Page 3

18 3 0
                                    

           Littafi na farko 📝

       Shafin kyauta na uku

Suna zuwa gida sai Fati ta azalzali Hafsat da sai sun koma gidan aure tunda su ne ƴan'matan bai kamata a ce ba su tafi kan amarya ba, kuma ga shi auren danginsu ne kar a ga laifinsu na rashin zuwa can, tunda kowa yana can sai su kaɗai daman ba su tafi da wuri ba kuma ga shi yanzu suna tafiya suka baro gidan saboda rashin samun wayar Nura, tunda komai ya daidaita ai sai su tafi gidan kan amarya. Yo su hankalinsu ma ya manta sam da zancen da suka yi da Ibrahim da zai kawo masu waya shiyasa Fati ta ce su tafi don shaf sun manta da wani zancen Ibrahim.
A daidai ƙofar gidan su Fati Lalla ta ajiye Fati sannan ta tuka mashin sai gidansu, ta bude gida ta shiga sannan ta mayar da kofar gidan ta rufe sannan ta kashe mashin ɗin kai tsaye ta wuce ɗakinta ta yi alwalar sallar magriba, bayan ta gama sallah sannan kuma ta yi wanka ta fara shirin tafiya kan amarya.

Ana gama sallar isha'i Fati ta fito daga gidansu ta nufi gidan su Lalla cikin shirinta na sahari wanda suka yi na kan amarya gaba-daya ƴan'matan amarya kuma kala guda suka yi, tana zuwa gidan su Lalla ta iske ta ita ma har ta shirya tana sallar isha'i a lokacin saboda wayar da suka gama ita da Nura yanzu tana shiri ya kira wayarta take faɗa masa Fati ta azalzale ta da sai sun tafi kan amarya, shi kuma yake yi ta jin babu daɗi a ransa da yana gida da yanzu a tare za su tafi da ita babu wanda zai kallar masa ita, amma yanzu da ya yi nisa ya san hakan za ta yi ta faruwa har sai ya dawo gida, tabbas da gaskiyar hausawa da suke cewa ko wa ya bar gida to gida ya bar shi, Allah Ya nuna masa sun gama jarabawa ya dawo gida lafiya don har fara jin kaɗaici yana damunsa tun ma kafin ya kwana garin har ya fara kewar gida da kewar ƙawarsa, sahibarsa kuma ƙanwarsa muradin ransa wato Lallarsa.

Bayan ta sallame sallar ne ta fara yi wa Fati ƙorafi tana cewa
"Besty ni fa kin san ban saba zuwa kan amarya ni kaɗai ba, wallahi ina jin kaɗaici a raina."
Ta ida maganar kamar za ta fashe mata da kuka, sai Fati ta saki baki da hanci tana kallonta kamar ba tare za su tafi ba take cewa wai ita kaɗai za ta tafi ita abun ma dariya ya ba ta na Hafsat amma sai ta dake ta ci magani sannan ta ce
"Ai na jima da sanin haka ƴan'mata, kuma ba kowacce rana ba ce take zama juma'a ba don haka in za ki tashi mu tafi ki tashi in kuma so kike yi cikin dangi a yi da ke to ki zauna ni kin ga tafiyata." Ta karasa maganar tana yin gaba kamar tafiyar gasken za ta yi don ta san in ta yi wa Lalla da wasa za ta ɓata masu lokaci ba za su tafi da wuri ba, za ta yi mata hirar kewar Nura da ta fara yi har dare ya yi masu kuma a tafi kan amarya a bar su, ga shi ba su san inda za a kai amaryar ba balle su iske ƴan kan amaryar can. Ai kuwa sai Lalla ta ce
"Wayyo ni Hafsat marainiya ! Wato Fati ba za ki ji tausayina ba ko? Babyna bai gari amma sai faɗa kike yi min don na faɗi gaskiya ko? Ai yana dawowa kamar a kunnensa aka yi."

"In za ki rufe dakin ki rufe mu tafi in kuma za ki tsaya min sharri ka waya ki yi record in ya zo ki kunna masa ai shikenan, ni na tafi sai kin zo." Cewar Fati da ta kusa fita daga ɗakin tana dawowa da baya haɗe da mika mata waya.

