Page 11

2 0 0
                                    


"Kar ka kuskura ka raina min miji wallahi! Don zan yi maka mugun rashin mutumci da ban taɓa yi wa wani kalarsa ba! Soyayya ce dai na ce ba na yi, ba ni sonka Nura nake so saboda shi ne farincikina, shi nake so! kuma zan shi so! sannan zan ci gaba da so har ƙarshen rayuwata." Ta ida maganar tana huci kamar wacce take shirin yin dambe da shi, shi dariya ta ba shi saboda yadda take kalahuttai tsakaninta da Allah saboda ya ambaci sunan saurayinta haɗe da Kiransa da yaro shi ne take yi masa masifa. Sai ya ce da ita
"Au nufinki ƙarya na yi? Ko ba yaron ba ne? Tun yanzu ma ki fita a harkarsa ki koya wa kanki sona, kodayake ma ga sona nan ina gani a cikin idanuwanki kawai dai...."
"Ashe kuwa kana yaudarar kanka wallahi in har kana tunanin ina sonka. Ashe ba ka ji me na ce ba kenan! Bara in maimata maka na ji. Na ce ba ni sonka ka fita a rayuwata, ba zan taɓa sonka kuma wannan ka rubuta ka aje." Ta katse sa da wanñan maganar wacce ba ta ba shi damar karasa maganarsa ba.
"Ni kuma na yi maki alƙawarin ke da kanki za ki furta kalmar ina sonka Ibrahim, ke da kanki za ki furta kalmar ba za ki taɓa iya rayuwa ba tare da ni ba yarinya, don haka cika baki ba naki ba ne don ba a san inda rana take faɗuwa ba." Cewar Ibrahim yana shiga motarsa amma bai rufe ba. don wannan ƴar hayaniyar har ta fara saka masa ciwon kai, sai ya tsinkayi muryarta tana cewa
"Ai kullum rana yamma take faɗuwa.  Don Allah me ya sa ba ka da tausayi ko kadan ne? Me ya sa kake neman tarwatsa soyayya da farincikin masoya? Me ya sa kake son rushe ginin da saura kaɗan mu karasa shi? Me ya sa ba za ka je ka nemi wata ba ka aura sai ni? In tambaya ka don Allah? Ni kaɗai ce mace a duniyar ko kuma ni kaɗai ce wacce kake son ganin bayana farincikina?"
"Saboda ke ce kika shigo gonata har kika min satar zuciya!" Ya ba ta amsar tambayarta ta karshe a taikace ba tare  amsa sauran tambayarsa ta farko ba.

Sai ta koma yi masa roko don dai ita har ga Allah ba ta iya masifa ba wannan ma da ta yi masa karfin hali ne kawai don ya rabu da ita.
"Don Allah ka yi haƙuri ka koya wa zuciyarka haƙuri da ni, hakan shi ne kawai mafita a gare mu, amma in har ka matse mani rayukka da yawa za su shiga cikin matsala wallahi, hatta iyayenmu sai abun ya shafe su, don haka nake sake rokonka da ka yi haƙuri da ni, wallahi zan iya nema maka mata in har kana so ina da ƙawaye da yawa zan iya haɗa ka da su."
In ji Lalla ta ida maganar kamar mai neman gafararsa saboda yadda ta marairaice masa kamar ba ita ce ta gama yi masa masifa ba.
"Ba ki yi min aldaci ba gaskiya!"
Cewar Ibrahim
"Wannan shi ne adalcin kawai." In ji Hafsat cikin sauri, don gani take yi ya sauko saboda yadda ya yi magana tana ga alamar zai hakura da ita. Amma a mamakinta sai ta ji yana cewa
"A wajenki yake adalci, amma ni a wajena ba adalci ba ne, ta ya ya za ki saci zuciyata kuma sannan ki ce in fita daga rayuwarki!" 
Ibrahim ya yi maganr yana kallonta ido cikin ido, kasa jurewa ta yi da kallon da yake yi mata sai ta ce
"Shi ne adalcin kuwa, na dai faɗa maka ka yi zan zaɓar maka mata"
"Ba ni buƙatar kowacce mace a cikin duniyata face ke, don haka ke na fara so kuma ke zan ci gaba da so, ko da kuwa sonki zai zama ajalina." Ibrahim ya yi maganar ba tare da ya kalle ta ba, sannan ya ƙara magana yana cewa
"Gobe in sha Allah zan koma a bakin aikina, ki kula min da kanki sai in na dawo in aurenmu ya tashi, ina yi maki fatan alƙairi my wife"
Ya idasa maganar yana shigewa motarsa haɗe da ba ta wuta, ya yi gaba abun sa don in har ya tsaya jin abin da za ta ce ba za a yi mai kyau ba, da kallo ta bi shi tana mamakin rashin zuciya irin nasa, duk gargadin da take yi masa amma burinsa dai ta zama matarsa, kai ina amfanin wata masifa da jaraba irin ta kalar masu Nacin tsiya irin su Ibrahim.

