NI DA YAYA SADEEQ18

1.3K 89 8
                                    

✨✨✨✨
NI DA YAYA SADEEQ
                      ✨✨✨✨

˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙

Chapter 18

______"haba Momy 'yar wannan abar ce zan fita da ita a matsayin iyali na?".
"Eh Ita d'in fa wallahi Sadeeq ka kiyaye ni ka raina ni ko? Duk abinda nike fad'a maka abanza nike fad'i saboda baka d'auka".
"Momy dan Allah kiyakuri na daina ki ce mata ta wuce mu tafi".
"Au bakin ka ciwo yake da bazaka  fad'a mata ba kai? Ko kafi 'karfi ne? Sadeeq ina raba ka da kiwan kyalla kana shige wa kyallah ta haihu". Momy ta fad'i haka cikin dakiya da tsitstsire sa da ido
Kame kame ya fara

Siddeeqah da taji haka tace "Momy sai mun dawo".

"to adawo lafiya 'yar albarka".

Harabar gidan ta fito  taja ta d'an tsaya kamin yayan nata ya fito su wuce,

adai dai lokacin mlm Habu ya wangele get motar su Jiddah ta silalo ciki idi driver ya samu guri yayi faking kana ya fito ya bude musu murfin motar Khadeeja ce ta fara fitowa sai Umar ya fito saida Khadeeja ta zura kan ta da hannayen ta a cikin motar ta kamo Jiddah da kyar Jiddahn ta iya fito wa tana cicci za le'be saboda yadda take cin zuciyar ta na mata daci da radadi akan dukan da Siddeeqah ta mata ita kadai tasan kalan tana jin cin mutuncin da tayiwa Siddeeqah

kallo daya Siddeeqah ta musu ta kawar da kan ta gefe tana dariya ciki ciki saboda yadda taga bakin Jiddah ya yi sun tumeme
Sadeeq ne ya fito shima ganin Siddeeqah na dariya ita kad'ai abin ya bashi mamaki yana shirin daka mata tsawa sai ya hangi Khadija rike da hannunan Jiddah Umar na biye da su suna taho wa
Kallo na yayi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Ya yi gaba abin sa cikin sauri nima na mara masa baya ba tare da na lura ba naji na ci karo da mutum a tsorace na ja da baya ina yarfe hannu na, ganin Jiddah ce na bige "mttsssss" na ja wani dogon tsaki naga sanda Khadija ta yi mata magana da alamar dai mantuwa tayi a mota saboda naga cikin motar ta koma  Idan jidda yayi 'kwala 'kwala murayan ta na rawa tace "wallahi zaki san kin ta'ba ni yarinya zan nuna miki kalar nawa rashin mutuncin banziya d'iyar shegu ke idan....".
"Tas tas". shine 'karan marin da Sadeeq ya wanke Jiddah da shi yana wuci yace "kada na kara jin kin ce mata shegiya duk lalacewar naka naka ne saboda hannun ka bai ru'bewa ka yan ke ka wurgar ita d'in jinjin ki ce nasan kin San da haka. 'bace min dagani kafin na 'ba'b'ballaki".

Jiddah kusan suman tsaye tayi saboda yadda taji saukar marin batayi zata ba lura Sadeeq yayi da Jiddahn bata cikin hayyacin ta d'an ta'be baki yayi ala mun ko a jinkin sa, kana ya kallo ni nayi sauri nayi 'kasa da kai na zaki wuce mu tafi ko sai na had'a dake munafuka kidinga yin abu sumi sumi to ki kaddara aure na dake... ".

Bai 'karasa maganar ba kira ya shigo a wayar sa laluba aljihun sa yayi ya fiddo batare da ya kalli sunan mai kiran sa ba yayi picking call d'in gami da karawa a kunnen sa sannan yayafito ni da hannu ya yi gaba. Sai a lokacin Khadeeja ta iso kallo na take yi nima da kallon na bita yaya Sadeeq har ya shiga mota nima bu'de gidan baya nayi na shiga na zauna sai Sadeeq d'in ya waigo fuskar sa a murtuke yace "ke uban waye diraiban ki zaki dawo gaba ki zauna ko saina miki tsinannan duka".
"uhm" ta fad'a kana ta dawo gaban motar. Habu mai gadi ya buɗe masa get ya fice daga gidan

Khadija na taba Jiddah tayi luuuuu zata zube a 'kasa cikin hanzari Khadeeja ta mai do ta kirjin ta ta run gume ta mamaki kwance akan fuskar Umar yace "wai aunty Khadija mai yasa meta ni ma yan zu na dawo kina tafiya nima naje gurin Habu mai gadi". Cikin kuka Khadija tace "Umar wannan wace kalar rayuwa ce daga wannan sai wannan gaskiya ni na gaji Zan roki Daddy ya barni na koma kaduna da zama wallahi bana son tashin hankali, nasan ita da Siddeeqah ne ko yaya tunda ina zuwa suka bar gurin". Ta 'karasa fad'a tana rushewa da wani irin kuka mai ban tausayi.

NI DA YAYA SADEEQ Where stories live. Discover now