NI DA YAYA SADEEQ

1.5K 86 5
                                    


NI DA YAYA SADEEQ
                 

بسم الله الرحمن الرحيم      

               Chapter 08

Yanayin tsarin ginin gidan 2 bedroom ne, amma a ko wani ɗaki anyi kofar da mutum zai iya bi ba sai yabi ta falo ba, sai ɗakuna biyu da suke a tsakar gida ɗayan na hanyar waje shine ɗakin yah Sadeeq,sai wanda idan su Momy sun zo suke sauka a ciki, a kwai kitchen a tsakar gidan da bayi,

Inna bata son amfani da kitchen din ɗaki tafi sabawa da na waje.

Amma ni nakan yi amfani dashi idan zanyi jagwal-gwalo na.

Kitchen ɗin na shiga na buɗe dirowar da nasan muna ajiye Indomie, na dauki guda ɗaya. Gas na kunna ruwa na fara tafasawa, kana nazuba Indomie ɗin, sannan nakawo tarugu 1 nasaka nazuba mangyaɗa a ciki ina cikin juyawa, sai ga Khadija taleƙo, cikin zolaya tace "ga yaya Sadeeq can afalo, yace mai kwatar ki yau sai Allah, Inna tayi bacci tun ɗazu, Momy kuma ta tafi ɗaki, daga ni sai Umar ne a falo.

Hantar ciki na ce tafara kaɗawa, jikina yafara rawa na kasa magana, bani da tsoro amma ina tsoran haɗuwa ta da shi, saboda ba da wasa yake min ba, amma duk da haka idan rashin kunya ta, ta tashi ina yimasa

A kiɗime nace "bari na fasa ihu tun kamin yacinmin kinga su Momy za suji su zosu zo su cece ni".

Saka tafin hannaye na nayi na toshe kunnuwa na, saboda inyi ƙarar iya karfi na, zan ƙwallara kenan tayi saurin toshe min baki da tafin hannun ta, tana ƙyalƙyala dariya, Ta ce "naɗauka keɗin jaruma ce, a she ba haka bane, kamar ba kece shekaran jiya kika cemin sai kin rama dukan da ya miki ba, taya zaki rama kina wannan tsoran?".

Sai alokacin nasaki ajiyar zuciya, nabi ta da duka ta fita tana dariya.

koda na duba Indomie na har ta dawu ta fara kamawa, kashe gas nayi, anan kitchen na zauna, a cikin tukunyar naci, inaci ina santi saboda tayi daɗi kuma nayi mata irin dahuwar da nikeso.

Bayan na gama ci, na buɗe baki na sosai na saki wata uwar gyatsa babu ko alhamdu lillah
Na miƙe tsaye nayi  miƙa.

Ɗaki na wuce inda natar da Khadija na sharar baccin ta hankalin ta kwance, kan gadon nima na hau kusa da ita na kwanta ina jina wani iri kamar wani abu zai faru dani.

Washe gari ban farka da asuba ba sai Misalin 8:9am Khadija babu irin tashin da bata yi min da asuba ba, akan nayi sallah amma naƙi, sai ma ƙara gyara kwanciya ta da nayi, Kamar yadda nasaba tashi haka nayi babu ko addu'ar tashi daga bacci, na sauka a kan gadon, brush na ɗauka, ina tatsa makilin ne Khadija ta shigo fiskarta ɗauke da  murmushi, da ganin bakin ta a kwai magana, "au ashe kin tashi daman ke nazo tasa wallahi". Ta faɗa tana matsowa kusa da ni.

"Eh tashi na kenan, wai yanaga kina ta murmushi ne?".

Tace "ba dole ba Daddy fa yazo, shine ma yace na taso ki saboda ya tambaye ni kina ina". Nace kina bacci".

"Amma wannan karon yazo dawuri gaskiya". Nafad ina ajiye makilin ɗin hannu na.

Tace "Eh naji yana cewa Inna da karfe 2:pm jirgin su da zai wuce lagos zai tashi shiyasa yayi sammakon zuwa".

Jin jina kai na nayi, alamar gamsuwa "to bari nayi sallah" nace tare muka futo  ta nufi ɗakin hajiya Inna, ni kuma na nufi rijiya na janyo ruwa, na zuba a bokitin wanka, na kai bayi saida na fara yin wanka sannan na ɗaura al'wala.

Tawul na ɗauro ajiki na, amma irin 'katon nan ne, kuma na wanke kaina babu ko ɗan kwali haka na fito daga cikin bayin.

Adai-dai lokacin yah Sadeeq ya shigo cikin gidan, haɗa ido mukayi, saida ya ƙare min kallo tsaf, sannan yaja dogon tsaki, shasha ya faɗa afili, kana ya wuce ya shiga ciki.

NI DA YAYA SADEEQ Where stories live. Discover now