Maimakon ta koma cikin gidansu sai ta wuce gidan su Fati duk da ba ta tunanin Fati tana gida saboda yau ranar aiki ce, amma dai gara ta je can ɗin har ta dawo saboda neman shawararta game da Ibrahim don ta gaji da wannan halin nasa, duk ta fi ganin laifi Fati a wannan harkar don ita ce ta fara ba shi lambarta har yake sha wa rayuwarta kai, don haka ita ce za ta ba ta shawarar yadda za ta daina kula shi don ta ga ya fiye nacin jaraba kuma bai jin gargadi ga rashin zuciya da babu a kirjinsa a ganinta, duk da ya ce zai koma inda ya fito amma ta san zai dame ta a waya.

Tana kai wa ƙofar gidansu sai ga Fati ta fito daga maƙotansu. Murmushi ta sakar wa Lalla ita kuma sai wani harara ta buga wa Fati mai ma'ana da yawa, ita kuma Fati ta san me hararar take nufi, ko ba ta faɗa ba ta san ita da Ibrahim ne don daman gidansu ne za ta tafi saboda yau ba ta je aiki ba ta fito za ta gidansu sai ta ganta tsaye ita da shi, shi ne ta shiga maƙotansu don in ta ce za ta koma gida ganinta za su yi. Yanzu kuma ta fito sai ga Lalla tana shirin shiga gidansu kuma. Sai Fati ta yi wa Lalla magana cike da tsokanar shakiyanci tana cewa
"Ƙawar Fati autar mama, masoyiyar Nura amaryar Ibrahim, Allah Ya ja zamaninki ta wajena har an gama shan soyayyar?." Ɓat fara'ar da Lalla ta fara yi saboda daɗin kirarin da ta fara yi mata, amma jin ta dangata ta da Ibrahim ya sanya ta ɗaure fuska tamau saboda jin haushinsa take yi musamman yadda suka yi da shi yanzu, sannan ta ce
"Ai na jima da sanin ke ce kika turo shi rayuwata don ya ɓata mana ginin da muka jima muna yi nida mahaɗin rayuwata."
"To miye a ciki? Gida biyu maganin gobara fa." In ji Fati. Ta ƙara cewa
"Mu shiga daga ciki autar mama." Cewar Fati.
"Ba don na zo yi maki gargaɗi ba da gidan ma ba shiga ba saboda kin nuna min bare ya fi ni a wajenki."  Lalla ta yi maganar tana wucewa cikin gidan su Fati ba tare da tsaya jiran Fatin ba. Ba ta iske kowa a tsakar gidan ba alamu sun nuna suna falon gidan, can ta wuce ta iske su a falon gidan suka kallon tashar Afrika TV, gaishe da mamar Fati ta yi sannan kuma ta yi zamanta nan ba tare da ta shiga ɗakin Fati ba, duk da ta ga wucewar Fatin dakinta kuma ta san tana can tana jiranta, amma ta ƙi shiga tana kallon TV ɗin ita ma. Sai da Fati ta ga Hafsat ta ƙi shiga ne sannan ta leko nemanta saboda ta san fushi ne ta yi da ita.
"Mama kin ga wai fushi take da ni."  Fati ta yi maganar tana kallon mamarsu.
"Kun fi kusa. Ba ruwana tsakaninku ne." Cewar mamar Fati.
"Besty ta zo ki ji don Allah, ba zan ƙara tsokanarki ba in sha Allah." In ji Fati tana kalar tausayi. Sai Mamar Fati ta ce
"Ahan! Daman na san laifinki ne, ki yi haƙuri autata kin ji" Mama ta idasa maganar tana kallon Lalla.
"Mama ki daina ɓata harkar tunda dai ta hakura." In ji Fati. Sai Lalla ta ce
"Wa ya ce maki na hakura? Ai zan rama kuma akwai ranar ƙin dillanci, yanzu ma don Mama ta yi magana ne da gida zan koma" Lalla ta yi maganar tana hararen Fati. Murmushi Fati ta yi sannan ta ce
"Shikenan tashi mu je ki ji akwai labari."
"Akwai gulma dai." Cewar yayan Fati da shigowarsa falon kenan."
"Ai mu ba mu gulma baban yaya." In ji Lalla sannan ta gaishe sa suka wuce ɗakin Fati.


