NI DA YAYA SADEEQ
Love story 2021 typing free book
Na
Siddiqahtulkhaireey Yahya (Sbeauty)EWF📚💪
TSOKACIDa sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, ban ƙirƙiri littafin NI DA YAYA SADEEQ saboda wani ko wata ba, nayi ne saboda nishadantar da Al'umma gami da faɗakar da su, kuma wannan shine littafina na farko fatan zakuyi hakuri da kura kuran da zaku ci karo da su.
SADAUKARWA
Wannan littafin sukutum ɗin sa, sadaukarwa ne ga mahaifiya ta. Hajiya Rukayya Muhammad (kamfani)
_________________________________
Shafi na farkoبسم الله الرحمن الرحيم
_______A zaune nike a kan tabarma cikin baranda, isaka na kaɗa bishiyar mangwaron da ke tsakiyar gidan mu, ganyen ta na faɗowa ƙasa gunin burgewa, dambu ne a gabana cikin wata y'ar samira inaci ina suɗe yatsun hannu na, saboda dambun yayi min daɗi kamar kar ya ƙare.
Ƙawata Ladiyo ce ta shigo gidan mu hannunun ta rike da goshin ta yana zubar da jini, koda na ɗaga kaina na kalle ta bance mata uffan ba, illah maida kaina ƙasa da nai na cigaba da cin dambu na, sai da na cinye dambun tas sannan na kora da ruwa, kana na buɗe baki na iya ƙarfi na nayi wata ƙatuwar gyatsa, wacce da gani kasan tarashin mutunci ce, irin wacce idan yaya Sadeeƙ yana guri nayi yake buge min baki.
Kallan Ladiyo nayi na taɓe baki na ce "Ladiyo wai lafiya kika zo ki ka tsaya min a kai? Ko aiko akayi?".
Ladiyo da dama jira take in tambaye ta, saboda tasan in bani na tambayeta ba tana iya faɗa min na gwasale ta, tana kuka take faɗan abinda ya faru cewa "ina yaron da jiya muka barar mai da markaɗe?".
"Eh na tuna shi me yafaru?".
"Yanzu haka daga aken da Ummata tai min gidan su Zulai anso mata kuɗin zubin a dashi nike, bayan na anso kuɗin, kan hanya ta ta dawowa na haɗu da yaron, wai ashe nan ne layin su, shine yai tamin ruwan duwatsu tako ina, har wasu abokan sa da suka gani suka taya sa, Allah ya taimake ni baban
Ramma yazo wucewa, shine da yaga abinda ke faruwa, ya tsawatar musu, shine suka ƙyale ni, amma wallahi inaga da sai dai a ɗauko gawa ta saboda jifan da suka min bana wasa bane, ko gida banje ba nayo nan saboda ya bani saƙo gunki cewa, idon ki idon shi sai ya fasa miki goshi"."Kan uban nan, yanzu dama acikin ƙauyen nan a kwai wanda zaija dani, har ma yace zai fasa min goshi, to ƙaryarsa taci ƙarya, wallahi kaf ƙauyen Dande banga mai tara ta gaba da gaba ba, kin san dai ko ta baya sai an shirya, to amma tunda yace haka muzuba ni dashi, shege ka fasa, ɗan halak sai yanka, kafin ya fasa min ni zan fara zuwa gidan su in fasa na Babar sa inya so kinga yaji daɗin fasa min nawa da hujja".
Inna da fitowar ta daga ban ɗaki kenan da buta a hannun ta, bayan ta aje butar ta ce "wai ke da wa siddeeƙah? Kike mulmulo irin wannan ashar ɗin, kamar bakya zuwa islamiya"? .
Cikin sakalci na ce "yo Inna bakiga Ladiyo bane?".
Sai alokacin Inna ta lura da Ladiyo da ke a tsaye gindin rijiya hannun ta ɗore bisa goshin ta.
"Na ganta sai akai yaya"?.
Cikin ƙosawa da tambayar da take min na ce "yo wai ke Inna bakiga goshin ta bane a fashe jini yana zuba?".
"Na gani man, ai tunda taƙi rabuwa dake, tana tare da wahala, gashi ta zama lusara bata iya taɓuka komai, amma tsokana fal cikin ta, tsokana kuwa tamai ƙarfi ce".
Na ce "yo Inna wanda yafasa mata goshin ne nima yace ace min ido na idon shi sai ya fasa min, shine abin yabani dariya da takaici har kika ji nayi wannan ashar ɗin, kuma wallahi idan duka ƙauyen nan gatan shi ne wallahi sai naci ubansa, duk abinda zai faru ya daɗe bai faru ba, be san wace ce Siddeeƙar Inna bane shiyasa, amma ko yaran goye aka amaba ta masa suna na, nan take jikin sa yake fara rawa saboda karo dani babu daɗi".
