*💞♥️💓Lalla Hafsat💞♥️💓*
Labari, Rubutawa✍️✍️
_Daga Alƙalamin_
*REAL NANA AISHA**WATTPAD : Humairah2019*
*____________________________________**🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*Tun dafa farkon littafin nan har zuwa ƙarshensa sadaukarwa ne a gare ku ƴan'uwa na amana, ƙawayen asali masu matuƙar muhimmanci a gare ni wato 6 STARS INDEED *(Sweetheart Farida, Habibaty Haupha, My Hanta Manab, My Zayishatul-humaira, my Fa'iza, and me also Nana Aisha 🥰🥰🥰)*
Littafi na farko 📝
_Daga wannan shafin na gama shafin kyauta, kar ku manta da Lalla Hafsat part biyu ne, har yanzu muna cikin part 1, kuma shafi na goma kaɗai ne muka yi har yanzu akwai saurar sarkakiya wacce sai wanda ya biya ne zai gane abin da yake wakana, da sauran rina a kaba reals fans, ku nemi naku ku karanta babu tsada nera 200 ne kacal, mutanen Niger ƙasata ku kuma 300FCFA ne sur n'importe quel sim, airtel, orange moov sahelcom_
Ina maraba da ku 🥰🥰🥰🥰*Shafin kyauta na goma*
"In har ba so kake yi ba ka nuna min ba ni ce na haifi Ibrahim ba, ina so a sanya ranar aurensu da Samira!"
Shi ne abin da Hajiya Sabira ta ce lokacin da ta shiga falon Alhaji Abubakar maimakon ta yi sallama. Kallonta ya yi yana mamakin ƙarfin hali irin nata, kamar ba da ita ya yi magana ba kwananki akan ba zai yi wa Ibrahim dole ba, kamar ba ta san abin da yake faruwa ba a wannan lokacin? Anya kan matar nan ɗaya kuwa? Tana da labarin komai kuma ta san komai amma take gaskiya?
Sai ya fara magana shi ma a hasale kamar yadda ta yi ɗin don ya gaji da masifarta a kwanan nan, ina dalili ina mafari, babu abin da mace ta aje sai son kai da son nata?"A gidan nan in aka cire ni kin fi kowa sanin halin da ake ciki? Kuma kin san abin da na faɗa maki kwanankin baya ko? In kuma kin manta zan iya tuna maki? Bari ki ji Sabira ko da ke ce kika haifi Ibrahim ba zan yi masa auren dole ba, auren soyayya ma da yawa an yi sa bai je ko'ina ba balle auren dole musamman namiji ne bai son auren, sannan kuma yana da wacce yake so,don haka ba zan tauye masa hakinsa ba wallahi, amma dai zan tuntuɓe sa in har ta amince to zan iya tursasa shi ya haɗa su ya aura saboda ni kaina ina jin tausayin Samira, amma ba batun hana shi auren wacce yake so!" Alhaji Abubakar ya yi maganar don ya fara jin haushin abubuwan da suke faruwa a gidansa.
"Ta nan ka ɓullo! In har zai haɗa su ya aura to babu damuwa amma dai a tattabar ƴata ce uwar gida, don wallahi ba zan sha wahala a kan yaro ba ina ji ina gani ya auro wata bare ta raba ni da shi, ƙarya ne wannan." In ji Hajiya Sabira tana kunfar baki saboda tsabar masifa
"Ki daina zancen ƴarki ce uwar gida sai in har na ga yiyuwar haɗa auren, in kin gama ki rufe kofar zan ɗan mike." Cewar Alhaji Abubakar ya idasa maganar yana nufar kuryar ɗakinsa don bai son hayaniya ko kaɗan. Ita kuma ta tsani suna magana ya share ta abun yana ƙona mata rai, sai ita ma ta bar masa ɗakin zuwa babban falo ta kama hannun Samira da take zaune tana jiran fitowarta daga wajen babansu, sannan suka yi cikin ɗakinta. bayan ta zauna sai ta zayyane wa Samira yadda suka yi da babansu.
cikin wani irin zabura da matuƙar ruɗani Samira ta tashi tsaye tana
"No! No! No! Ba zai yiyu ba! Ba zai taɓa yiyuwa ba in haɗa wata da wanda nake so a matsayin matansa! ko da ba ni son shi ba zan taɓa yarda mijina ya auri wata ba balle ina matuƙar sonshi da ƙaunarsa, wallahi mama zan iya kashe ko wacece wacce za a haɗa mu da ita, don haka na haƙura da aurensa Allah Ya ba ni nawa mijin ni ma don na tsani kishiya ko sunanta ba ni son ji."
"Dole ki aure sa Samira! Dolenki ki aure sa don wacce yake so ba sonshi take yi ba." Cewar Hajiya Sabira cikin ɗaga murya don auren Samira ne kawai zai sanya ta cikar burinta a kan Ibrahim na wani kudiri nata wanda ta bar wa kanta shi a matsayin sirri.
Samira ba ta ce komai ta fita daga ɗakin da kallo mama ta bi ta cike da tausayinta saboda soyayyar da take yi wa wani shi ma yana son wata, son maso wani koshin wahala. Tana fita sai ga Farida ta shigo dakin da sallama ko kallonta mama ba ta yi balle ta amsa sallamarta, sai ma tashi da ta yi ta wuce kuryar ɗaki, ita ma Farida sai ta bi ta ɗakin tana cewa
"Mama me ya sa ba za ki fahimce ni? Mama me ya sa za ki ɗora min laifin da ban aikata ba? Wallahi mama da za ki ji abin da Samira ta yi wa Yaya Ibrahim da sai kin yi tir da halinta saboda ko kaɗan abin da ta aikata bai yi kama da son da take iƙirarin tana yi masa ba, kuma fa don ya yi mata kashedi shi ne ta mare ni ban san hawa ban san sauka ba, ke ma kika mare ni ba tare da kin tambayi abin da yake faruwa ba, na ji na amince ni ce mai laifi don Allah ki yi haƙuri ki gafarce ni mama."

VOUS LISEZ
LALLA HAFSAT
Storie d'amoresoyayya, son zuciya, son maso wani, kaddara, tsaka mai wiya, dss