Bayan sun zauna sai Lalla ta kwashe yadda suka yi da Ibrahim ta faɗa wa Fati har wulakanci da ta yi masa ba ta ɓoye mata komai ba. Kallonta Fati ta yi tana mamakin wani hali ne ta ɗaukar wa kanta saboda an ce ana sonta? Shi wanda ya ce yana sonka shi ne zai cancanci wulakanci? Ba ta san wacce kalar soyayya ce Lalla take yi wa Nura haka ba wacce take shirin mayar da ita marar hankali kuma marar sanin darajar ɗan Adam. Magana ta fara ba tare da ta kalle ta ba
"Tambaya biyu zan yi maki ina so ki ba ni amsarsu. Don Allah wanda ya ce yana sonki ya cancaci wulakanci a gare ki? Ba fa ƙinki ya ce yana yi ba so ya ce!  Sannan kina da tabbacin cewa Nura shi ne mijinki don kun jima kuna soyayya da shi?"
"Me kike nufi ne besty? Abin da na yi masa kuma shi ne nake gani kawai mafita a gare ni saboda ba ni son damuwa ko kaɗan, tambaya ta biyu kuma shi ne da izinin Allah."  In ji HAFSAT
"Ba a wulakanta wanda ya ce yana sonka sai dai a nemi a lallaɓa shi don a rabu lafiya, sannan kuma ba a yi masa maganar waninsa a tare da shi hakan shi ne yake ƙara masa kaimin kula da wacce yake son ɗin, don haka ki daina wulankata duk wanda yake sonki , ki nemi wata hanya wacce kike ganin za ta dace da ke wajen rabuwa da shi. Bari ki ji wasu samari in har suna neman soyayya ba su samu ba ko da ba a wulankata su ba, sai su yi wa budurwa asiri yadda sai abin da suka ce da ita, za su yi mulkin mace yadda ransu yake so don haka ki taimaka ki daina yi masa wulakanci don Allah duk da jikina yana ba ni Ibrahim ba kalar masu cutarwa ba ne." Ta yi maganar idanunwanta tar a kan Lalla wacce ta tafi dogon tunani saboda maganganun Fati sun ɗan shiga jikinta. Sai Fati ta ci gaba da cewa
"Sannan kuma gara da kika ce da izinin Allah shi ne mijinki, saboda in har Allah bai nufa ba, ko da a ce ba Ibrahim ɗin kika aura ba za ki ji kunya matuƙar ba ki auri Nura ɗin ba a kan abubuwan da kike wa Ibrahim."

LALLA HAFSATOù les histoires vivent. Découvrez maintenant