💞♥️💓Lalla Hafsat💞♥️💓
Labari, Rubutawa✍️✍️
Daga Alƙalamin
REAL NANA AISHA
WATTPAD : Humairah2019*
____________________________________🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________Littafi na farko 📝
Shafi na biyu
Sai dai babu yadda zai yi dole ne sai ya yi tafiyar don ta zame masa cilas, amma da ba don haka ba da ya ce mai motar ya sauke sa saman hanya ya dawo gida don ba zai yarda wani ya kallar masa Lalla ɗinsa ba, haka ya yi ta gwada lambarta ko za ta shiga sai dai sam babu network saboda cikin daji suke haka ya yi hakuri ba don ya so ba sai don babu yadda zai yi ne, sai sako ya tura mata saman ɗayan layinta wanda yake cikin babbar wayarta in network ya dawo sai ta same shi. Sai faman kallon wayarsa yake yi ko sakon zai tafi amma ina ya ƙi tafiya sai can bayan kusan awa ɗaya sannan ya tafi sai kuma yana yi jiran amsa amma shiru kake ji kamar an aiki loma jewayar maƙoshi. Sai alakanta rashin samun amsar da matsalar network ne babu inda yake.
💞💞💞💞💞
Shi kuma Ibrahim a tuninsa zafin abin da ya ce ne ya sanya Nura kashe waya sai ya ce a fili
"Da alama saurayinta ne,oho ma dai ko ma miye ɗinta ni kam sai na je na ganta"
A haka suka iso gida, kai tsaye ɓangarensa ya wuce, dreba yana biye da shi da akwatinsa, makuli ya sanya haɗe da buɗe ɗakin, yana buɗewa wani kamshi ya daki hancinsa na turaren wuta da turaren ɗaki,kuma ga shi an gyara masa ɗakin gwanin birgewa sai ka ce wanda yake da mata, murmushi ya yi yana jin daɗin wannan aikin da aka yi masa ya san ba kowa ba ne zai gyara masa ɗaki face Farida don ita ce kaɗai take da makulin ɗakinsa kuma ita kaɗai ce yake shiri da ita kaf gidan in aka cire mahaifinsa, ita ce ta fi kowa kirki a gidan nasu shiyasa tasu da ita ta zo ɗaya kuma yake ji da ita fiye da kowa a gidan kamar yadda take ji sansa fiye da sauran yayyanunta. A fili ya ce
"Allah Ya yi maki albarka ƙanwata, kuma ya ba ki miji na gari"
Sai ya wuce ƙuryar ɗaki kai tsaye banɗaki ya shiga ya yi wanka haɗe da alwala ta sallar la'asar. Sai da ya yi sallah sannan ya shiga cikin babban falon gidan, da sallama a bakinsa ya shiga, Hajiya Sabira tana hakimce saman kujera da wata budurwa da take sanye da riga da buje ƴan kanti duk sun fitar da surar jikinta, fuskarta cike da kwaliyya kamar za ta je gasar kyau sai kallonsa take yi tana sakar masa murmushi amma sam bai san tana yi ba saboda hankalinsa yana ga Farida wacce ta fito da gwadala tana cewa
"Oyoyo! Oyoyo! Ɗan'uwa rabin jiki, ina yi ta sauri in kai maka abinci da na girka maka na musamman har ka riga ni isowa ma." Ta ida maganar a shagwaɓe.
"Ƙanwata shagwaɓaɓɓiya, ai ni har na yi fushi da ke, wai kina jin na iso ko ki tarbe ni" ya ida maganar yana zama saman kujera da take fuskar Hajiya Sabira yana cewa
"Mama na same ku lafiya?"
Kafin ta amsa sai ya tsinkayi muryar Farida cikin shagwaɓa tana cewa
" Yayana ba haka ba ne wallahi ina sallah ka shigo kuma ka ga ban gama yi maka abinci ba shiyasa ban tafi wajenka ba, kai ma ka san ai ba mu yin ƴar haka da kai" ta ida maganar tana zuwa kusansa haɗe da mayar da kallonta ga Hajiya Sabira da take yi maganar ido ita da budurwar da take zaune kusanta, tana cewa
"Maman kin san ban gama girkin da wiri ne ba ko?"
Hajiya Sabira ta ce
"Don Allah ki raba mutane da zancen nan duk kin hana mutane magana daɗa kin fara ko?"
Farida ta marairaice haɗe da cewa
"Yanzu kuma me na yi ni ?"
Hajiya Sabira ta ce
"Humm, Ibrahim an zo lafiya ya hanya"
Ya amsa da
"Lafiya kalau Alhamdulillah mama ya bayan rabuwa?"
"Sai Alkairi" kawai ta ce sannan ta zunguri budurwar da take kusanta da take yi ta faman kallonsa, sai a lokacin hankalinta ya dawo jikinta sai ta yi magana cikin kashe murya tana cewa
"Sannu da zuwa yayan Farida, fatan an iso lafiya?" Ta ida maganar tana wani fari da ido saboda yadda ta ga yana son Farida shiyasa ta kira sa da hakan, sai ya amsa mata da
"Lafiya kalau Alhamdulillah"
Tana shirin ƙara magana sai ta ga ya tashi tsaye yana cewa
"Mama zan shiga in ɗan huta kafin sallar magriba"
"Yaya ka tsaya mana in zubo maka abinci na fa gama" cewar Farida, sai ya ce da ita
"Ki kai min ɗakina kin ji ƴar ƙanwata?"
Cikin murmushi Farida ta ce
"An gama sir." Ta ida maganar da alamar girmama yadda sojawa suke gai da manyansu, sai ta ba shi dariya bai san lokacin da ya kyalkyale da dariya ba yana cewa
"Kai ƙanwata duk ni kaɗai?"
Ta ce
"Ka fi ƙarfin haka yayana na musamman, gani nan tafe kar ka yi bacci har ka ci abinci ka ƙoshi"
"An gama antyna." Inji Ibrahim sai ya yi gaba yana murmushi, duk lokacin da yake tare da ƙanwarsa Farida yana jin daɗi a ransa saboda yadda take kula da shi ko yayannunta da suke uwa ɗaya ba ta kulawa haka saboda ba su wani sakar mata fuska don tana kula shi saboda mugun kishin da yake tsakaninsu duk da ba shi da mahaifiya da rai amma suna yin kishin da shi yadda suka ga mahaifiyarsu tana yi da shi, ita kuma Farida babu ruwanta da abin da suke kullawa saboda ƙaunar da take tsakaninsu tun lokacin da aka haife ta shi ne yake kula da ita fiye da sauran kannensa har shakuwa ta shiga tsakaninsu fiye da tunanin mai karatu wanda sai bayan Farida ta girma ne ta fahimci ba uwa guda ta haife su ba saboda tsana da tsangomma da take gani mahaifiyarta tana yi masa.
A haka ya kai ɗaki yana tunanin rayuwar duniya da yadda yake jin ƙanwarsa Farida, da ace yana da wani babban aboki wanda ya san zai kula masa da Farida sosai da sai dai kawai ya haɗa ta da shi don ba zai so ba ta auri wanda zai gallaza mata ba kasancewarta mace mai hankali da hangen nesa da girmama manya, yana ji a ransa duk ranar da Farida ta yi auri mijinta ya buge ta a ranae sai ya kulle mijin don ba zai taɓa yarda ba, shiyasa kullum yake yi mata addu'ar Allah Ya ba ta miji na gari salihi wanda ba shi da matsala mai hali irin nata.
