"Nura ba ka san ajinka ba ne!" Cewar principal a ɗan tsawace, wacce ta gaji da lallaɓar Nura tunda malamarsu ta kawo su wajenta a kan ba ajinsu guda da Lalla ba, amma sun ƙi yarda da hakan sai dai cewa suke yi ai unguwarsu guda don haka aji guda za a kai su ba za su yarda a raba su ba. Ai kuwa sai ya fashe da kuka don ya tsorata da irin tsawar da ta yi masa duk da ba da ƙarfi sosai ta yi maganar ba. Nura yana fashewa da kuka sai ita ma Hafsat ta fashe da kuka.
Kallon-kallo ake tsanakin principal da malamar su Nura, suna mamakin wannan shakuwar ta yara kamar waɗanda suka fito ciki ɗaya na yadda ba su son a raba su da junansu ga kuma kukan da suke famar yi masu kamar waɗanda aka yi wa duka.
"Ikon Allah!" Cewar malamar su Nura.
"Sai kallo!" In ji principal ta idasa maganar haɗe da fara lallaɓar Nura don ta gane tsawar da ta yi masa ce ta sanya shi firgita haɗe da kukan wanda har ya firgita Hafsat. Yayin da malamar su Nura take lallaɓar Hafsat don yara sai da lallashi musamman ƴan aji na ɗaya wanda ba hankali ne da su ba"Madam ina gani abin da za a yi a kai su aji guda don shi ne mafita a gare mu da su don wannan ɓata mana lokaci kawai za su yi." Cewar malama bayan sun yi nasarar shawo kan su Nura daga kukan da suke yi.
"Hakan nake tunani a raina, ku je da su can ajin naki. Amma yaran sun ba ni mamaki ko dai ƴan'uwa ne?" Cewar principal tan kallon su Hafsat
"Wallahi ban sani ba Madam. Amma duk yadda aka yi akwai shaƙuwa tsakaninsu." In ji malamarsu Nura
"Haka ne gaskiya . To Allah Ya sa su mayar da himma ga karatu, don in har na ga za su yi min shiririta dole zan raba masu aji. Ba zan ɗauki lalaci ba gaskiya " in ji malamarsu Nura ta idasa maganar tana kama hannayensu sannan suka yi wa principal sallama suka wuce aji.
Ko a cikin ajin ma waje guda suke zauna, ba ta ce masu uffan ba ta fara koyar da su darasinsu na yara har zuwa lokacin fita break ya yi sannan suka fita. A tare suka tafi siyen abin da za su siye na break, kuma bayan sun dawo suka zauna suka ci tare. Bayan sun gama kuma suka keɓe waje daban suna wasarsu har zuwa lokacin komawa break ya yi sannan suka koma aji.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya kullum Hafsat ba ta da aboki a makaranta sama da Nura, kodayaushe suna tare babu abin da yake raba su wa junansu. In har ɗaya ba shi da lafiya to ɗaya ba zai tafi makaranta ba saboda tare suke tafiya kullum. Wannan dalilin ya sanya ko ƙawa Hafsat ba ta da ita haka Nura shi ma ba shi da shi sai dai waɗanda suke dawowa gida tare.
Inda aka ci sa'a suna fahimtar karatu sosai daga farasanci har zuwa larabci. Dayake yadda karatun nasu yake shi ne da safe in suka yi faransanci da yamma kuma malamar islamiya ce take yi masu karatun mahammadiya. Wannan kenan.
Ranar da ba a zuwa makaranta kuma sai su tafi Islamiya a can ma ajinsu guda sai dai ba su zama waje guda saboda ba a yarda da hakan ba, su ma sun sani don wajen mata daban na maza daban ba kamar yadda ake zama school ba ana haɗewa akwai bambanci.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya tun ana tafiya tare da su a makarantar boko har aka daina don yau da gobe sai Allah har sun san hanya kodayake dama can sun san hanyar kawai dai ba a barin suna tafiya su kaɗai ne saboda tsaro, amma yanzu dayake akwai masu zuwa makarantara sosai a hanya shi ya sa suke tafiyarsu su kaɗai ba tare sun jira kowa ba ko kuma an jira su har ma sun tsayar da wani wajen tafiya.
A haka iyayen su Hafsat suka fita daga takaba, sannan suka ci gaba da rainon yaransu, ƴan biyu da Maryam waɗanda sai girma suke ƙarawa ma sha Allah. Sosai dangi suke taimaka masu duk da Lawali ya bar masu dukiya wacce za ta ishe su amma ba a taɓa ta ana taimaka masu. Ƙanensa sosai suke aiko masu da abinci da kuɗi duk da ba gari guda suke da zama ba. Amma babu abin da suka rage su da shi na rayuwar yau da kullum musamman Hassan wanda shi ne yake gari guda da shi. Duk sati yake kawo masu abinci ko saboda iyayensu da suke cikin gidan ai bai kamata ba su bar matan Lawali su kaɗai da ɗawainiya ba. Ga kuma aminin Lawali Sulaiman wanda shi ma ba baya wajen taimaka masu dayake yana da hali sosai ga kuma siyasa da yake taɓawa kaɗan-kaɗan. Nan da nan ya turo wa ƙanensa Abubukar kuɗi don ya siye wa iyalan amininsa abinci da sutura.