Lalla ba ta ce komai kawai sai ta ɗauki wayarta da jakarta da tana yin gaba, ba ɓata lokaci ta rufe ɗakinta saboda daman duk gidan babu kowa suna can, sannan suka rufe ƙofar gida suka tafi a adedeta sahu don ba za ta iya tukin mashin ɗin dare ba shiyasa kawai ta buƙaci su hau adedeta sahu. Suna zuwa bakin hanya ba su sha wahala ba suka samu adedeta sahu suka tafi gidan su amarya.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

Bayan sallar magriba Farida ta rangaɗa waka na kece raini, ta matsu su tafi wajen antynta wacce ta sace wa yayanta zuciya lokaci guda, shiyasa tun da aka yi sallar magriba take yi ta zumuɗin tafiya shi kuma ya ce sai an gama sallar isha'i , ba ta dai fito ba daga cikin ɗakinsu sabida tsaro don tana tsoron mamansu ta hanata tafiya shiyasa ta yi zamanta ba ta leko ba, sai ta waya ne ma ta kira Ibrahim yake ce mata ai sai bayan isha'i za su tafi in babansu ya shigo sun gaisa da shi, don ba zai yiyu ba ya dawo daga tafiya bai ga mahaifinsa ba a ranar da ya dawo ba saboda ya san da wiya in ya fita yanzu in ya dawo ya iske babansu bai yi bacci ba. Shiyasa ya ce da Farida ta bari har su gaisa da babansu sannan su tafi.
Ana gama sallar isha'i tun a masallaci Ibrahim suka haɗe da babansu a can suka gaisa sannan bayan sallah kuma suka biyo hanya tare har suka zo gida suna gaisawa yana yi masa tambayoyi game da aikin, a tare suka wuce babban falon gidan tun a hanya ya yi wa Farida message da ta fito su tafi, shigarsu falo ta yi daidai da fitowarta daga ɗakinta, tana gaishe da babansu haɗe da cewa
"Babana sannu da zuwa."
"Malama babanmu dai za ki cewa, wannan wayo ne ai." Inji Ibrahim yana murmushi saboda ya san ya tsokani ƙanwar tasa, ai kuwa a shagwaɓe Farida ta ce da babansu wanda yake shirin yin zaune saman kujera shi ma yana kallonsu ya san za a fara drama yanzu tsakanin yaya da ƙanwa.
"Babana ka ga big bro ko?"
Alhaji Abubakar ya ce
"Ina ganinsa mana, sai in hana ki rakkiyarsa ma ai sai mu gani abin da za a yi tunda har yana tsokanarki."
"Yauwa babana na kaina." In ji Farida tana yi ma Ibrahim dariya, sai ta ƙara de cewa
"Bari ma in koma ɗaki babana, sai da safe."
"Yau kuma ni za ki yi wa haka shalelena, please babanmu ku sanya baki, mama ku sanya baki ta rakka ni don Allah." Cewar Ibrahim yana maganar haɗe da kallon mama da take hakimce saman kujera tana kallonsu yadda suke yi sai ka ce uwa guda ta haifi Farida da Ibrahim, da yadda suke gudanar da rayuwarsu cike da fahimtar juna da jin daɗi ba su da damuwar komai in suna tare da juna, kamar ta shake Ibrahim take ji don kullum cewa take yi shi ne ya rabata da ƴarta don duk cikin ƴaƴanta Farida ce kawai mai kula sa, babu wanda bai biyo halinta ba saɓanin Farida ita kaɗai ce take da hali irin na mahaifinta da kuma halin Ibrahim shiyasa tasu ta zo ɗaya har wani kamani kuma suke sai ka ce uwa guda ta haife su. Ƙaramin tsaki Hajiya Sabira ta ja a ranta tana yamutsa fuska haɗe da cewa
"Rufa ni sakaya ni, wacce ni? Kun fi kusa da ita fiye da wacce ta haifeta ma." Duka kallonta suka yi sam babu wanda ya ji daɗin maganar da ta yi, basarwa kawai suka yi don inda sabo sun saba da halinta na rashin kyautata wa Ibrahim da ba ta yi, amma sai Farida ta yi magana don ta ga kamar ran Ibrahim ya ɗan sosu da maganar
