NI DA YAYA SADEEQ
Ramadan kareem✨ 🌙
Ramadan kareem ✨🌙
Ramadan kareem ✨🌙Ina fatan kowa yana cikin koshin lfy ya Azumi
Allah ya karbu ibadun mu 🙏Please dan Allah a daure ayi min
comment
Da
voteAlfar Mar wannan wata da muke ciki na Ramadan ayi following dina 🙏😎
* * * * * * *
·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙
Chapter 26
___Ya dauki tsayin lokaci a haka yana kallon tsala tsala cinyo yin nata, daka bisani ya mike yana mai jin haushin kansa ko me yagani a jikin wannan kwailar yarinyar? Haka ya tambayi kanshi ganin bashida amsa yaja dogon tsaki duk abinda Sadeeq yake yi Siddeeqah bata san inda kanta yake ba saboda tana da nauyin bacci
Izuwa lokacin cikin nasa yai masa sauki sosai sai dan abinda ba a rasa ba
Dukan kafar ta ya shiga yi kamar a mafarki taji ana bugun ta a tsorace ta bude ido ganin Sadeeq ne yasa ta dan ji sanyi a ranta
Dube dube ta fara sai alokacin ta tuna ashe a falo ta kwana ta dirowa tayi daga kan kujerar ta wangale baki tayi hamma Sadeeq harda toshe hanci yayi saboda da tayi hammar bata kare bakin ta ba wai kada yaji wari, tayi mamakin ganin sa amma sai bata nuna nasa ba ta bige da cewa "wash".
A yatsine Sadeeq ya dube ta wallahi shi har cikin zuciyar sa ya tsane ta mtwssss ya kuma Jan tsaki a karo na biyu, afili yace "wallahi Daddy bai kyauta min ba daya aura min yarinyar nan"
Duban sa itama tayi tace "aikin banza wai harara a duhu".
Bata karasa fada a gaban sa ba ta ruga da gudu saboda tasan duka ne zai biyo baya ta ko yi sa'a dakin Ummin abude yake tana fadawa ta maida kofar ta rufe kana ta fara maida numfashi daka bisani tabi lafiyar gado
Da takaicin ta Sadeeq ya mike
Ko kadan babu laka a jikin sa ahankali ya ke tafiya har ya haura sama ya shiga makwancin sa*** * * * * * * * *
Bayan ta gama gyara bra dinta ta dubi Badyy tace "dan zuge min zif din". Da "to". Badyy ta amsa kana ta zuge mata kamar yadda ta bukata.
Basu jima ba sai ga lubancy ta zo tana ganin Zuby tare da Baddypp tayi kicin-kicin da rai, sarai Zuby ta gane nufin Lubancy amma sai ta basar tace "yauwa dama tun dazu ke nike jira muje ko".
Ba tare da Lubancy ta tanka mata ba tayi gaba asakarce Zuby ta bi bayan Lubancy da kallo kana ta maida kallon ta ga Badyy tace "am mata mu mun tafi sai idan mun hadu wani satin".
Badyy ta ce "to".
Koda suka fito bakin get din sun tarar da Zuly na jiransu amoto saboda haka basu wani tsaya bata lokaci ba suka shiga Zuly tajasu suka dau hanya
Tafiya suke babu mai kula dan uwan sa Zuby aka fara saukewa saboda unguwar tasu tafi kusa kana tayi musu sallama ko da tazo bakin get din ta rasa ya zatayi saboda tasan mai gadi yanzu bacci yake yi, can ta sauke ajiyar zuciya da sauri ta fiddo wayar ta daga cikin jakar ta number Mama ta shiga laluba Mama dake safa da marwa a dakin ta taji ringing din wayar ta da sauri taje ta dauko kana ta duba screen d'in saboda taga wace me neman nata
Ganin sunan shalele na yawo akai yasa Mama tai saurin dagawa gami da karawa a kunnen ta daga can bangaren Zuby tace "Mama a bude min kofa". Daga haka ta kashe wayar bata dade ba sai ga Maman tazo ta bude mata, tana shiga Mama ta maida get din ta tura ahankali Zuby zatai magana Mama tai sauri ta tashe mata baki tun kan su karasa falon Zuby ta cire nikabin fuskar ta cikin sanda suka wuce falon basu zarce ko ina ba sai dakin Zuby kana Mama ta maida kofa ta rufe Masifa mama ta shiga zazzagawa inda sabo Zuby ta saba saboda indai Abba nanan to fa haka Mama ke yi sai da ta gama kana Zuby ta dubi Mama tace "haba Mama wai meyisa ki ke min irin wannan ne? Ni gaskiya bana so ki sani a gaba ki tai min masifa sai kace yarinya karama".
أنت تقرأ
NI DA YAYA SADEEQ
القصة القصيرةEvery love story is beautiful but ours is my favourite. Na tsane ki wawuya duk ranar da kika ji ni SADEEQ nace ina son ki kada ki taba yarda dani sbd ba gaskiya bane yaudarar ki zanyi... Kaka kara kaka kada ku bari a baku labari saboda salon na daba...