NI DA YAYA SADEEQ
TUNATAR WA
Du'aah
Bakyada Miji ?👈🤴
To Allah Ya baki Miji nagari Alfarman wannan watan🤲aurenki bayan Sallah ne?👈👸
To Allah ya baewa Iyayenki abunda za ayi auren Alfarman wannan watan🤲Kinyi aure ?👈🧕
To Allah ya baku zaman lafiya da kwanciyar hankali ke da mijinki Alfarman wannan watan
🤲Bakya haehuwa? 👈😥
To Allah ya baki haehuwa da 'yaya masu Albarka Alfarman wannan watan🤲Ciki ne dake ? 👈🤰
To Allah ya sauke ki lafiya musha biki Alfarman wannan watan🤲Kin Haehu ?👈🤱
To Allah ya bar maki 'yayanki ya sa masu Albarka Alfarman
wannan watan🤲Kina samun sa6ani da mijinki? 👈😫
To Allah ya dae dae ta atsakanin Ku ya sa Ku fahimce junan Ku ya kuma qara gam din soyayya har qarshin rayuwar ku Alfarman wannan watan 🤲Kina da masifaffiyar kishiya ? 👈😳
To Allah ya hada hankulanku Alfarman wannan watan 🤲Kinada masifaffiyar Uwar miji ?👈🙄
To Allah ya azirtata da kamuwa da sonki taji dk duniya bata kaunar kowa sae ke Alfarman wannan watan 🤲Kinada damuwa ?👈😩
To Allah yaye maki wannan damuwar Izuwa Farinciki har qarshen rayuwarki Alfarman wannan watan🤲Iyayenki suna raye ?👈🧑🦳👨🦳
To Allah yasa su cika da Imani yasa Ku rabu da juna lafiya Alfarman wannan watan🤲Mahaefiyar ki ba lafiya ?👈😩
To Allah ya bata lafiya da nisan kwana Alfarman wannan watan🤲Mahaefinki ba lafiya? 😩
To Allah ya bashi lafiya da nisan kwana Alfarman wannan watan🤲Mahaefanki basa raye? 👈😥
To Allah yaji qansu da rahma yasa Aljannah ce makomarsu ke kuma Allah ya baki hakurin rashinsu Alfarman wannan watan 🤲
Kinajin azimin yau ?👈🤣
To Allah ya baki hakuri da juriya ya kuma kar6e Ibadan ki Alfarman wannan watan🤲Kinji dadin wannan addua?👈🙏
To Allah ya farantamin nima kaman yanda na farantawa Aunties dina Alfarman wannan watan🤲👈Ina rokon ka ya Allah dan tsarkin mulkin ka duk wacce ta dauki hannun ta mai Albarka tayi/yayi
Following #dina
Tayi /yayi #commen
Ku kai min #vote
Da fatan duk munyi Sallah lafiya Allah ya maimaita mana 🙏🌙
* * * * * * * *
·٠•●♥ بسم الله الرحمن الرحيم ♥●•٠·˙
CHAPTER 27
"lafiya naga duk kin rasa nutsuwar ki lokaci guda ko wata maganar Abban ya fad'a miki?".
Mama ta tambayi Zuby dake faman safa da marwa a falo dayan hannun ta dafe da goshin ta saboda jirin da take gani.Cikin sauri Zuby ta juyo ta kalli Mama tace "ina lafiya Mama wallahi ni mutuwa zanyi bana son Maheer Mama ki taimaka min idan Abba yace sai na aure sa mutuwa zan yi".
A dai dai lakacin Abba ya fito daga bedroom din sa da jaka trolley a hannu sa yana ja yar karama, da alamar tafiya zai yi, yaji duka abinda Zubaidan ta fada ransa na suya yace "aikuwa sai dai ki mutu amma ko gawar ki ce sai an kaita gidan Maheer zan can banza zan can hofi, duk laifin ki ne Mariya" ya fad'a yana maida duban sa gare ta "ke kika bata yarinyar nan amma gabaki dayan ku zanyi maganin ku bari na dawo tafiya, kuma kufara shirye shiryen biki daga yanzu zuwa kowani lokaci za'a daura aure". Yana gama fadar haka ya fice abun sa,
Maganar da yayi da Usman jiya ta kara dawo mai sabuwa fil yaji kamar yanzu ake fada masa ita, take zuciyar sa ta fara kuna da radadi tabbas ka haifi d'a ne amma baka haifi halin sa ba idan kuwa hakane Mariya ta dade tana raina masa hankali amma ya godewa Allah da jiya Usman ya ganar dashi, shi dama ya dade yana zargin da akwai abinda suke boye masa ya bari ne saboda yasan dole wataran asirin su zai tonu, ya kuduri aniyar sa ido sosai akan ta saboda yagano abinda take aikata wa, aran sa yace "ya tabbata Mariya ce ta Lalata yarinyar saboda duk wani abu da take yi da sanin ta take aikatawa tabbas idan ya gono ba abun arziki bane kashin Mariya ya bushe dan san da zai bata Zubaidan tayi alkawarin bata tarbiya kamar diyar da ta haifa ta cikin ta da haka ya kawar da tunanin ya shiga cikin mota ya bata wuta.
YOU ARE READING
NI DA YAYA SADEEQ
Short StoryEvery love story is beautiful but ours is my favourite. Na tsane ki wawuya duk ranar da kika ji ni SADEEQ nace ina son ki kada ki taba yarda dani sbd ba gaskiya bane yaudarar ki zanyi... Kaka kara kaka kada ku bari a baku labari saboda salon na daba...