"Shikenan mu je amma yasin kar ƙara, don in ka ƙara tsokanata sai na yi kuka."  Ta ida maganar a shagwaɓe kamar ƴar yarinya ƙarama ta yi kyau abunta cikin hijabinta mai hannunwa ya yi mata kyau tsaf da ita.
"Ba zan ƙara ba ƙanwata mai son farincikin yayanta, mu je to. Mama mun tafi gari a yi mana addu'a."
In ji Ibrahim ya ida maganar yana kallon mama da ta daskare tana jin haushi a ranta na Ibrahim, wai Ibrahim ɗin nan da me yake taƙama ne da zai dinga yi mata yi mata wannan iskancin ne, ta yaya zai yi tafiya tare da ƴarta amma ba zai faɗa mata ba kafin lokacin ko kuma ya nemi izininta sai dai ta ji labari, lallai dole ta san abun yi tun wuri, ba zai yiyu ba sam ya raba ta da ƴarta. Sai ta karkarce baki kamar babu abin da take sakawa a ranta sai ta ce
"Ina kuma za ku tafi ne cikin daren nan?"
"Gari za mu tafi mama." Cewar Farida.
Wani kallon kar ki raina min wayo, sannan kuma ba da ke nake ba Hajiya Sabira ta yi wa Farida sannan ta ce da ita
"Kuma shi ne ba za ki ce da  Samira ta shirya ku tafi tare ba? Ke Samira tashi ki shirya ku tafi tare da su ai ke ma ƙanwarsa ce."
Samira wacce take zaune tana tunanin Ibrahim kuma da yadda yake magana yanzu duk ya tafi da imaninta kuma ga shi tana ganin su baba sun shigo falon amma ko kallonsu ba ta yi ba balle su samu albarkar gaisuwa daga gare ta , don ita sam ba ta tarbiya a gidansu babu wani zancen gaisuwa haka suke gudanar da rayuwarsu sai a hankali ga su nan dai, cikakkun ƴan boko ne na bugawa a jarida irin wanda babu wata tarbiya a gidan. Samira tana shirin tashi tsaye sai Farida ta ce
"Amma mama gidan su Anty Safiya za mu tafi fa, kuma don na ga inda za mu tafi gida ne, kuma ba wani nisa ne za mu yi ba shiyasa ma ban faɗa maku ba." Ta ida maganar tana yi ma Ibrahim signal da ido don ta san in har ta ce haka to fa da wiya Samira ta tafi, ai kuwa Samira da ta tashi da murnata ta yi ɗaki don ta shirya, za su yi tafiya da Ibrahim sai ta ji inda aka ce za su tafi ai kuwa sai cewa ta yi
"Ku je ba zan tafi ba "
Ibrahim a zuci wani daɗi ya ji a ransa amma dayake bai son babansu ya fahimci wani abu sai ya ce da ita
"Me ya sa?"
Tsabar haushin da take ji ko amsa masa kasa yi ta yi sai wucewa da ta yi a ɗakin da ta sauka tana jin taikaci a ranta,  sai ita kuma Hajiya Sabira ta mayar da kallonta ga Farida sannan ta ce da ita
"Burinki ya cika ta fasa tafiya ko? Baƙar munafuka ni dai wallahi wannan baƙin halin ba nawa ba ne, akwai inda kika koyi munafurci don ni dai ban iya shi ba."
Kafin su ce wani abu sai Alhaji Abubakar da ya ji haushin abin da Hajiya Sabira ta yi yanzu sannan ya ce da su
"Ka ga Ibrahim ku tafi Allah Ya kiyaye hanya," suka amsa da amin a tare sannan suka yi gaba. Cikin wata ƙatuwar mota suka tafi wacce wannan karon ne Ibrahim ya fara hawanta saboda ya fito daga mission Côte d'Ivoire (Ivory cost) ya samu kuɗi sosai ya siyeta kuma a lokacin sai ya tafi wata mission wani gari shiyasa bai samu damar hawanta ba sai wannan karon da zai tafi gidan su sahibarsa wacce bai taɓa ganinta ba a fili sai dai a zuci wacce ta yi nasarar sace masa zuciya dukda bai taɓa ganinta a fili ba, amma muryarta kaɗai da ya ji ya shiga shaukin begenta da ƙaunarta.