Banyi aune ba naji anbige min baki, a masifance na ɗago da kaina dan naga wani mai tsaurin idon ne, da har ina magana zai bigen baki.
Diriricewa nai, ganin shi a gaba na nasan ko ba a faɗa ba shine ya bigen baki, ɗan ƙaramin baki na na zumɓuro. Yayin da muka haɗa ido ya wani kashe min idon sa ɗaya. Yana cewa "shegiya mai zubin aljanu, bari na fara cin naki uban, kamin shi yaci nasa, shashasha kawai, naga ƙafar ki a waje kiga yadda zanyi da ke, sakarya daƙiƙiya kawai, ba arabi ba boko, sai yawan gaɗa a dandali, ke fa ko a cikin matan ƙauyen kin fita zakka, saboda kinfi su wauta da tumasanci, saboda kin ga Inna na ɗaure miki gindi kina yin abinda kika ga dama, kina ganin kamar gata take miki, to ki sani Inna ta riga da ta gama cin kasuwar ta, ke kuma yanzu kike fara tasowa. Saboda baki san komai game da rayuwa ba, kwata-kwata ma nawa kike? ko 14 years old baki kaiba amma kin addabi mutanan gari, kullum ana cikin kawo ƙarar ki muna bada haƙuri".
Ladiyo dake tsaye har yanzu kamar wacce aka dasa ya kalla, irin kallon nan na gargaɗi kana ya ce "ke yama kike da suna?".
Ladiyo dake a tsaye hannun ta akan goshinta, cikin rawar baki da rikicewa ta ce "Ladiyo".
"Oho koma dai maye sunan naki maza ki bi nan". yai mata nuni da hanyar fita gidan."
Ya kuma cewa "ko a ƙofar gidan nan idan kika bari na kuma ganin ki, to ko na lahira sai yafiki jin daɗi, bare kuma in ga wa'innan y'an ƙafafuwan naki a cikin gidan nan, Allah sai na ɓaɓɓallaki".
A kausashe ya ce "Ina fatan kinji abinda nace miki? idan kunne yaji gangar jiki ta tsira. "Oya maza ɓace min da gani, kamin nayi ball da ke".
Ladiyo jiki na 'bari ta bar gidan mu, a ɗari da hamsin.
Kallo na yayi muka haɗa ido ya wurgo min harara, ramawa nima nayi, gami da haɗawa da ƙunƙuni ciki-ciki na ce "nima fa idon nan ba fina akai ba, da har ake wani min barazana da su, kuma mu zuba ni da kai, zaka san ka bige min baki".
"ke! Me kike cewa?".
Sai alokacin Inna tai magana, saboda tasan ɗazun ko tayi ba mai sauraron ta, ta ce "haba Garba,
waini me yarinyar nan taimaka ne daka tsaneta? ba nason haka fa, tun ba yau ba nasha faɗa maka, amma dake ka rainani bakajin magana ta, ko kaɗan saboda kaga ni kaka ce, to alhaji ƙaramin zai zo ai, tunda watan ya kusan ƙarewa, idan kai ban isa da kai ba shi na isa dashi. Kuma shine mahaifin ka, idan yafaɗa maka wataƙil kaji nasa tunda ni kaƙi jin nawa".Ya san halin Inna sarai da mita, dan haka sai ya kawo wasa a maganar ya ce "haba hajjaju makkatun mu karrama, ranki shidaɗe, ki daɗe kiyi ƙarko, kiyi shekarun bishiyar dabino, wane ni ai ban isa in raina ki ba, duk da cewa nike aurenki amma ke ke bada umarnin, Kuma yadda Kiki ce hakan ake yi, ina mai tabbatar miki bani kuma shiga shirgin ta daga yau".
washe baki Inna tai, cikin jin daɗin furucin shi ta ce " ko kaifa Garba shikenan ya wuce amma da kasa ka y'ar mutane gaba sai ramewa take, shiga ciki yanxu zansa ta kawo maka abincin naka.
💋💋💋💋💋💋
_Kar ku manta kuyi_Comment
Shear
Vote_I love you all_
💋💋💋💋💋💋
*S BEAUTY CE ✍️*
ČTEŠ
NI DA YAYA SADEEQ
PovídkyEvery love story is beautiful but ours is my favourite. Na tsane ki wawuya duk ranar da kika ji ni SADEEQ nace ina son ki kada ki taba yarda dani sbd ba gaskiya bane yaudarar ki zanyi... Kaka kara kaka kada ku bari a baku labari saboda salon na daba...