy tace "bazan saurare ka ba Sadeeq, baka da abinda zaka fada min na yarda, kaima kasani domin bakada wani uzuri kayi abinda nace maka kawai".
Tana gama fadar haka ta kashe wayar.
Jim kad'an saiga wani kiran ya sake shigowa daga yadda naga Momy ta daga wayar na gane yaya Mubarak ne, d'an yayan ta, na sanshi sosai ya nada mutunci da yana nan ne da zama, amma yanzu yatafi India saboda ya karasa karatun sa a can, kallo na tayi kana tace
"bani ruwa mara sanyi nasha". "To" nace na mike cikin natsuwa koda na dawo har ta kammala wayan.𝐘𝐚𝐮 𝐬𝐡𝐚𝐟𝐢𝐧 𝐛𝐚𝐢𝐲𝐢 𝐭𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐛𝐚 𝐤𝐮𝐲𝐢 𝐡𝐚𝐤𝐮𝐫𝐢 𝐝𝐚𝐬𝐡𝐢 𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐡𝐚𝐫 𝐧𝐚𝐠𝐚 𝐫𝐮𝐰𝐚𝐧 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧 𝐳𝐚𝐧 𝐲𝐢 𝐦𝐮𝐤𝐮 𝐰𝐚𝐧𝐢 𝐚𝐧𝐣𝐢𝐦𝐚 𝐢𝐧𝐬𝐡𝐚 𝐀𝐥𝐥𝐚𝐡
Love you 💖💋💖💋💖
YOU ARE READING
NI DA YAYA SADEEQ
Short StoryEvery love story is beautiful but ours is my favourite. Na tsane ki wawuya duk ranar da kika ji ni SADEEQ nace ina son ki kada ki taba yarda dani sbd ba gaskiya bane yaudarar ki zanyi... Kaka kara kaka kada ku bari a baku labari saboda salon na daba...