✨✨✨✨
NI DA YAYA SADEEQ
✨✨✨✨˙·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙
_Ku tsaya ku karanta_
*Amincin Allah ya tabbata a gareku masoya na* _readers musamman na kan wattap daku nike ina fatan ko waccen ku tana cikin koshin lfy ya sanyi to barkanmu da war haka_
_🤙Ni ce dai taku *Siddiqahtul khair y faru* wacce kuka fi sani da *S BEAUTY* a gaskiya bana jin dadin yadda da yawan ku kuke karanta *NOVEL* dina amma ba kwayimin vote da comment uwa uba ma ba kuyi following dina ba gaskiya banji dadi ba ya kamata yadda nike faran ta muku nike nishadantar daku kuma na ilmantar kuma ku faran tamin ta hanyar yimin follow da comment da vote wannan shine ta hanyar da zu biyani domin nima nasamu kwarin gwuiwar da zan dunga yi muku typing a kullum insha Allah saboda inason insha Allah na gama book din kafin mu shiga watan azumin *RAMADAN* saboda akwai program din da zan gabatar muku a cikin azumin insha Allah amma anan wattap kawai saboda haka ku bani had'in kai dan Allah naga canji a wannan karan ngd_
Chapter 20
______Sun d'auki kusan mintuna goma shabiyar a haka batare da d'ayan su ya yi 'kwa'k'kwaran motsi ba sai sautin bugun zuciyar Sadeeq dake sauka fat fat, Siddeeqah kuwa duk da akwai na'urar sanyin dake saka cikin motar sanyi saida ta jike da gumi sharkaf idanuwan ta sun dad'a fitowa waje, dago raunannun idanun sa yayi da suka koma launin gwauta saboda tsabar bacin rai ya sauke su akan na Siddeeqah, da sauri ta maida kanta kasa tana wasa da y'atsun hannun ta zuciyar sa ce take ingiza sa da ya shake mata wuya wata zuciyar kuma ta ce masa "Kul Sadeeq ka kashe gawar da ba taka ba, ka bud'e mata mota ta fita" haka kuwa akai yabi shawarar zuciyar da ta gar gad'e sa soboda haka ya bude mata murfin motar Siddeeqah naji ya bud'e tayi sauri ta bude murfin ta fito har tana neman dungurawa a kasa soboda yanayin Sadeeq d'in yayi mugun bata tsoro da sauri da sauri take tafiya jefa kafar ta kawai take batare da tasan inda take jefewa ta ba, ji tai ta ci karo da mutum a tsorace ta ja da baya ganin Sadeeq ne yabiyo ta d'ayar hanyar da ake iya haduwa da Wanda yabi ta gaban gida, yanda taga yanayin sa har yafi d'azun firgitar wa idanuwan sa sun kara yin jaa kamar Jan gauta, nufo ta ya fara yana d'an Murmushi yana shafa sajen sa, 'kafa mai naci ban baki ba gudu ta fara shima ya mara mata baya cikin ikon Allah saiga Momy a harabar gidan da alamar wani abu take ne ma saboda idanuwan ta a kasa suke, da gudu Siddeeqah taje bayan ta ta 'boye tana nishi "ke lafiyan ki kuwa daga ina haka kamar an koro ki?". Momy ta fad'a tana duban Siddeeqah Bata lura da Sadeeq ba, da hannu Siddeeqah ke nuna mata inda Sadeeq yake sai alokacin Momy ta dube sa, washe baki yai ya wayance yace ma Siddeeqah "ba dai kin ki bari na kama ki ba nima zan rama yarinya, waifa Momy ce mata nayi ta jirani mu taho tare shine ina gama faking ta rigani fitowa shine nabi bayan ta da ta hango ni sai tafara gudu nima shine na biye mata". Siddeeqah kamar sakarya haka ta saki baki da hanci tana kallon shi lallai ya iya tsara labari,
cikin gamsuwa da abinda ya fad'a Momy tace "ai da baka biye mata ba yarinya ce, amma gaskiya kun dade ko ka kaita wani gurin ne? Daddyn ku na ta kiran ka a waya baka dauka munyi tunanin ko ba lafiya ba hankali ya fara tashi".
"Wallahi lafiya lau Momy layi muka tarar a gurin saloon d'in, amma me ya fito dake naga kamar wani abu kike nema?"."to babu damuwa, eh wallahi d'an kunnen Jiddah ne guda daya ya fad'i sanda suka dawo daga asbiti".
Tace "anan ya fad'i shine nace bari na duba ko zan gani".
"haba Momy ke da kanki ina sauran yaran gidan?".
"Suna ciki Khadija ta ce ta gaji zata shiga ta huta dan ko abincin rana bata ci ba, Umar kuma yana tare da Jiddah, Ummi kuma tun safe ban kuma ganin ta ba".
"Kibar neman haka Momy muje ciki ba rabon ta bane kawai sai asai mata wani".
"dama a cikin irin tsara bar da auntyn kaduna ta kawo musu ne alokacin da ta dawo daga India daham ne yanada tsada sosai yanzu ita kadai ce ba ta da".
YOU ARE READING
NI DA YAYA SADEEQ
Short StoryEvery love story is beautiful but ours is my favourite. Na tsane ki wawuya duk ranar da kika ji ni SADEEQ nace ina son ki kada ki taba yarda dani sbd ba gaskiya bane yaudarar ki zanyi... Kaka kara kaka kada ku bari a baku labari saboda salon na daba...