Sai ta taga(window) Samira take lekon su Ibrahim lokacin da suke fita daga gidan, tana ji tana gani sun fita amma an barta a gida, ita ta fara tsorata da wannan halin na Ibrahim don duk lokacin da ya zo hutu hakan yake yi mata ko gaisuwarta bai amsawa, kuma duk lokacin da zai zo hutu tana gidan zai zo amma har yanzu babu fahimtar juna ko ɗaya a tsakaninsu sai azabtuwa take yi da soyayyarsa don ita son gaskiya ne take yi masa saɓanin iyayensu da suke son haɗa su saboda wani dalili nasu na daban, ita kuma sam ba ta son hakan da yake yi mata ta fi son su fahimci juna da shi tun yanzu saboda za ta zama matarsa amma babu wani hirar kirki da yake shiga tsakaninsu, gaskiya ba za ta yarda da wannan abun ba dole ne ta koma gidansu a san wacce za a yi don ta gaji da wannan zaman da take yi ace shekara kusan ashirin da shida ba ta yi aure ba, kuma wanda za ta aura ɗin bai taɓa yi mata hirar kirki ba sai dai kullum tsana da tsangoma, ba don Allah Ya ɗora mata sonsa ba da tuni ta cire sa daga zuciyarta ta je ta yi auri da samarinta. Kuma ƙarin bakinciki ma shi ne wai yanzu Farida ta ce mata gidan Anty Safiya za su tafi don ta san ba su shiri da ita don ta kar ta bi su ne, amma ta san da wiya ma a ce can suka tafi watakila makircin Farida ne da ta saba yi mata tamkar Farida ba jininta ba ce take yi mata hakan saboda yayanta da suke uba guda ita kuma ita da mahaifiyarta uwa guda ta haife su. Abin da ba ta sani ba shi ne Farida kuma ba tsanarta ta yi ba halinta ne ba ta so na shigar da take yi da kuma boko da ta yi mata yawa ga kula samari barkatai kuma a hakan take son yayanta.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞

Bayan fitar su Ibrahim daga falon, sai Alhaji Abubakar ya kalli Hajiya Sabira yana cewa
"Don Allah ki faɗa min wai ke kika haifi Farida ko dai an sauya maki ita ne a asibiti don kin san dai ni lokacin da kika haihu na yi tafiya ba ni gida?"
"Haka nake tunani kullum don na kusa tafiya ma a yi min test NDA ni da ita don na fara tunanin da wiya in ni na haife ta." Cewar Hajiya Sabira ta ida maganar a zafafe, ganin da ta yi Alhaji Abubakar bai ce komai ba sai kallonta da ya yi kawai yana mamakin hali irin nata, mace kamar ba mai ilmi ba kishi yana neman kaita ya baro, duk wiyar da Ibrahim ya sha yana ƙarami bai ishe shi ba sai an ƙara masa da wata yanzu da ya girma. Ganin da ta yi yana kallonta da mamakin abin da ta ce ya hana sa samun damar cewa komai,  saboda maganarta da ta tsaya masa a rai sosai da sosai, sai ta samu damar ƙara cewa
"Tabbas na fara zargin wani ya sauya min ƴa a asibiti ko kuma ita ce amma tun tana ƙarama an yi mata asirin rabata da ni saboda a ce matuƙar yaron can ya zo garin nan to babu wani jin daɗi da kwanciyar hankali , bakina zai fara ciwo , zuciyata tana tafarfasa, haba! Haba! Wallahi na gaji da wannan halin nata, bari ma yau ta dawo ta zo sai ta zaɓa ko ni ko wancan yaron mai zugata tana yi min rashin kunya"
"Wato Hajiya Sabira halinki sai ke, Allah Ya sawwaka Ya shirya ki in ke mai shiryiwa ce don wallahi al'amarinki sai addu'a kawai" inji Babansu Ibrahim ya ida maganar yana hawa saman dinnig don in har ya biye mata yanzu za su tafka abun kunya gaban Samira don ba ta kirki ko kaɗan yarinyar ga rashin ɗa'a, saboda bayan fitar su Ibrahim ta gama lekensu dawowa ta yi falon ta zauna kuma a gaban idanunta ta ji Hajiya Sabira tana bambami amma ba ta bar falon ba sai ta yi zaune don so take ta yi kalar tausayi yadda za a sanya ranar aurensu ita da Ibrahim nan lokaci kaɗan.


Littafin kuɗi ne, nera ɗari biyu yake in kuna son karantawa har ƙarshe ki tuntuɓi wannan lambar +22784506476

Real Nana Aisha 🥰

LALLA HAFSATOù les histoires vivent. Découvrez maintenant