Bayan wani lokaci su Lawali suka fara karatunsu a Jami'ar Niamey, shi da Sulaiman amininsa ɗan gidan aminin mahaifinsa kuma. A lokacin ne aka yi wa Usaina aure, bayan ta gama karatun koyarwa na firameri dayake ita shi ta zaɓa kasancewarta mace. A Toroɗi cikin dangin iyayenta aka kai ta, wacce sam ba ta so ba don dai babu yadda za ta yi ne saboda ganin tana birni ake ɗauke ta aka kai ta ƙauye duk da mijin da ta aura ɗin malamin makaranta ne kuma cousin ɗinta ne a can yake koyarwa.
Su Lawali suna shekara ta biyu a jami'a Hasan ya samu jarabawar shiga jami'a shi ma, a lokacin shi ma tare da abokinsa ɗan maƙotansu mai suna Abubakar wanda su ma abotarsu kamar ta Lawali da Sulaiman ne har ma za a iya cewa ta kere tasu ɗin. Komai a tare suke yin shi tamkar ƴan gida guda kuma waɗanda suka fito ciki ɗaya, wani ma in ya ji sunan Hassan har tambaya yake yi me ya sa ba a kiran Abubakar da Hussain don a zatansu shi ne ɗan biyu ɗinsa duk da ba kama suke yi ba amma shakuwarsu ce ta kawo hakan.
Su Hassan ba su yi ƙasa a gwiwa ba suka iske yayannunsu a can suka fara karatunsa.Bayan wani lokaci abubuwa da yawa suka faru ciki har da kammalawar karatun su Lawali inda suka fito da sakamako mai kyau, dayake aikin gidan gona ne suka yi, suka fara aiki a lokacin ne aka raba su inda aka tura guda Zinder wato Sulaiman, shi guda kuma aka kai shi Tahoua wato Lawali, sam ba su ji daɗin haka ba, don dai babu yadda za su yi ne, sai suka yi haƙuri haɗe da sanyawa karatun albarka. A lokacin duk ƴaƴan Alhaji Samaila sun girma kowa ya yi nisa da karatu, wasu ma duk sun yi aure in aka cire auta Hauwa'u wacce sai sauran maza biyu da suke sakandari
A can Tahoua Lawali ya haɗu da Amina wacce ita ma fulani ce aiki ne ya mayar da iyayenta can da zama suka yi aurensu na so da ƙauna, bayan aure suka zauna a nan gidan su da yake garin Maraɗi tare da danginsa, da hutunsa ya ƙare sai ya koma a bakin aikinsa tare da amaryarsa, ana yin wata goma da aurensu Amina ta haifi santalelen ɗanta namiji son kowa ƙin wanda ya rasa, ranar suna yaro ya ci sunan Samaila wato kakansa na wajen uba, yaro ya samu gata sosai a wajen kakanninsa saboda ƙarar da iyayensa suka yi wa kakanninsa na yi masa takwara. Bayan Samaila kuma Amina ta haihu mace mai suna Saratu . A lokacin ne wajen sunan Saratu, Hasan ya haɗu da wata budurwa bakatsina ƴar asalin Maraɗi, yana ganinta ya ji ya kamu da sonta bai yi ƙasa a gwiwa ba ya bayyana mata asirin zuciyarsa inda ba ta ba shi wahala wajen amincewa ba. Nan da nan manya suka shiga lamarin aka biya komai sannan aka ɗaura aurensu. A lokacin Hasan yana koyarwa saboda shi ne karatun da ya yi, ba laifi yana samun albashi daidai gwargwado. wata rana abokinsa Abubakar ya zo kawo masa ziyara ne a hanya ya haɗu da wata ƴan'mata mai suna Hajara. Tun da yake bai taɓa soyayya ba amma kallo ɗaya da ya yi wa yarinyar nan ya ji ya kamu da sonta. Duk da mahaifinta mai kuɗi ne sosai bai yi zaton zai samun ta ba, amma dayake Allah Ya kaddara haka za su yi aurensu da ita. Iyayenta suka nema masa aurenta ba tare da tunanin ita ƴar gidan masu kuɗi ce shi kuma ƴaƴan ma'akatan gwamnati ne wanda sai wata ya mutu ne suke samun kuɗi. Haka mahaifinta ya amince ba, don shi mutumin kirki ne sosai mai kuɗi wanda ya san darajar ɗan Adam. Bayan aure matar Abubukar suke zaune a gida guda ita da matar Hassan wanda gidan ma a tare suka siye shi har suka gina shi tare. Dayake Hassan ya riga Abubukar aure shiyasa bai koma ba gidan sai ya bari har zuwa lokacin da zai yi aure shi. Shi ne yanzu matar ta tare a gida. A maimakon su raba katanga sai suka bar shi haka nan ba tare da sun raba ba saboda ƙarfin zumuncin da yake tsakaninsu sai dai runfa kawai da kowannensu ya killace ɓangarensa da ita. A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya komai a tare suke yi kamar waɗanda suke da miji guda, hatta girki tare suke yin shi, in sun gama kuma sai su zuba su ci. Haka su ma mazajensu tare suke cin abinci sai ka ce ƴaƴa da ƙane_
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya yau da gobe asarar mai rai, matar Abubakar ta riga matar Hassan samun ciki inda ta haifi ƴarta mace sai dai ba ta tsaya ba, ko sati ba ta yi ba ta rasu. Bayan watanni matar Hassan Saudat ta samu cikinta na farko, wanda take yi ta rashin lafiya, iyayenta sun so ta koma wajensu da zama don su yi jinyarta amma ƙememe Hajara ta hana Saudat tafiya saboda ta ji hirar da Hassan yake yi da Abubakar inda yake masa zancen bai son tafiyar Saudat gida, hakkinsa ne ya kula da ita bai son ɗora wa iyayenta nauyi. Wannan zancen da ta ji shi ya sa ta roki alfarma za ta kula da Saudat tamkar yadda za ta kula da ƴar'uwarta ta jini. A haka cikinta ya fara girma, duk da Hajara tana da ciki ba ta nuna wa ba, ta yi shiru da bakinsa don ta san tana cewa ciki ne da ita za a hana ta kula da Ssudat. A haka cikin Saudat ya tsufa sai a lokacin ne ta fara samun lafiya, sai a sannan suka gane ashe ita ma Hajara tana nan kunshe da nata cikin ba a sani ba saboda bai wani ba ta wahala ba. Sai da ya fara turo gaba ne sannan aka fahimci da cikin. Sosai iyayen Saudat suka yi mata godiya na alkairin da ta yi masu wanda ba za su taɓa mancewa da shi saboda ta yi masu hallaci a rayuwa don babu abin da ba ta yi wa Hajara, duk da kasancewarta ƴar gidan masu kuɗi ba ta taɓa nunawa Saudat hakan ba ko a fuska