NI DA YAYA SADEEQ

2.5K 128 12
                                    

NI DA YAYA SADEEQ
                  

               Na
Siddiqahtulkhaireey Yahya (S beauty ✍️)
             
                 EWF📚✍️
__________________________________
             
  *Page 03*

بسم الله الرحمن الرحيم

            
Asbitin gabaɗayan sa a lalace yake, saboda ginin jar ƙasa ne, wani ɓangaren ma duk ya rushe, ɗakunan  da ake kwantar da marasa lafiya guda 4 ne kawai, Sai office 1 da ma'aikatan asbitin suke zama a ciki, gabaki ɗaya asbitin gado biyu ne.

A bakin asbitin yayi faking, Asbitin bashida kofar shiga ko ta ina shiga a ke saboda ba a kewaye yake ba, ya ɗauki kusan  seconds goma a cikin motar, kamin ya kashe ya fito,
sai da ya fara buɗewa Inna ta fito, kana ya buɗe bangaren da nike yaɗan zuro jikin sa ciki ya miƙo hannu ya janyo ni, Inna  faɗi take "kabita a hankali ba cikakkiyar lafiya gare ta ba".
Ɗauka ta yayi irin ɗaukar da a kewa jarirai, kana ya nufi asbitin,
Inna biye da mu a baya.

Da yike yah sadeeq sananne ne a gari bama iyaka kauyen mu kaɗai ba harda birni, saboda babban ɗan sanda ne.

Wata nurse ce ta  hangomu da sauri ta ƙaraso inda muke, cikin rawar jiki tace "yallaɓai cikin wancen ɗakin zaka kaita zatafi hutawa, babu mutane da yawa a cikin sa". Tafaɗa haka tana nuna mai ɗakin da yatsan ta manuniya, "alright" shine abin da kawai ya faɗa.

Ɗakin da a kace ya kai ni shine ɗakin da ake ji dashi a cikin asbitin, saboda a kwai siminti da gado guda ɗaya tak, mun tarar da mara lafiya a kan gadon  kwance, saboda ya ɗora ni aka sauke mara lafiyar gunin ban tausayi, gashi masu jinyar ta basa kusa.

"yallaɓai ɗora ta a kai". A cewar nurse ɗin data sa aka sauke mara lafiyar.

Be yi mamaki ba, saboda ya saba kawo ni asbitin, kuma irin haka ne take faruwa.

Ɗora ni yayi akan godon, kana ya fice abin sa.

Da sauri Nurse ɗin tabi bayan shi tare da wa'inda suka cicciɓi marar lafiyar da aka sauke a kan gado.

Bai jima ba saiga shi ya dawo tare da  wata nurse, hannun  ta rike da wani ɗan karamin farantin silba, sai kyalli yake, kan wani teburi na katako ta ijiye, sannan ta matso kusa dani, ta ɗora hannun ta a kan wuya na, "a kwai zafi a jikin ta yallaɓai, zazzaɓi ne ya kamata". Nurse tafaɗa tana duban shi, kin tanka mata yai, dan kuwa kunnan uwar shegu yai mata.

"Meke damun ki?". Nurse ta tambaye ni,

"Duka jiki na ciwo yake min, amma kirji na yafimin ciwo".

Fuska ta ta kalla da kyau sai taga shatun hannu tace "kamar dukan ki akayi ko, domin shaidar hannu ya bayyana a kan kuncin ki raɗa-raɗa".

Na buɗe baki zanyi  magana kenan yah sadeeq ya wurga min harara.

Kallon nurse ɗin yai  ya ce "ke maye aikin ki?".

"Duba mara lafiya". Ta faɗa bakin ta na rawa.

saida ya ɗaure fuskar sa babu alamun wasa a tat-tare da shi yace "to kiyi aikin ki, dan wannan bai shafeki ba, kiyi abinda ya dace".

Cikin in-ina ta ce "to ranka shidaɗe na tambaya ne saboda nasan irin maganin daya dace na bata, amma kaya ƙuri naga kamar ranka ya ɓaci".

Be kuma bi ta kanta ba yafi ce daka ɗakin, tasha fama dani sosai kamin na bari tasoka min allurar da za ai ƙarin ruwa, shima saboda naga yah sadeeq ya dawo ɗakin ne.

Banfi minti 25 da samin ruwan ba, baccin wahala ya ɗauke ni, koda na farka bayan wasu awanni da bazu wuce 2 ba, sai naga momy zaune a kan wata farar kujera, irin tarobar nan, da alama daka gida aka zo da kujerar ma, mamakin ganin ta ne ya kamani,  miƙewa nai zaune na jingina filo a baya na, kallon ta nikeyi ina muts-tsuka idanu, ban gama mamaki ba saida naga  Khadija, tashigo ɗakin hannun ta ɗauke da kular abinci, da kwano, Umar, na biye da ita a baya.

NI DA YAYA SADEEQ حيث تعيش القصص. اكتشف الآن