"Ki yi haƙuri mama, amma hankalina ne ya tashi da jin wannan maganar, shi yasa na kasa jurewa har sai kin gama yin bayani. Mama ƙwaƙwalwata ta cushe, tunani ya tsaya cak, na daina fahimtar abin da kike cewa ko kaɗan saboda maganarki ta wai an kawo kuɗin aurena! Ban san yadda zan fasalta yanayin da na shiga ba, duk da ina son Nura amma ai ya dace a faɗa min kafin a kawo kuɗi? Kuma ga shi har ya ce bai amince min da na tafi Niamey ba? Me ya sa Nura zai yi min Haka? Me ya sa zai ɓoye min abin da yake ganin ya dace da ni? Me ya sa mama? Ko dai Nura ya sauya min ne ? Me yasa zai sauya min lokaci guda? Abubuwan da muke yi a tare da shi sai dai ya kewaye ya faɗa maki. Me yake faruwa da Nura ne saboda ba haka muka saba yi da shi ba! Ba haka muka tsara rayuwarmu ba? Me ya sa zai fara sauya min a lokacin da nake mafarkin zai kasance nawa? Me ya sa zai min yin haka? Ina farincikin da baikona da ya yi amma ina takaicin rashin faɗa min da bai yi ba a lokacin..."
Cikin tsawa mama ta katse Hafsat tana cewa
"Wai ke wacce irin yarinya ce? Na ce ki tsaya in fahimtar da ke amma sai wani zancen banza kike sanyo min cikin maganata wanda ba shi da kan gado ko kaɗan? Ki min shiru in yi bayani da yaren da za ki fi fahimtar halin da ake ciki, da kuma akasin da aka samu wajen kawo kuɗin aurenki"
Ganin da mama ta yi Hafsat ta ƙi magana sai bin ta da ido take yi kawai kamar wata shashasha ko sauna saboda kallon da take yi wa mama sai ka ce doluwa don ta saki baki tana kallonta. Sai ya sanya mam matsawa gab da ita tana kama hannunwanta cikin nata, sannan ta fara magana cikin murya mai kama da rarrashin tana cewa
"Hafsat ki yi haƙuri da abin da zan ce maki yanzu. Na san ke mai ilmi ce kuma mai biyayya ce ke, ina son ki ci gaba da yi mana biyayya da izinin Allah za ki ci ribar biyayya kuma ba za ki taɓa taɓewa ba har abada. Kin san dai babu mai auren mijin wani ko? Kuma kin san ba mai auren matar wani ko? Kuma kin san duk lokacin da auren bawa ya zo ko ya shirya ko da bai shirya ba sai an yi shi ko? ko da ace yana son auren ko akasin hakan? Don Allah autata kar ki ba ni kunya wajen yi mana biyayya saboda an samu akasi ba Nura ne ya yi baikonki ba. Wannan halin da kike ganina kwanan nan duk shi ne musabbabin shigata damuwa, saboda na san ba a kyauta maki ba ko kaɗan duk da ba mu damar hana abin da Allah Ya hallata, kuma ba mu da ikon hana faruwan abin da yake a rubuce cikin littafinki na kaddara. Duk damuwar da nake ciki a wannan lokacin halin da za ki shiga ne in kika ji labarin za ki auri wanin Nura.."
"Haba mama wannan wacce kalar wasa ce kike yi min kamar dai tatsuniya wai zan auri wanin Nura, haba mama ki daina kar ki sa zuciyata ta buga." Cewar Hafsat wacce tun da mama ta fara magana ta natsu tana kallonta, don ita duk a tunaninta cewa mama za ta yi surprise ce Nura ya so yi mata shi yasa ya ɓoye mata, sai dai me? Kunnunwanta suka jiyo mata magana akasin haka wai wani ne ya yi baikonta. Shi ne ta yi wannan maganar hana fashewa da kuka gwanin ban tausayi, ita ma mama saura kaɗan ta fara hawaye saboda sanin halin da ƴarta za ta shiga nan gaba, tun ba a je ko'ina ba har ta fara kuka ina ga tafiya ta yi nisa, ganin da Hafsat ta yi mama ta kasa magana sai ta ce
"Mama don Allah ki ce wasa kike yi min. Don Allah mama ki yi magana kar ki sanya zuciyata ta fashe don ta fara barazanar tarwatsewa tun da kika ambaci sunan wanin zuciyar(Nura) da suna shi ne ya yi baikona" Sai ta sake fashewa da kuka, tana faɗawa jikin mama zuciyarta tana bugawa da sauri-sauri kamar wacce zuciya ya kama a nan take, cikin kuka ta ce
"Mama ki ce min mafarki nake yi don Allah!" Sai ta mari kanta tana cewa
"Ya Allah ka tashe ni da mumunan mafarkin nan da nake yi." Ta idasa maganar tana tashi daga jikin mama hawaye suna bin fuskarta shafe-shafe gwanin ban tausayi, duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata saboda halin da ta shiga lokaci guda.
"Ki yi haƙuri autata, ba a son ranmu haka ta faru ba, sai dai ba mu da yadda za mu yi ne saboda wani dalili mai karfi wanda ya sanya aka samu sauyi duk da ba muka zaɓa ba,shi ne angon da kansa ya je wajen kawunki neman auren, kuma ba mu da zaɓi da ya wuce mu ba shi don ya cancanci fiye da hakan a wajenmu." In ji mama tana kallon Lalla cike da tausaya wa rayuwarta don gaskiya ta san ba a yi mata adalci ba sai babu yadda za a yi tunda an ɗaure jijiyoyinsu, an tambayi aure a inda suke jin kunya babu kuma yadda suka iya.
